Amupitan: Majalisa Ta Cin Ma Matsaya kan Nadin Sabon Shugaban INEC da Tinubu Ya Yi

Amupitan: Majalisa Ta Cin Ma Matsaya kan Nadin Sabon Shugaban INEC da Tinubu Ya Yi

  • Joash Amupitan ya bayyana gaban majalisar dattawa domin tantance shi a matsayin sabon shugaban hukumar zabe mai zaman kanta kasa (INEC)
  • Sanatoci sun yi masa tambayoyi a yayin tantancewar wadda aka gudanar a zauren majalisar da ke babban birnin tarayya Abuja
  • Daga karshe majalisar ta gamsu da bayanan da ya yi mata tare da amincewa da nadin da Mai girma Bola Ahmed Tinubu ya yi masa

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Majalisar dattawa ta tabbatar da Farfesa Joash Ojo Amupitan (SAN) a matsayin sabon shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC).

Majalisar dattawan ta tabbatar da nadin ne bayan kammala tantancewarsa da ta ɗauki sa’o’i biyu a zauren majalisar a birnin tarayya Abuja.

Majalisar dattawa ta tabbatar da nadin Amupitan a shugabancin INEC
Farfesa Joash Amupitan da shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio. Hoto: @SenateNGR
Source: Twitter

Jaridar Daily Trust ta ce a lokacin tantancewar, Sanatoci sun yi masa tambayoyi masu muhimmanci da suka shafi zabe, gudanar da harkokin hukumar, manufofi, da kuma dokar zabe.

Kara karanta wannan

Amupitan: Sabon shugaban INEC ya fadi shirinsa kan sahihin zabe a gaban majalisa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tinubu ya nemi a amince da nadin Amupitan

Idan ba a manta ba, shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, ya tura sunan Amupitan ga majalisar dattawa domin tabbatarwa a matsayin sabon shugaban INEC, bayan karewar wa’adin Farfesa Mahmood Yakubu.

Wasikar neman tabbatar da shi ta samu karatu a zaman majalisar da shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, ya jagoranta.

Majalisa ta tabbatar da nadin Amupitan

Majalisar ta tabbatar da Amupitan ne bayan kada kuri’ar murya da Sanata Godswill Akpabio, ya jagoranta, jim kaɗan bayan ya amsa tambayoyi daga sanatoci.

An ba da damar shigar Amupitan cikin zauren majalisar ne bayan shugaban masu rinjaye, Sanata Opeyemi Bamidele, ya nemi a soke dokar majalisa ta 12 domin ba bak’i damar shiga, inda Sanata Abba Moro (PDP, Benue ta Kudu) ya mara masa baya.

Jaridar The Punch ta ce shugaban majalisar dattawa, Sanata Akpabio, ya tarbi Amupitan tare da iyalansa, inda ya yaba musu saboda goyon baya da suka nuna masa.

Kara karanta wannan

Majalisa na shirin cika burin Tinubu, za ta tantance sabon shugaban INEC, Amupitan

Kafin fara tambayoyi, Akpabio ya bayyana cewa an riga an tantance Amupitan daga ofishin mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro na (NSA).

Hakazalika ya bayyana cewa hukumar DSS da Ofishin Sufeto Janar na ƴan sanda sun tabbatar da cewa babu wani tarihin laifi da aka taɓa samu a kansa.

Majalisa ta tabbatar da nadin Amupitan
Sabon shugaban hukumar INEC, Farfesa Joash Ojo Amupitan. Hoto: @MSIngawa
Source: Twitter

Tantancewar ta fara ne da misalin karfe 12:55 na rana, inda Amupitan ya bayyana manufarsa ta tabbatar da sahihin zabe, gudanar da gyare-gyare a hukumar, da kuma faɗaɗa amfani da fasahar zamani a tsarin zabe na Najeriya.

Bayan amincewar majalisar, Farfesa Amupitan zai jagoranci shirye-shiryen zaben gwamna na jihohin Anambra da Osun da kuma kafa tushen babban zaben shekarar 2027.

Amupitan ya yi bayanai gaban majalisa

A wani labarin kuma, kun ji cewa sabon shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC), Farfesa Joash Amupitan, ya je gaban majalisar dattawa.

Sanatoci sun yi masa tambayoyi a yayin tantance shi biyo bayan nadin da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi masa.

Farfesa Amupitan ya bayyana tsare-tsarensa don tabbatar da cewa an gudanar da sahihin zabe a kasar nan.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng