An Samu Sauki: Farashin Masara, Wake da Wasu Kayan Masarufi Ya Sauka a Najeriya

An Samu Sauki: Farashin Masara, Wake da Wasu Kayan Masarufi Ya Sauka a Najeriya

  • Hauhawar farashin kaya a Najeriya ta fadi zuwa 18.02%, mafi ƙanƙanta tun watan Yunin 2022, cewar rahoton NBS
  • Hukumar kididdigar ta ce an kuma samu saukar farashin abinci zuwa 16.87%, musamman masara, da su wake
  • Jihohin Ekiti, Rivers, da Nasarawa suka fi samun tashin farashin abinci; yayin da Bauchi da Niger suka fi samun sauƙi

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Hukumar kididdiga ta kasa (NBS) ta bayyana cewa hauhawar farashin kaya a Najeriya ta fadi zuwa 18.02% a watan Satumba 2025.

Saukar farashin kayayyakin zuwa 18.02% shi ne mafi ƙanƙanta da aka samu a Najeriya cikin shekaru uku, cewar NBS.

Hauhawar farashin kayayyaki ta fadi a Najeriya, an samu sauki kayan abinci.
Hoton 'yan kasuwa suna hada-hadar kasuwanci a Najeriya. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

An samu saukar farashin kayayyaki

Wannan sabon rahoto ya nuna sauƙin matsin tattalin arziki, tun bayan watan Yunin 2022, kamar yadda rahoton jaridar The Cable ya nuna.

Kara karanta wannan

An shiga tashin hankali: 'Yan bindiga da makiyaya sun mamaye gari guda a Benue

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewar rahoton CPI da NBS ta fitar a ranar Laraba, adadin hauhawar farashin ya ragu da 14.68% idan aka kwatanta da na Satumba 2024 wanda ya kai 32.70%.

Hukumar NBS ta bayyana cewa:

“Wannan yana nuni da cewa hauhawar farashin kayayyaki (na shekara-shekara) ya ragu a watan Satumba 2025 idan aka kwatanta da watan Satumba 2024."

A kan kididdigar wata zuwa wata, hauhawar farashin ya tsaya kan 0.72%, kasa da na watan Agusta 2025 wanda ya kai 0.74%, inji rahoton Channels TV.

Farashin abinci ya sauka zuwa 16.87%

Hukumar NBS ta kuma bayyana cewa hauhawar farashin abinci ya sauka zuwa 16.87% a watan Satumba, 2025 idan aka kwatanta da 37.77% a Satumba, 2024, raguwa mai yawa da ta kai 20.9%.

Rahoton ya ce:

“Saukar da aka samu ya samo asali ne daga ragin farashin hatsi (masara), garin rogo, wake, gero, dankali, albasa, ƙwai, tumatir da barkono.”

Kara karanta wannan

Minista ya tafi kasar waje, ya je duba jiragen yakin sojojin Najeriya da ake kerawa

Rahoton ya ce hauhawar farashin abinci a cikin watanni 12 ya tsaya kan 24.06%, kasa da na bara wanda ya kai 37.53%.

NBS ta ce an samu saukar farashin kayan abinci yayin da hauhawar farashin kayayyaki ta fadi.
Hoton kayayyakin abinci da suka hada da dankalin turawa, albasa, tumaturi da sauransu. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Farashin kayan abinci a jihohin Najeriya

A bangaren jihohi, Ekiti (28.68%), Rivers (24.18%), da Nasarawa (22.74%) ne suka fi tsadar farashin abinci, yayin da Bauchi (2.81%), Niger (8.38%), da Anambra (8.41%) suka fi sauƙin kaya.

Sai dai a kididdigar wata zuwa wata, Zamfara (15.62%), Ekiti (12.77%), da Sokoto (12.55%) ne suka fi tashin farashin abinci, yayin da Akwa Ibom (-12.97%), Borno (-12.95%), da Cross River (-10.36%) suka samu sauki.

Masana tattalin arziki na ganin cewa saukin da ake ci gaba da samu alama ce ta cewa manufofin tattalin arzikin gwamnati da gyaran kasuwanci sunafara haifar da sakamako mai kyau.

Farashin hatsi a kasuwar Dandume

A zantawarmu da Abdulmumin Sani, mazaunin Dandume da ke jihar Katsina, ya yi mana bayani game da farashin hatsi a kasuwar.

Abdulmumini ya ce:

"Sabuwar masara mai aure ta kai har N25,000, ina nufin buhunta, sannan tsohuwa mai aure ta kai har N33,000, amma da safe an sayar da ita tsakanin N30,000 da N32,000, farar masara kuma ta kai N41,000.

Kara karanta wannan

Ta tabbata, sojojin Najeriya sun kama hatsabibin ɗan ta'adda da aka jima ana nema

"An sayar da farin wake tsakanin N80,000 da N82,000, sannan an sayar da waken suya har zuwa N53,000. Shinkafa sabuwa ta kai N23,000, tsohuwa kuma N27,000.
"Dawa ta kai N30,000, Dauro kuma N45,000, sannan Gero ya kai har N42,000, kuma an sayar da Rogo kan N35,000."

Farashin kayayyaki a watan Agusta

A wani labarin, mun ruwaito cewa, hukumar NBS ta tabbatar da cewa hauhawar farashin kayayyaki a Najeriya ya ragu a watan Agusta, 2025.

A wani rahoton NBS ta fitar yau Litinin, 15 ga watan Satumba, 2025, ta ce hauhawar farashin kaya ya sauka zuwa 20.12% a watan jiya.

Rahotan ya danganta wannan sauki da aka samu da saukar farashin shinkafa, gero, dawa, garin masara da wasu kayan amfani na yau da kullum.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com