Tauraruwar Kano Ta Kara Haskawa, Jihar Ta Samu Babban Nasara a Sauyin Yanayi
- Jihar Kano ta daga daga matsayi na 35 zuwa na hudu a jerin jihohin da suka fi inganta kula da sauyin yanayi a Najeriya
- Wannan nasara ta samo asali ne daga jagoranci mai hangen nesa, sauye-sauyen doka da hadin kan al'umma, in ji Kwamishina
- Gwamnatin jihar Kano ta yaba wa abokan hulɗarta na cikin gida da na ƙasa da ƙasa bisa goyon baya da hadin kai
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Jihar Kano ta samu babban lambar yabo a fannin kulawa da sauyin yanayi, inda ta tashi daga matsayi na 35 a bara zuwa na 4.
Kano ta samu matsayin ne a Kididdigar Ayyukan Jihohi kan Sauyin Yanayi ta Najeriya na shekarar 2025.

Source: Facebook
Wannan na kunshe a cikin sanarwar da Kwamishinan Muhalli da Sauyin Yanayi na Kano, Dr. Dahir M. Hashim ya bayyana hakan a shafinsa na X.
Gwamnatin Kano ta taka sabon mataki
Dr. Dahir M. Hashim a bayyana cewa wannan nasara tana nuna irin jagoranci mai hangen nesa na Gwamna Abba Kabir Yusuf, wanda ya sanya sauyin yanayi a tsakiyar manufar ci gaban jihar.
A cewarsa:
‘Wannan ci gaba yana nuna hangen nesa da jajircewar Gwamnanmu wajen dorewar muhalli da ci gaban jihar Kano."
A cikin shekara guda da ta gabata, Kano ta aiwatar da muhimman sauye-sauye da suka hada da kaddamar da sabuwar dokar sauyin yanayi.
Sannan ta yi amfani da makamashi na zamani a hukumomin gwamnati, da zuba jari a ayyukan dasa itatuwa da hana ambaliya a fadin jihar.

Source: Facebook
Haka zalika, jihar ta ci gaba da gyaran muhallin birane, wanda ya taimaka wajen inganta ingancin iskar da aka shaka da dawo da lafiyar muhalli.
Wadannan matakai, in ji Kwamishina, sun gina tubalin dorewa da ci gaba mai tsafta da adalci ga kowa.
Gwamnatin Kano ta yabi abokan hulda
Dr. Hashim ya yaba da rawar da kungiyoyi daban-daban suka taka, daga gwamnati zuwa al’umma da abokan hulɗa na ƙasa da ƙasa, wajen cimma wannan nasara.
"Wannan lambar yabo ta fito ne daga haɗin gwiwa tsakanin ƙungiyoyin gwamnati, al’umma, kungiyoyin fararen hula da sauran masu ruwa da tsaki."
Kwamishinan ya kara da nuna godiya ga Ma’aikatar Muhalli ta Tarayya karkashin Mallam Balarabe Abbas Lawal.
Haka kuma Dr. Hashim ya yabi Sashen Sauyin Yanayi, saboda taimako da jagoranci da suka bayar.
Ya kuma jinjinawa kungiyar Society for Planet and Prosperity (SPP) da Jami’ar Bristol ta Birtaniya, wadanda suka jagoranci wannan kididdiga ta ƙasa.
Gwamnatin Kano dauki sabon kambu
A wani labari, kun ji cewa a cikin rahoton da Hukumar Tattara Bayanan Ƙasa (NBS) ta fitar tare da tabbatarwa, jihar Kano ta yi nasarar ninka kudin shiga da take samu daga haraji.
Ibrahim Adam, mai ba Gwamna Abba Kabir Yusuf shawara kan harkokin labarai, ya bayyana cewa an samu wannan nasara ne saboda sauyin da gwamnati ta yi tun hawa mulki.
Ya kuma jaddada cewa gwamnati ba ta ƙara haraji ga talakawa ba, musamman ma masu amfani da keke Napep, kamar yadda wasu suka yi zargin cewa an yi a baya bayan nan.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


