Daga Gidan Gyaran Halin Kano, An Mayar da Abduljabbar Nasiru Kabara Abuja

Daga Gidan Gyaran Halin Kano, An Mayar da Abduljabbar Nasiru Kabara Abuja

  • Hukumar NCoS ta Kano ta tabbatar da cewa ta mayar da Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara wani gidan gyara hali a birnin tarayya
  • Mai magana da yawun hukumar, Musbahu Kofar Nassarawa, ya ce matakin ya yi daidai da dokokin aiki da tsarin tsaro da hukumar ke bi
  • NCoS ta tabbatar da cewa sauya wurin ba zai shafi hakkokin shari’a, walwala da damar kare kansa ta doka ta ba Abduljabbar ba

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar – Hukumar kula ga gidajen gyaran hali (NCoS) ta tabbatar da cewa ta mayar da Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara, wani sabon gidan gyara hali da ke karkashin ikon tarayya.

Wannan mataki na zuwa ne bayan wani bincike da hukumar ta gudanar bisa ga ka’idojin gudanarwa, da nufin tabbatar da tsaro, da kula da yanayi na gyaran hali ga masu laifi.

Kara karanta wannan

"Ba siyasa ba ce": Jagoran APC ya kare yafiyar Tinubu ga masu manyan laifuffuka

Sheikh Abduljabbar Kabara
Sheikh Abduljabbar da aka daure kan batanci a Kano. Hoto: Ashabul Kahfi TV
Source: UGC

Vanguard ta wallafa cewa mai magana da yawun hukumar, Musbahu Kofar Nassarawa ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata ga manema labarai a Kano.

Dalilin fitar da Abduljabbar Kabara daga Kano

A cewar Musbahu, sauya wurin Abduljabbar zuwa wani gidan gyara hali na tarayya ba wani abu ba ne da ya saba wa tsarin aikin hukumar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Domin a cewarsa, doka ta ba da cikakken iko wajen raba fursunoni bisa la’akari da matakin tsaro da kuma bukatun gyaran hali.

Ya bayyana cewa wannan mataki ya dace da tanadin dokar hukumar ta shekarar 2019, wadda ta tanadi cewa ana iya mayar da kowane mai laifi zuwa cibiyar da ta dace da matsayinsa.

Leadership ta rahoto ya ce hukumar na gudanar da irin wannan sauyi lokaci zuwa lokaci domin tabbatar da ingantaccen tsarin kula da fursunoni a fadin Najeriya.

Za a kare hakkokin Abduljabbar Kabara

Kara karanta wannan

Asiri ya tonu a Amurka: IMF ya ce ana fitar da haramtattun kudi daga Najeriya

Kofar Nassarawa ya jaddada cewa wannan mataki bai shafi matsayin shari’ar Sheikh Abduljabbar ba, ko kuma damar da yake da ita ta kai ƙara ko samun wakilci na lauya.

Abduljabbar Nasiru Kabara Kano
Sheikh Abduljabbar Kabara yana wa'azi. Hoto: Ashabul Kahfi TV
Source: UGC

Ya kara da cewa:

“Hukumar tana tabbatar da cewa dukkan hakkokin doka na Abduljabbar da walwalarsa suna cikin kariya, kamar yadda doka ta tanada.”

Ya ce manufar hukumar ita ce tabbatar da tsaron rayuka, gyaran halin masu laifi, da kuma taimaka musu wajen sake hadewa da al’umma bayan kammala wa’adin hukuncinsu.

Sauya wa Abduljabbar Kabara waje na kan doka

Musbahu ya ce sauya wa Sheikh Abduljabbar Kabara waje zuwa cibiyar da ke karkashin ikon tarayya ya yi daidai da bukatar tsara fursunoni gwargwadon yanayinsu da halin da suke ciki.

Hukumar ta ce tana yin hakan ne don tabbatar da cewa duk wani fursuna yana samun kulawa mai kyau, da kuma damar koyon sana’o’i ko ilimi don gyaran rayuwarsa.

Triumph ya yi bayani bayan zama da Shura

A wani labarin, mun rahoto muku cewa Sheikh Shuaibu Abubakar Lawan ya yi hira da manema labarai bayan zama da shura.

Kara karanta wannan

Mai gidan marayu ya gamu da fushin kotu bayan kama shi da yaran Kano 8 da aka sace

Malamin da ake kira Triumph ya bayyana cewa sun yi zama kuma ya amsa dukkan tambayoyin da aka masa yayin tattaunawar da suka yi.

Ya yi karin haske da cewa bai ba jama'a hakuri saboda ya gaza kare abin da ya fada ba, sai dai ya ce wasu ba su fahimci abin da ya fada ba.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng