'Dalilin da Ya Sa Na Kasance Musulmi kuma Kirista a Lokaci Guda': Mawaki Ya Magantu
- Shahararren ɗan wasan barkwanci ya yi karin haske kan kasancewarsa Musulmi kuma Kirista a lokaci guda
- Nasboi ya bayyana dalilin da yasa yake ɗaukar kansa a haka saboda asalinsa daga iyaye ne masu addinai daban-daban
- Mawakin ya ce mahaifinsa Musulmi ne daga yankin Yarabawa, mahaifiyarsa kuma Kirista ce daga Warri da ke jihar Delta
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Ikeja, Lagos - Fitaccen ɗan wasan barkwanci kuma mawaƙin Najeriya, Lawal Nasiru ya fadi addinan da yake bi.
Mawakin wanda aka fi sani da Nasboi, ya bayyana dalilin da yasa yake ɗaukar kansa Kirista da kuma Musulmi.

Source: Instagram
Mawaki Nasboi ya fadi addinai da yake bi
Hakan na cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X wanda a baya aka fi sani da Twitter a jiya Laraba 15 ga watan Oktoban 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mawakin ya bayyana cewa tarbiyyar da ya samu daga iyaye masu addinai daban-daban ta canja tunaninsa.
Ya ce mahaifinsa Musulmi ne daga yankin Yarabawa, yayin da mahaifiyarsa Kirista ce daga Warri a yankin Neja-Delta, kuma wannan haɗin ya sa ya zama mai buɗaɗɗen tunani.
Nasboi ya rubuta cewa:
"Baba na Bayarabe ne, mahaifiyata kuma ta fito daga yankin Warri, mahaifina Musulmi ne yayin da mahaifiyata kuma Kirista.
"Wannan ne ya sa ban san wariya da bambance-bambance na addini ko kabilanci ba, shi ne tarbiyyar da na samu.”

Source: Instagram
Abin da Nasboi ya koya a rayuwa
Nasboi ya ƙara da cewa an haife shi a Port Harcourt, ya kuma yi karatu a Jami’ar Uyo da ke Akwa Ibom, inda ya koyi mutunta bambance-bambancen al'umma.
Lokacin da wani masoyinsa ya tambaye shi wane addini yake bi, ya bada amsa cikin barkwanci cewa shi "Christmus" ne, wato Kirista kuma Musulmi.
Nasboi ya ce wannan fahimta ta haɗin addinai na cikin gida ta taimaka masa wajen ganin duniya ba tare da ƙiyayya ko rarrabuwar kawuna ba.
Ya jaddada cewa manufarsa ita ce nuna cewa addini bai kamata ya raba mutane ba, domin kowa ɗan Adam ne, komai asali ko imani.
Martanin wasu game da rubutun Nasboi
Masu ta'ammali da shafin X sun yi martani game da rubutun Nasboi inda mafi yawa suke masa shagube.
@olamilekan7:
"Wannan shi ke tabbatar da cewa kai ba ka da kabilanci a rubutunka bayan kalaman da ka yi kan yan matan Yarbawa ya karyata hakan.
"Ka bar wani daukar kanka wani, da kai da babanka duk ba wani abu ba ne."
@youhate4kt"
"Babu wanda ya tamabaye ka duka wannan shirme da ka rubuta."
Mawaki Portable ya zabgawa Fasto mari
Mun ba ku labarin cewa mawakin Najeriya, Habeeb Olalomi Badmus ya mari wani Fasto da ke wa'azi kusa da shagonsa na siyar da kayan shaye-shaye.
A lokacin, mawakin da ake kira Portable ya gargadi Faston da ya bar kusa da shagonsa inda ya ke zargin yana damun abokan huldarsa.
An yada faifan bidiyon a kafofin sadarwa inda mutane da dama suka goyi bayansa yayin da wasu ke cewa abin da ya yi ya kauce hanya.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng


