Tarihin Abokin IBB, Mamman Vatsa da Tinubu Ya Yi wa Afuwa bayan Hukuncin Kisa

Tarihin Abokin IBB, Mamman Vatsa da Tinubu Ya Yi wa Afuwa bayan Hukuncin Kisa

Afuwa da shugaban kasa Bola Tinubu ya yi wa marigayi Mamman Vatsa ya jawo Legit Hausa bincike kan wasu abubuwa game da tarihinsa.

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Niger - A makon da ya wuce ne shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi wa Janar Mamman Jiya Vatsa afuwa bayan shekaru da rasuwa.

Tarihi ya nuna cewa Mamman Vatsa ya kasance daya daga cikin wadanda suka kulla alaka ta kusa da Janar Ibarhim Badamasi Babangida kafin yanke masa hukuncin kisa.

Janar Mamman Jiya Vatsa
Hoton marigayi Janar Mamman Vatsa. Hoto: Minna City of Literature
Source: Facebook

A wannan rahoton, Legit Hausa ta tattaro wasu muhimman abubuwa game da rayuwar marigayi Mamman Vatsa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Haihuwa da rayuwar Mamman Vatsa

Bincike ya nuna cewa an haifi marigayi Janar Mamman Vatsa a ranar 3 ga Disamba, 1940 a jihar Neja.

Kara karanta wannan

Duniya labari: Babban malamin addini ya riga mu gidan gaskiya

Wani rahoto na Vanguard ya nuna cewa Janar Vatsa aboki tun na yarinta ne ga Ibrahim Badamasi Babangida, kuma su biyun abokan karatu ne da suka halarci makarantu iri daya.

IBB a lokacin da ya ke soja
Janar Babangida a lokacin da ya ke soja. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Kamar Babangida, Vatsa ya halarci Government College Bida daga shekarar 1957 zuwa 1962, sannan ya fara aikin soja ta hanyar shiga NMTC a ranar 10 ga Disamba, 1962.

Matsayin da Mamman Vatsa ya rike

Mamman Vatsa ya yi aiki a matsayin Ministan Babban Birnin Tarayya (Abuja) tun daga shekarar 1985, inda ya jagoranci sauye sauye da dama.

Bayan haka, Vatsa ya yi aiki a matsayin kwamandan Makarantar Sojin Kasa ta Najeriya (NASI) daga 1979 zuwa 1983.

Wani yanki na iyakar Najeriya da Kamaru
Wasu mutane a zaune a yankin Bakassi da ya kasance iyakar Najeriya da Kamaru. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

A ƙarshen mulkin Shugaba Shehu Shagari, Vatsa ya zama QMG, mukamin da ya riƙe har zuwa juyin mulkin Disamba 1983.

A 1981, lokacin da sojojin Kamaru suka harbe suka kashe sojojin Najeriya guda biyar a yankin Bakassi da ake takaddama a kai, Vatsa ya jagoranci tsare iyakar Najeriya.

Alakar Vatsa da Janar Babangida

Janar Ibrahim Babangida ya bayyana cewa shi da marigayi Janar Mamman Vatsa sun dade suna abokai tun suna yara, tare suka tashi kuma tare suka yi karatu a makaranta daya.

Kara karanta wannan

Dangantaka ta yi tsami tsakanin Wike da Tinubu? An ji gaskiyar abin da ya faru

A littafin da ya rubuta, IBB ya ce dangantakarsu ta yi tasiri sosai a rayuwarsu, domin bayan sun shiga aikin soja ma, sun cigaba da kasancewa tare a fannoni da dama.

IBB da Janar Vatsa
Janar Mamman Vatsa da Ibrahim Babangida. Hoto: Getty Images
Source: Twitter

Ya kara da cewa tun daga makarantar sakandare, sun saba da juna sosai, inda sukan yi mu’amala cikin shaƙuwa da kuma takara ta abota.

Yadda aka yankewa Vatsa hukuncin kisa

Wani rahoto da Premium Times ta wallafa, wani mai shirya fina-finai ya ce tsohon shugaban soja, Janar Ibrahim Babangida, ya taba gaya masa cewa shi ne ya bada umarnin kashe Mamman Vatsa.

Mai shirya fina-finan ya ce:

“Na tambayi Ibrahim Babangida game da labarin Mamman Vatsa, sai ya ba ni amsa cewa sun yi karatu tare a makarantar sakandare ta Bida.”

Ya ci gaba da cewa:

“An shirya juyin mulki a lokacin da Babangida, inda ake shirin kashe shi a barikin Dodan.
"Mamman Vatsa ya samu labarin wannan shirin amma bai gaya wa abokinsa (Babangida) ba. Kodayake ba ya cikin wadanda suka shirya juyin mulkin, kotun soja ta same shi da laifi.”
Janar Babangida da Tinubu
Shugaba Tinubu na gaisawa da janar IBB. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Twitter

A cewar mai bayar da labarin, Babangida ya ce kalubalen da ya fuskanta a lokacin shi ne tsakanin kaunar abokinsa da kuma bin ka’idojin soja.

Kara karanta wannan

Bayani kan sake auren Maryam Sanda da yadda aka nemi Buhari ya mata afuwa

Tribune ta rahoto cewa iyalan Mamman Vatsa sun fito sun musa dukkan zarge zargen da aka yi masa a lokacin Babangida wato IBB.

Tinubu ya yi wa Mamman Vatsa afuwa

A wani labarin, mun kawo muku cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi wa marigayi Mamman Vatsa afuwa.

Hakan na zuwa ne bayan shugaban kasa ya zauna da 'yan majalisar kolin kasa a makon da ya wuce a birnin tarayya Abuja.

Afuwar da aka yi wa Mamman Vatsa ta wanke shi daga laifin juyin mulki da kotun soja ta same shi da aikatawa a lokacin Janar Babangida.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng