Sojoji Sun Yi Artabu da 'Yan Ta'adda ana Batun Sulhu a Katsina, Mutum 12 Sun Kwanta Dama

Sojoji Sun Yi Artabu da 'Yan Ta'adda ana Batun Sulhu a Katsina, Mutum 12 Sun Kwanta Dama

  • Sojojin Najeriya sun yi zazzafan dauki ba dadi da wasu miyagun ‘yan bindiga a kauyen Mabai da ke jihar Katsina
  • Rikicin ya faru ne bayan wani taron zaman lafiya da aka gudanar a Kakumi, a ke karamar hukumar Bakori a jihar
  • Duk da wuta da sojojin u ka ba su, ‘yan ta’adda sun kwantar da jami’an rundunar sojin kasar nan biyu a gadon asibiti

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Katsina – Sojojin Najeriya sun yi nasarar hallaka wasu ‘yan bindiga 12 a wani artabu da ya ɓarke da yammacin ranar Lahadi a kauyen Mabai.

An yi dauki ba dadin a cikin ƙaramar hukumar Kankara ta Katsina sa’o’i kadan bayan wasu daga cikin jagororin ‘yan ta’adda sun yi yaryjejeniya da mazauna kananan hukumomi uku.

Kara karanta wannan

Katsina: Kananan hukumomi 3 sun zauna da ƴan bindiga, an kulla yarjejeniyar sulhu

Sojoji sun fafata da yan ta'adda a Katsina
Wasu daga cikin sojojin Najeriya na kasa (a hagu), jiragen yaki (a dama) Hoto: HQ Nigerian Army
Source: Facebook

Zagazola Makama ya wallafa cewa lamarin ya faru ne da misalin 5.30 na yamma, jim kaɗan bayan wani taron zaman lafiya da aka gudanar a kauyen Kakumi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sojoji sun gwabza da ‘yan ta’adda a Katsina

Majiyoyi sun bayyana cewa ‘yan bindigan sun wuce kusa da sansanin sojoji da ke Mabai, inda daga nan ne suka bude wuta kan dakarun.

Wannan al’amari ya haifar da musayar wuta mai zafi inda aka kwashe tsawon lokaci ana musayar wuta da dauki ba dadi tsakaninsu.

A ƙarshe, dakarun sun yi galaba a kan ‘yan ta’addan, tare da kashe su 12 a wurin, yayin da wasu suka tsere da raunuka, yayin da aka kara tsaurara tsaro a yankin.

Sojoji sun jikkata a Katsina

A yayin gumurzu da ‘yan bindigar, sojoji biyu sun samu raunuka, inda aka garzaya da su zuwa asibitin soji da ke Katsina domin samun kulawar likitoci.

Sojoji sun jikkata a Katsina
Hoton taswirar jihar Katsina, inda aka fafata da 'yan ta'adda Hoto: Legit.ng
Source: Original

Majiyoyin tsaro sun tabbatar cewa an shawo kan halin da yankin ke ciki, tare da ƙaddamar da sintiri da sa ido na musamman don dakile wani harin bazata.

Kara karanta wannan

Dakarun sojoji sun ragargaji 'yan ta'addan Boko Haram a Borno

Rundunar sojin Najeriya ta sha nanatawa cewa tana da cikakken niyyar murƙushe duk wani abu da zai barazana ga zaman lafiya da tsaron rayuka da dukiyoy.

Yankin Kankara na daga cikin wuraren da ke fama da hare-haren ‘yan bindiga da garkuwa da mutane, duk da jama’a suna sulhu da kungiyoyin ‘yan ta’adda.

An zauna da 'yan ta'adda a Katsina

A baya, mun wallafa cewa kananan hukumomi uku — Bakori, Funtua da Malumfashi — sun hallara a garin Kakumi da ke karamar hukumar Bakori a jihar Katsina don zama da 'yan ta'adda.

Sun hallara a Kakumi domin su tattauna tsakaninsu da shugabannin wasu daga cikan daban 'yan bindiga da su ka hana su zama lafiya, bayan garkuwa da mutane da kashe jama' a ba kakkauta wa.

A cikin yarjejeniyar, ‘yan bindigan sun yi alkawarin dakatar da hare‑hare da sace‑sace daga ranar 12 ga Oktoba na shekarar 2025, musamman a yankunan da rikici ya shafa domin jama'a su sarara.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng