Dalilin Majalisa na Kafa Kwamiti kan Zargin Yi wa Kiristoci Kisan Kiyashi a Najeriya

Dalilin Majalisa na Kafa Kwamiti kan Zargin Yi wa Kiristoci Kisan Kiyashi a Najeriya

  • Majalisar Dattawa ta kafa kwamitin mutane 12 don nazari kan zargin kisan kiyashi kan Kiristoci a ƙasar nan
  • Majalisa ta ce kamitin zai tattara bayanai, ya nemi hujjoji, sannan ya tuntubi majalisar Amurka da ta yi zargin
  • Sannan ta ce za a tura wata tawaga daga kasar nan zuwa Amurka domin bayyana matsayin Najeriya kan zargin

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT, Abuja Majalisar dattawan Najeriya ta bayyana dalilanta na kafa kwamitin mutane goma 12 kan zargin yi wa Kiristoci kisan kiyashi a kasar nan.

Wannan mataki ya biyo bayan wata muhawara da ta barke a majalisar sakamakon maganganun wani dan majalisar Amurka da suka jawo cece-kuce a duniya.

Majalisar Dattawa ya zauna kan kisan kiristoci
Wasu daga cikin Sanatoci yayin zaman majalisa Hoto: The Nigerian Senate
Source: UGC

BBC Hausa ta wallafa cewa a lokacin wani zama na sirri da majalisar ta gudanar a ranar Talata, 'yan majalisar sun tattauna kan yadda ya dace a mayar da martani kan zargin.

Kara karanta wannan

2027: Majalisa ta yi wa 'yan Najeriya albishir kan gyaran dokar zabe

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Majalisar Najeriya ta zauna kan batun kisan Kiristoci

Jaridar Vanguard ta wallafa cewa Majalisa na shirin daukar matakan diflomasiyya domin kada al'amarin ya shafi dangantakar kasashen waje.

Wasu sanatoci sun jaddada bukatar gudanar da bincike cikin natsuwa da adalci kafin yanke hukunci a kan zargin.

Mai tsawatarwa a majalisa, Dr. Mohammad Tahir Monguno, ya ce an kafa kwamitin ne domin tattara sahihan bayanai.

Sannan kwamitin zai tantance hujjoji da kuma bai wa majalisar shawarwari masu ma'ana ta yadda za a bullo wa lamarin.

Ya bayyana cewa aikin kwamitin shi ne zai gano bakin zaren ta hanyar ci gaba da nazari da kuma tattaunawa da masu ruwa da tsaki a fannonin tsaro da jin kai.

'Yan Majalisar Tarayya za su yi bincike

Monguno ya kara da cewa kwamitin zai nemi hadin kai da hukumomi daban-daban ciki har da na cikin gida da na kasashen waje domin samun cikakken bayani.

Kara karanta wannan

Sarkin Musulmi ya magantu kan neman 'raba' Najeriya a gaban gwamnoni a Legas

Ya ce:

"Za mu yi aiki tukuru mu gano hakikanin matsalar domin kada a yanke hukunci bisa zato ko rauni."

Majalisar ta nuna damuwa cewa idan an yarda da zargin ba tare da cikakken bincike ba, hakan na iya haifar da daukar matakai da za su shafi tattalin arzikin Najeriya.

Majalisa ta kafa kwamitin mutum 12 kan zargin kisan kiristoci
Hoton Shugaban Majalisar Dattawa, Akpabio Hoto: The Nigerian Senate
Source: Facebook

Dr. Muhammad Tahir Munguno ya ce:

"Za a fahimtar da majalisar Amurka cewa zargin ba haka ba ne, domin an fi kashe musulmi a matsalolin tsaron Najeriya."

Majalisar ta kuma jaddada bukatar kaucewa yada bayanai marasa tushe wanda ka iya kara rura wutar rikici.

Ya ce kwamitin zai gabatar da rahoto nan gaba kadan da shawarwari kan matakai masu dorewa don magance rikice-rikicen tsaro da kare hakkin addinai a Najeriya.

Majalisar Musulunci ta magantu kan kisan kiristoci

A baya, mun wallafa cewa Majalisar Kolin Musulunci ta Najeriya (NSCIA) ta yi karin haske kan zarge-zarge da ake yi na cewa ana kai wa Kiristoci kisan kiyashi a Najeriya.

Kara karanta wannan

Ana wata ga wata: Majalisa na son dawo da zaben 2027 zuwa 2026

A sanarwar da mataimakin mai ba da shawara kan shari’a na NSCIA, Imam Haroun Muhammad Eze, ya sanya hannu, majalisar ta ce irin wannan furuci zai jawo matsala a cikin al'umma.

Majalisar ta yi kira ga hukumomi da ‘yan kasa da su fito fili wajen ƙaryata irin waɗannan zarge-zarge don kada a ci gaba da baza labaran da ba su da tushe ballantana makama.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng