Yaki da Zaman Banza: Gwamnatin Tinubu Ta Bude Cibiyoyin Samar da Aiki a Jihohi
- Gwamnatin Tarayya ta kaddamar da cibiyoyin samar da aiki domin rage rashin aikin yi da bunkasa ayyukan matasan kasar
- Ministar Kwadago, Nkeiruka Onyejeocha, ta ce cibiyoyin za su hada matasa da damar samun aiki ta amfani da fasahar zamani
- An bayyana shirin a matsayin wani bangare na tsarin Renewed Hope na Shugaba Bola Tinubu domin habaka tattalin arziki
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Lagos – Gwamnatin Tarayya ta kaddamar da sabon shiri domin yaki da matsalar rashin aikin yi da kuma samar da ayyuka masu inganci ga ‘yan Najeriya.
Karamar ministar kwadago ta tarayya, Nkeiruka Onyejeocha, ce ta sanar da hakan yayin wani taro da aka gudanar a birnin Lagos.

Source: Facebook
Vanguard ta rahoto cewa ministar ta ce shirin na daga cikin manyan tsare-tsaren shugaba Bola Tinubu da ke da nufin hada masu neman aiki da damar aiki kai tsaye.

Kara karanta wannan
'Yan bindiga sun kashe fiye da mutane 10 a sabon harin da suka kai garuruwan Filato
Yadda cibiyoyin aikin za su amfani matasa
Minista Onyejeocha ta bayyana cewa cibiyoyin za su hada ayyuka da dama ciki har da bincike ta hanyar fasahar zamani, bin diddigin bayanan masu neman aiki da bayar da shawarwari kan aiki.
Dazu jaridar Punch ta wallafa cewa ta ce:
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
“Cibiyoyin za su zama wata kafa ta zamani da za ta ba matasa damar samun aiki da kuma gogayya da takwarorinsu a matakin kasa da kasa.
"Wannan tsarin zai samar da hadin kai a tsakanain masu sana'a da kuma karfafa tattalin arzikin gida Najeriya.”
Gwamnatin Tinubu ta kaddamar da shirin LEEP
A yayin taron, ministar ta kuma kaddamar da shirin LEEP, wanda ke da nufin inganta kwarewar matasa da cike gibin rashin samun horo wajen inganta aiki.

Source: Twitter
Ministar ta ce:
“Ba kawai samar da aiki muke son yi ba, muna son gina tsarin da zai kare hakkin ma’aikata, tabbatar da albashi mai kyau.”
Maganar hadaka da gidauniyar Mastercard
Ministar ta yaba wa gidauniyar Mastercard bisa hadin gwiwar da take yi da Najeriya ta hanyar shirin Young Africa Works.
Shirin ya taimaka wajen samar da ayyukan yi, bunkasa kasuwanci da koyar da fasahar zamani ga dubban matasan Najeriya cikin shekaru shida da suka gabata.
Ta ce manufar wannan hadin gwiwa ta dace da burin gwamnati na samawa matasa aiki ta amfani da basirar da suke da ita.
Gwamnati za ta cigaba da tallafawa matasa
Onyejeocha ta tabbatar da cewa ma’aikatarta za ta ci gaba da aiwatar da manufofin da ke goyon bayan samar da ayyukan yi, hada kan jama’a da tabbatar da zaman lafiya da habaka tattalin arziki.
“Ma’aikatar Kwadago za ta ci gaba da aiki tare da gidauniyar Mastercard da sauran abokan hulɗa domin gina makoma mai inganci,”
Inji ta
Hon. Tasiu Ishaq ya raba tallafin N250m
A wani labarin, mun kawo muku cewa dan majalisar jihar Jigawa mai wakiltar karamar hukumar Dutse ya raba tallafin N250m.
An yi bikin raba kayan tallafin ne a fililin taron tunawa da Malam Aminu Kano da ke Dutse, inda Hon. Tasiu Ishaq ya raba motoci da sauransu.
Gwamnan jihar Jigawa, Malam Umar Namadi da ya halarci taron ya yaba wa Hon. Tasiu Ishaq kan tallafawa jama'ar mazabar shi.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

