ADC Ta Yi Magana kan Tururuwar Gwamnoni da Manyan 'Yan Adawa zuwa APC

ADC Ta Yi Magana kan Tururuwar Gwamnoni da Manyan 'Yan Adawa zuwa APC

  • ADC ta bayyana takaici bayan karin gwamnoni a jam’iyyun adawa sun sauya sheka zuwa jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya
  • Mai magana da yawun ADC, Bolaji Abdullahi ya ce sauya shekar gwamnonin jihohi ya tabbatar da shirin APC na mamaye siyasar kasar nan
  • Jam’iyyar ta zargi gwamnatin APC da jefa yawancin 'yan Najeriya cikin talauci da wahala, amma an fi mayar da hankali a kan siyasa

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja Jam’iyyar hamayya ta ADC ta ce sauya shekar da gwamnonin jihohin Enugu da Bayelsa suka yi zuwa jam’iyyar APC mai mulki ya tabbatar da zargin da ta ke yi.

Mai Magana da Yawun ADC na kasa, Bolaji Abdullahi da ya bayyana haka ya ce jama’a sun dade suna gargadin cewa Shugaba Bola Tinubu na shirin mayar da Najeriya mai tsarin jam’iyyar daya.

Kara karanta wannan

Hana El Rufai taro: Kotu ta umarci 'yan sanda su biya jam'iyyun adawa diyyar N15m

ADC ta caccaki APC kan sauya sheka
Shugaba Bola Tinubu, Bolaji Abdullahi Hoto: Sanusi Bature D-Tofa/Bolaji Abdullahi
Source: Facebook

Daily Trust ta wallafa cewa Bolaji Abdullahu ya bayyana sauya shekar a matsayin cin amanar siyasa da ya jaddada watsi da muradun jama’a don wata manufa ta son kai.

ADC ta caccaki jam’iyyar APC

Daily Post ta wallafa cewa Bolaji Abdullahi ya ce duk da cewa a fili APC na ganin tana samun karuwa da karin gwamnoni, amma ba riba ba ce.

Ya zargi masu sauya sheka da watsar da al’ummarsu domin shiga jam’iyyar da ta jefa yawancin ‘yan kasa cikin kunci.

“Zaben 2027 ba zai kasance tsakanin jam’iyyu kadai ba, zai kasance tsakanin talakawan Najeriya da jam’iyyar da ta gurgunta rayuwarsu.’

ADC ta dura kan Shugaba Bola Tinubu

Jam’iyyar ADC ta caccaki gwamnatin Tinubu bisa gazawa a fannonin tsaro, tattalin arziki, lafiya, jin dadin jama’a da yakar cin hanci da rashawa.

ADC ta zargi APC da mamaye siyasar Najeriya
Hoton Mai Magana da ADC, Bolaji Abdullahi Hoto: Bolaji Abdullahi
Source: Facebook

An ji Bolaji Abdullahi ya bayyana cewa ko masu goyon bayan APC a baya yanzu suna nesanta kansu da jam’iyyar saboda yadda abubuwa ke tafiya.

Kara karanta wannan

Tsohon gwamna ya ƙi karbar tayin muƙami daga Shugaba Tinubu, ya faɗi dalilansa

Ya ce:

“Farashin abinci yana kara tashi kowace rana, ba aiki, tsaro ya tabarbare. Talakawa na fama da wahala amma maimakon jagororin adawa su tsaya tsayin daka, sun zabi su shiga jam’iyyar da ke da alhakin haka.”

Ya ce masu mulki na murna da sauya shekar gwamnonin, amma su a jam’iyyar ADC suna farin ciki da cewa hakan ya bayyana bambanci tsakanin masu kishin kasa da ‘yan dadi mulki.

ADC ta fallasa shirin dakile ta

A baya, mun wallafa cewa Shugaban riƙo na ƙasa na jam’iyyar ADC, David Mark ya zargi gwamnatin tarayya da shirin amfani da kotuna domin kawo wa tafiyarsu cikas.

Sanata Mark ya bayyana haka ne a birnin Abuja, lokacin da ya karɓi baƙuncin ƙungiyar lauyoyin ADC ta ƙasa, ƙarƙashin jagorancin Abdullahi Abdurrahman, inda ya ce wannan abin damuwa ne.

Tsohon 'dan majalisar ya jaddada cewa wannan shiri da ake ƙulla wa ba zai haifar da da mai ido ba, domin mutanen Najeriya sun farka, kuma ba za su sake yarda da danniya ba.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng