Malamai, 'Yan Siyasa da Sarakunan Arewa Sun Hada Kai kan Rashin Tsaro da Tattali

Malamai, 'Yan Siyasa da Sarakunan Arewa Sun Hada Kai kan Rashin Tsaro da Tattali

  • Sarkin Musulmi da sauran manyan malamai sun halarci taron malaman Musulunci na Arewa da aka yi a jihar Kaduna
  • Taron ya maida hankali kan tsaro, amfani da kafafen sada zumunta da bukatar hadin kai tsakanin malamai da shugabanni
  • An kammala taron da kudurin hada kai, tattaunawa da karfafa shugabancin addini don magance rashin tsaro da fatara

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.


Jihar Kaduna – Manyan malamai da shugabannin addinin Musulunci a Arewacin Najeriya sun bayyana damuwa yadda rashin tsaro ke kara ta’azzara a kasar.

Malamai, sarakunan gargajiya da 'yan siyasar Arewa sun yi gargadin cewa Najeriya na iya fadawa cikin rikici idan ba a dauki matakin gaggawa ba.

Taron Malaman Arewa a Kaduna
Dr Bashir Aliyu Umar na jawabi yayin taron malaman Arewa a Kaduna. Hoto: Jibwis Nigeria
Source: Facebook

Masarautar Zazzau ta wallafa a X cewa mai martaba Ahmad Bamalli ne ya wakilci mai alfarma Sarkin Musulmi a taron Malaman Arewacin Najeriya da aka yi.

Taron aka gudanar a Kaduna ya tattaro fitattun malamai, ‘yan siyasa da shugabannin addini domin tattauna hanyoyin tabbatar da zaman lafiya da hadin kai a cikin al’umma.

Kara karanta wannan

Yaki da zaman banza: Gwamnatin Tinubu ta bude cibiyoyin samar da aiki a jihohi

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sarkin Musulmi ya ce lokacin hadin kai ya yi

Ambasada Ahmad Bamalli ya ce Sultan ya bukaci shugabannin Musulmi su hada kai don dakile rashin tsaro da kuma matsalar amfani da kafafen sada zumunta wajen yada kiyayya.

Sarkin Musulmi ya ce:

“Wannan ne lokacin da ake bukatar Musulmai su hade su zama tsintsiya madaurinki daya. Malamai su yi wa’azi kan zaman lafiya, hakuri da hadin kai bisa koyarwar addinin Musulunci.

Ya jaddada cewa yada labaran karya da kalaman kiyayya ta hanyar kafafen sadarwa na daga cikin abubuwan da ke haddasa rikice-rikice da rarrabuwar kawuna a kasa.

Doguwa, Yari sun jaddada bukatar hadin kai

'Dan majalisar wakilai, Alhassan Doguwa, ya bukaci karin hadin kai tsakanin malamai da ‘yan majalisa don karfafa zaman lafiya da kyakkyawan shugabanci.


“Tsaro aikin kowa ne,”

- In ji shi.

Ya kara da cewa majalisar wakilai za ta goyi bayan duk wani shiri da zai hada kan al’umma da kuma kare darajar Musulunci.

Kara karanta wannan

Tinubu ya alakanta rashin tsaro da masu satar ma'adinai, ya yi kira ga duniya

Taron Malaman Arewa a Kaduna
Sanata Abdulaziz Yari da wasu malamai a wajen taro a Kaduna. Hoto: Jibwis Nigeria
Source: Facebook

A nasa jawabin, Sanata Abdul’aziz Yari na Zamfara ta Yamma ya gargadi mutane da kada su daura laifin rashin tsaro gaba daya kan gwamnati.

Sheikh Gumi ya magantu kan talauci

Fitaccen malamin addini, Sheikh Ahmad Abubakar Gumi, ya bukaci a inganta tattaunawa tsakanin kungiyoyin Musulmi domin magance matsalar talauci da ta’addanci.

Gumi ya kuma bukaci a sake duba dokokin batanci a kafafen sada zumunta ba tare da hana ‘yancin fadar albarkacin baki ba, yana mai cewa burin taron shi ne hadin kai da gyara, ba rikici ba.

A wani sako da shafin Jiwbis Nigeria ya wallafa a Facebook, Legit ta hango malamai daga bangarorin Izala biyu, Darika da sauransu a wajen taron.

Limamin Abuja, Farfesa Ibrahim Makari ya wallafa a Facebook cewa yana tare da mahalarta taron duk da cewa ba ya Najeriya.

An dauke Sheikh Abduljabbar daga Kano

A wani rahoton, kun ji cewa an sauya wa Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara wajen zama daga jihar Kano.

Kara karanta wannan

Sarkin Musulmi ya magantu kan neman 'raba' Najeriya a gaban gwamnoni a Legas

Hukumar kula da gidajen gyaran hali ta jihar Kano ce ta bayyana haka ga manenma labarai a ranar Talata.

Sai dai hukumar ta bayyana cewa hakan ba zai shafi walwalar malamin ta kowace fuska ba, kuma za tabbatar masa da dukkan hakkokin shi.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng