Hana El Rufai Taro: Kotu Ta Umarci 'Yan Sanda Su Biya Jam'iyyun Adawa Diyyar N15m
- Babbar kotu ta yi hukunci cewa dokar hana tarukan siyasa da ’yan sanda suka kafa a Kaduna ta sabawa kundin tsarin mulki
- Alkalin kotun ya ce ’yan sanda sun wuce gona da iri, kuma sun tauye ’yancin jam’iyyun adawa na gudanar da taruka
- A hukuncin da ta yanke, kotu ta umurci ’yan sanda su biya jam’iyyun N15m a matsayin diyyar tauye musu hakkinsu
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Kaduna – Wata babbar kotu da ke Kaduna ta yanke hukunci cewa haramcin da kwamishinan ’yan sanda na jihar ya kafa kan tarukan siyasa ya sabawa kundin tsarin mulkin Najeriya.
Alkalin kotun, Mai Shari’a Murtala Zubairu, ne ya bayyana haka a hukuncin da ya yanke a ranar Laraba.

Source: Twitter
Rikici a taron 'yan adawa a Kaduna
Jaridar The Cable ta rahoto cewa Mai shari'a Murtala ya kori karar da ’yan sanda suka shigar kan jam’iyyun ADC da SDP, yana mai kiran karar da “cin zarafin kotu.”

Kara karanta wannan
'Yan bindiga sun kashe fiye da mutane 10 a sabon harin da suka kai garuruwan Filato
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wannan lamari ya samo asali ne daga taron jam’iyyar ADC da aka yi a ranar 30 ga Agusta, 2025, wanda tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai, da wasu jagororin jam’iyyar suka halarta.
A lokacin da ake shirya taron ne, Legit Hausa ta ruwaito cewa 'yan daba sun tarwatsa gangamin, sun lalata kujeru, kayan sauti da sauran su.
Bayan farmakin, rundunar ’yan sanda ta Kaduna ta gayyaci El-Rufai da wasu mambobin ADC shida don amsa tambayoyi bisa zargin “hada baki, tayar da tarzoma, da cutar da mutane.”
Kotu ta zargi ’yan sanda da sabawa doka
Amma a hukuncin sa, Mai Shari’a Murtala ya bayyana cewa ’yan sanda sun wuce iyakokin da doka ta ba su.
Hakazalika ya ce sun take ’yancin jam’iyyun adawa na yin taro kamar yadda Sashe na 40 na Kundin Tsarin Mulki ya tanada.
Mai Shari'a Murtala ya ce:
“A bayyana yake, ’yan sanda sun keta hakkin jam’iyyun adawa kuma sun nuna yunkurin amfani da iko fiye da kima, don haka kotu na da ikon hana irin wannan abu gaba ɗaya.”
Kotu ta sa a biya ADC, SDP diyyar N15m
Kotun ta umurci ’yan sanda su biya N15m a matsayin diyyar zaluntar jam’iyyun ADC da SDP, kamar yadda rahoton Punch ya nuna.
An ce rundunar 'yan sanda ta biya N5m saboda dakatar da taron jam'iyyun na Satumba 4, 2025; ta biya N5m saboda kiran jam'iyyun “masu tarzoma a bainar jama'a."
Hakazalika, kotun ta ce 'yan sanda za su biya jam'iyyun adawar diyyar N5m saboda samun takardar hukuncin gaggawa da aka bayar ba bisa doka ba.

Source: Twitter
Umurnin kotu na karshe ga 'yan sanda
Mai Shari’a Murtala ya kuma soke takardar dakatarwa da kotu ta bayar a ranar 4 ga Satumba, yana mai cewa “ba ta da tushe kuma an bayar da ita ba bisa ƙa’ida ba.”
Kotu ta kuma hana kwamishinan ’yan sanda na Kaduna da jami’ansa yin katsalandan a harkokin siyasar jam’iyyun adawa ba tare da bin doka ba.
Haka kuma ta umurce su da su gudanar da cikakken bincike kan rahoton tashin hankali na ranar 30 ga Agusta, 2025, su kuma mika rahoton ga babban lauyan jihar Kaduna cikin kwanaki 60.
Martanin El-Rufai kan hana su taro
Tun da fari, mun ruwaito cewa, tsohon gwamnan Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, ya caccaki jami'an 'yan sanda kan hana wani taron shugabannin jam'iyyar ADC.
El-Rufai ya zargi ‘yan sanda da yin amfani da iko fiye da kima, inda ya ce kwamishinan ‘yan sanda na jihar ya samo umarnin kotu da ya hana taron ba bisa ka'ida ba.
Shugabannin jam'iyyar ADC na yankin Arewa maso Yamma ne dai suka so gudanar da taron jaje ga mambobinsu da aka farmaka a Kaduna, amma 'yan sanda suka hana
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

