Farouk Lawan: Tsohon 'Dan Majalisa Ya Rabu da Kwankwasiyya bayan Barin Kurkuku

Farouk Lawan: Tsohon 'Dan Majalisa Ya Rabu da Kwankwasiyya bayan Barin Kurkuku

  • Tsohon ɗan majalisar wakilai, Farouk Lawan, ya ce afuwar da Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi masa ta dawo da shi siyasa
  • Ya bayyana cewa tun bayan da aka tabbatar masa da hukunci a kan karban cin hanci, tsarn tafiyar Kwankwasiyya da ya ke kai ta yi watsi da shi
  • Hon. Farouk Lawan na daga cikin mutane 175 da Shugaban Kasa Tinubu ya yi wa afuwa a makon da ya gabata a kasar nan

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – Tsohon ɗan majalisar wakilai, Hon. Farouk Lawan, ya bayyana cewa yafiyar da ya samu daga shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ranar 9 ga Oktoba, 2025, ta ba shi damar dawo wa siyasa da karfinsa.

Kara karanta wannan

"Ba siyasa ba ce": Jagoran APC ya kare yafiyar Tinubu ga masu manyan laifuffuka

Hon. Farouk Lawan, wanda ya wakilci mazaɓar Bagwai/Shanono a jihar Kano, na cikin jerin mutane 175 da aka ba su afuwar shugaban ƙasa.

Farouk Lawan ya dura a kan Kwankwasiyya
Hoton Shugaba Tinubu yana gaisawa da Hon. Farouk Lawan, Rabi'u Musa Kwankwaso Hoto: Hon Faruq M Lawan/Rabiu Musa Kwankwaso
Source: Facebook

Daily Trust ta wallafa cewa an yanke masa hukunci a shekarar 2021 bisa tuhumar karɓar cin hanci domin cire sunan kamfani daga jerin waɗanda aka zarga da hannu a badakalar tallafin mai na 2012.

Yadda dan majalisar Kano ya sha dauri

BBC Hausa ta ruwaito cewa bayan ya kammala zaman gidan yari a watan Oktoba na 2024, Hon Farouk ya bayyana cewa halin da ya shiga ta sauya masa tunani game da siyasa da amana.

Tsohon dan majalisar ya nuna takaici da yadda kungiyar Kwankwasiyya ta yi watsi da shi a lokacin da yake cikin hali har ta kai shi ga zaman gidan yari.

Ya bayyana cewa:

“Duk lokacin da Allah ya jarrabce ka, sai ya ba ka damar gane waɗanda da gaske suke tare da kai.”

Ya kara da cewa wani muhimmin jigo a kungiyar bai taɓa kiran don taya shi jaje ko taya shi murna da ‘yancin da ya samu shekara guda da ya fitowarsa.

Kara karanta wannan

Dangantaka ta yi tsami tsakanin Wike da Tinubu? An ji gaskiyar abin da ya faru

Farouk: Na umarci masoyana su zabi NNPP

Tsohon dan majalisa, Hon. Farouk Lawan ya ce ko da yake yana cikin jam’iyyar PDP lokacin da yake gidan yari, ya umarci magoya bayansa su goyi bayan NNPP a zaɓen 2023.

Hon Farouk Lawan ya zargi Kwankwasiyya da watsi da shi
Hoton Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso Hoto: Rabiu Musa Kwankwaso
Source: Facebook

Sai dai yanzu yana ganin jam’iyyar ba da dace da bukatunsa na siyasa ba:

“A ganina, siyasa ya kamata ta zama mai fadi da ƙayatarwa. Amma NNPP a yanzu tana da kankanta, ba ta dace da buri na na siyasa ba.”

Ya bayyana cewa zai fi mayar da hankali kan babban sahun siyasar ƙasa, maimakon takura kansa a cikin ƙungiya ko jam’iyyar da ba ta da tasiri a manyan lamurra.

Tsohon dan majalisar Kano ya samu 'yanci

A baya, kun samu labarin cewa tsohon ɗan Majalisar Tarayya daga jihar Kano, Hon. Farouk Lawan, ya shaki iskar ‘yanci bayan zaman gidan yari na tsawon shekaru biyar

Tsohon 'dan majalisa, Farouk Lawan ya shahara a siyasar Najeriya musamman a lokacin da yake wakiltar mazaɓar Bagwai/Shanono a Majalisar Tarayya, amma lamari ya canja masa.

Kara karanta wannan

Bakary: Dan adawar Kamaru ya ce ya kayar da Paul Biya a zaben shugaban kasa

A loakcin da ya shugabanci Kwamitin Binciken Badakalar Tallafin Mai, an kama shi da karɓar $500,000 daga cikin adadin da ake cewa ya nema, wato $3m daga dan kasuwa Femi Otedola.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng