Gwamna Radda Ya Sake Tabo batun Sulhu da 'Yan Bindiga a Katsina
- Gwamnan jihar Katsina, Dikko Umaru Radda, ya tabo batun yin sulhu da 'yan bindiga a gwamnatinsa
- Dikko Umaru Radda ya bayyana cewa gwamnatinsa ba za ta taba shiga tattaunawa da 'yan bindiga ba
- Gwamnan ya bada tabbacin cewa gwamnatinsa za ta bude kofar goyon bayan yarjejeniyar zaman lafiya da al'umma suka shirya
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Katsina - Gwamnan jihar Katsina, Dikko Umaru Radda, ya ce gwamnatinsa ba za ta taba shiga tattaunawa kai tsaye da ‘yan bindiga ba.
Gwamna Radda ya ce gwamnatinsa ta bude kofar amincewa da yarjejeniyar zaman lafiya da al’ummomi suka shirya da kansu domin kawo karshen rikici a yankunansu.

Source: Facebook
Jaridar The Punch ta ce Gwamna Radda ya bayyana hakan ne a ranar Laraba, yayin da yake kaddamar da karin mambobi 100 na rundunar C-Watch a Katsina.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cewarsa, lokacin da gwamnatinsa ta fara shirin kawo rundunar C-Watch shekaru biyu da suka gabata, ta kawo sabon salo na tsaro da ba a taba gwadawa ba, amma da niyyar kawo karshen matsalar ta’addanci.
"Mun hau mulki ne da nauyin tabbatar da zaman lafiya da tsaro a sassa da dama na jihar. Abin da kawai nake da tabbaci a kai shi ne, wannan gwamnati ta kudiri aniyar kawo karshen ta’addanci."
"Na yi yakin zabe a kai, kuma ba zan ci amanar wannan amincewar da jama’a suka yi mini ba.”
- Gwamna Dikko Radda
Radda ya musanta tattaunawa da 'yan bindiga
Gwamna Radda ya karyata rahotannin da ke cewa gwamnatinsa tana tattaunawa da ‘yan bindiga, yana mai cewa hakan ba gaskiya ba ne.
“Na bayyana a bainar jama’a cewa gwamnatina ba za ta tattauna da ‘yan bindiga ba. Amma za mu ci gaba da maraba da zaman lafiya."
- Gwamna Dikko Radda
Gwamnan ya bayyana cewa tsarin ‘Katsina Model’ wani shiri ne da ke ba al’umma ikon shiryawa da kulla yarjejeniya da ‘yan bindiga da suka tuba da kansu, suka mika makamansu, jaridar Vanguard ta tabbatar da labarin.
"Rawar da gwamnati ke takawa ita ce ta karfafa gwiwar al’umma wajen zaman lafiya, tare da tabbatar da bin doka da oda."
"Muna son mu tabbatar da cewa al’ummomin da suka samu zaman lafiya sun amfana ta fuskar ci gaba da ingantacciyar rayuwa.”
- Gwamna Dikko Radda

Source: Facebook
Me Radda ya ce kan shirin zaman lafiya?
Gwamna Radda ya ce shirin ya samu nasara a wasu yankuna da dama, inda karamar hukumar Jibia ta kwashe watanni takwas ba tare da harin ‘yan bindiga ba, yayin da Batsari ta samu watanni bakwai na cikakken zaman lafiya.
Haka nan, Danmusa, Safana, Faskari, da Sabuwa, sun samu saukin hare-hare tun bayan fara wannan shirin zaman lafiya.
Sahabi Abdulrahman ya shaidawa Legit Hausa wannan matsayar da Gwamna Dikko Radda ya dauka abin a yaba ce.
Ya nuna cewa ko kadan bai kamata gwamnati ta hau kan teburin sulhu da 'yan bindiga ba.
"Tabbas muna goyon bayan wannan matsayar, domin bai kamata gwamnati ta rima tattaunawa da 'yan bindiga ba."
- Sahabi Abdulrahman
Sojoji sun hallaka 'yan bindiga a Katsina
A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun sojojin Najeriya sun yi artabu mai zafi da 'yan bindiga a jihar Katsina.
Dakarun sojojin sun hallaka 'yan bindiga 12 yayin artabun da suka yi a kauyen Mabai da ke karamar hukumar Kankara.
Majiyoyi sun bayyana cewa ‘yan bindigan sun wuce kusa da sansanin sojoji ne da ke Mabai, inda daga nan ne suka bude masu wuta.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


