Jos, Gombe da Wasu Birane da Ake Sayar da Litar Fetur N1000, an Samu Sauki a Kano

Jos, Gombe da Wasu Birane da Ake Sayar da Litar Fetur N1000, an Samu Sauki a Kano

  • An samu hauhawar farashin man fetur a wasu jihohi, musamman na Arewacin Najeriya, inda lita ta haura N950
  • A Jos, Gombe, Makurdi da Maiduguri, gidajen mai da dama sun rufe ko suna sayar da man tsakanin N950 zuwa N1000
  • Ana danganta karancin mai da kuma hauhawar farashin fetur din da rikicin matatar Dangote da kungiyar PENGASSAN

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Rahotanni sun bayyana cewa farashin man fetur ya sake yin tashi sama zuwa N1,000 kan kowace lita a wasu yankunan ƙasar nan.

Wannan ne karo na farko da aka ga sayar da litar fetur kan N1,000 tun bayan watan Afrilun 2025, inda daga nan ne farashin ya sauka ƙasa da N900.

Farashin litar fetur ya haura zwa N1000 a wasu jihohin Najeriya.
Mutane sun tsaya a gidan man NNPCL suna sayen man fetur. Hoto: @nnpclimited/X
Source: Getty Images

Farashin fetur ya tashi, jama’a sun koka

Rahoton jaridar Daily Trust ya nuna cewa, an samu dogon layi a gidajen mai da dama a manyan birane irin su Jos, Gombe, Makurdi, Maiduguri da Ilorin.

Kara karanta wannan

An shiga tashin hankali: 'Yan bindiga da makiyaya sun mamaye gari guda a Benue

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A Jos, an ce yawancin gidajen mai ba sa sayar da fetur a ranar Laraba, sai wasu kaɗan da ke sayarwa a tsakanin N950 zuwa N1,000 kan kowace lita.

Wani direba mai suna Ibrahim Suleiman ya koka da cewa kafin Mayun 2023, yana cika tankin motarsa da N7,000 zuwa N8,000, amma yanzu kudin ya ninka sau uku.

“Ba zan iya yin tafiya ta sama da kilomita 100 ba yanzu saboda tsadar mai,” in ji Ibrahim Suleiman.

Haka kuma a Gombe, mazauna garin sun bayyana fushi kan yadda farashin ya tashi daga N920 zuwa N1,000 kan kowace lita, abin da ya sa direbobi da masu motoci ke rage zirga-zirga ko kara kudin haya.

Wani direba, Anas Lawan, ya ce:

“A cikin kwanaki kaɗan farashin ya ƙaru da N30 – daga N910 zuwa N970.”

Ana zargin gidajen mai na boye fetur

A wasu wurare, direbobi sun zargi masu gidajen mai da boye man domin ƙirƙirar karancin fetur na wucin gadi.

Kara karanta wannan

Asiri ya tonu, an kama hatsabiban yan bindiga da suka hallaka Sarki Mai Martaba

Wani direba, Abdullahi Adamu, ya ce:

“Wannan ya zama tamkar sata. Wasu sun rufe gidajen mai ba don babu man ba, sai don kawai su ƙara farashi.”

A Makurdi, Mustapha Mohammed, wani manajan gidan mai, ya ce matsalar ta samo asali ne daga jinkirin isowar mai sakamakon rikici tsakanin matatar Dangote da PENGASSAN.

An rahoto cewa gidan mai da dama sun rufe, yayin da wadanda ba su rufe ba suke sayar da fetur din tsakanin N60 zuwa N1000.
Wasu mutane na kokarin sayen fetur a wani gidan mai. Hoto: Getty Images
Source: UGC

An samu saukin fetur a jihar Kano

A Maiduguri, direbobi na siyan lita ɗaya tsakanin N1,000 da N1,100, inda wasu masu mota da keke Napep suka daina fita aiki gaba ɗaya.

A Ilorin kuwa, yawancin gidajen mai sun daidaita farashin zuwa tsakanin N920 da N930 kan kowace lita, daga N865 zuwa N870.

Sai dai abin mamaki, a Kano farashin ya dan sauka daga N960 zuwa N950 kan kowace lita, inda gidajen mai irin su AY Maikifi, AA Rano da AYM Shafa ke sayarwa a wannan farashin.

Rahoton ya nuna cewa a ranar Litinin, gidajen man NNPCL a Kano sun kara farashin daga N905 zuwa N968, kafin ya dawo N950.

Kara karanta wannan

Dakarun soji sun fafata da ƴan bindiga, an gano ƴan China da aka yi garkuwa da su

A zantawar Legit Hausa da Malam Hussaini mai fetur, wani dan bumburutu a hayin Dan Mani, Rigasa, Kaduna, ya ce suna sayar da kwatar jarka a kan N1,400.

"Mu dai har yanzu N2,800 ne rabin galan, jarka kuma N5,600, ko mu sayar N5,500, ina maka magana a kan yau Juma'a (17 ga Oktoba, 2025.).
"Ta iya yiwuwa an samu karin kudin mai din, amma ni ban kara ba don ban sayo sabon mai ba, na sayo da yawa ne, kuma har yanzu ina da saura, ka ga ba zan iya kara ko kwabo ba."

Shi kuma Muhammadu Garba, wani da ke sana'ar cajin waya, ya ce shi yanzu ya hakura da sayen fetur, ya je an mayar da janaretansa ya koma amfani da gas.

"Tun da na fahimci ba za a samu saukin farashin fetur ba, na je aka mayar da janareta na mai amfani da gas, tun safe nake kunna shi har dare amma bai wuce na sayi gas din N4,000 ba."

- Muhammadu Garba.

Ya yi kira ga gwamnati da ta duba halin da talaka yake ciki, ta rage farashin fetur ko a samu saukin sufuri da saukin wasu kayayyakin masarufi.

Kara karanta wannan

Ta tabbata, sojojin Najeriya sun kama hatsabibin ɗan ta'adda da aka jima ana nema

Dalilin tashin farashin man fetur

A wani labarin, mun ruwaito cewa, farashin litar man fetur ya karu zuwa kusan N1,000 a wasu birane sakamakon wasu matsalolin jigila da aka samu.

Kungiyar ‘yan kasuwar mai ta kasa (IPMAN) ta zargi masu rumbun ajiya da kara farashi bayan Dangote ya dakatar da lodin mai.

‘Yan kasuwa sun ce suna shirin fara shigo da man fetur daga kasashen ketare kai tsaye don dawo da gasa da rage farashi a kasuwa.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com