"Ba Siyasa ba ce": Jagoran APC Ya Kare Yafiyar Tinubu ga masu Manyan Laifuffuka
- Jigo a jam’iyyar APC, Abayomi Mumuni, ya ce yafiyar shugaban kasa ba rashin adalci ba ne, illa wata dama ce ta jin kai
- Ya ce yafiyar da aka bai wa wasu ‘yan kasa da aka yankewa hukunci, ciki har da masu laifin kisan kai, mataki ne na jin kai
- Abayomi Mumuni ya bukaci gwamnati ta kara bayani game da yadda ake zabar wadanda za su ci gajiyar wannan gafara
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT, Abuja – Wani jigo a APC, Abayomi Nurain Mumuni, ya goyi bayan matakin da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya dauka na yafe wa wasu ‘yan Najeriya.
Shugaba Bola Tinubu ya yafe wa wasu ‘yan Najeriya da aka yankewa hukunci, matakin da ke kara tayar da kura a fadin kasar.

Kara karanta wannan
Daga karshe, an garzaya da ministan Tinubu ketare domin jinyar cutar da ke damunsa

Source: Facebook
Jaridar Vanguard ta wallafa cewa wannan gafara, wacce ta hada da wasu da aka same su da manyan laifuffuka kamar kisan kai, ta jawo surutu daga bangarori da dama.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jagora a APC ya yabi matakin Tinubu
Independent ta wallafa cewa a wata sanarwa da ya fitar ta hannun hadiminsa na yada labarai, Rasheed Abubakar, Mumuni ya ce yafiyar na cikin ikon Shugaban Kasa.
Ya bayyana cewa wannan yafiya tana da tushe a kundin tsarin mulki, kuma tana da nufin karfafa adalci, tausayi da gyaran hali.
Ya ce shugaban kasa Tinubu na kokarin daidaita tsakanin hukunci da gafara ba tare da rage girman laifi ko raina wahalar wadanda abin ya shafa ba.
Alhaji Mumuni ya ce irin wannan gafara abu ne da ake aikatawa a kasashen da ke tafiyar da dimokuradiyya, musamman idan aka lura da wasu dalila.
Mumuni ya nemi gwamnatin APC ta kara bayani
Daga cikin dalilan da jagora a APC ya bayar irin su cunkoson gidajen yari, gyaran halin fursunoni, da kuma bukatar sake hada al’umma da wadanda suka gyaru.
Alhaji Mumuni ya ce:
“Wasu daga cikin fursunonin sun nuna nadama da kokarin gyara kansu. Ba su dama ta dawo cikin al’umma zai ba su kwarin gwiwa su zama ‘yan kasa nagari.”
Ya kara da cewa hakan zai rage nauyin da cunkoso ke dora wa gidajen yari, tare da kawo sauki ga ‘yan uwan fursunonin da ke fama da matsin tattalin arziki.
Mumuni ya kuma bukaci gwamnati ta fito fili da ka’idojin zabar wadanda ake yi wa gafara tare da tabbatar da an saka tsarin lura da su bayan an sako su.
Ya kara da cewa:
“Jama’a za su fi yarda da irin wannan mataki idan sun ga ana yin sa bisa gaskiya da adalci — ba saboda son rai ko siyasa ba.”
Dan ta'adda ya ci moriyar afuwar Tinubu
A baya, mun wallafa cewa Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya sassauta wa Kelvin Oniarah, wanda aka fi sani da Ezigbe, hukuncinsa daga shekaru 20 zuwa 13 ta hanyar afuwa.
Gwamnati ta ce an rage hukuncin Ezigbe ne saboda ganin yadda ya nuna nadama da kuma shiga karatu a National Open University of Nigeria (NOUN) daga gidan yari.
Rahotanni sun tabbatar da cewa Ezigbe ya kasance ɗaya daga cikin 'yan ta'adda da suka addabi jihar Delta musamman wajen ayyukan garkuwa da mutane, a yankin Kokori.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

