Sheikh Gumi Ya Hango Mafita kan 'Yan Bindiga a Sulhun Hamas da Isra'ila

Sheikh Gumi Ya Hango Mafita kan 'Yan Bindiga a Sulhun Hamas da Isra'ila

  • Malamin Musulunci, Sheikh Ahmad Gumi ya sake kira ga hukumomi kan bukatar yin sulhu da 'yan bindiga a Najeriya
  • Dr. Gumi ya ambaci yarjejeniyar Hamas da Isra’ila a matsayin misalin cewa ana iya samun sulhu ta hanyar tattaunawa
  • Malamin ya ce idan manyan kasashe na iya sulhu da kungiyoyin da ake kira 'yan ta’adda, Najeriya ma za ta iya hakan

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Gabatarwa
Jihar Kaduna – Fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Ahmad Gumi, ya sake jaddada bukatar gwamnatin tarayya ta bude hanyoyin tattaunawa da ’yan bindiga.

Bajimin malamin ya yi kiran ne domin kawo karshen rikici da kashe kashen da ya dade yana addabar Arewacin Najeriya.

Sheikh Ahmad Mahmud Gumi
Sheikh Gumi yayin da ya ke wani wa'azi. Hoto: Dr Ahmad Abubakar Mahmud Gumi
Source: Facebook

Malamin ya bayyana haka ne a shafinsa na Facebook ranar Litinin, inda ya ce hanyar da ta fi dacewa wajen samar da tsaro mai dorewa ita ce zaman lafiya ta hanyar fahimtar juna.

Kara karanta wannan

'Yaki ya kare,' An saki Falasdinawa yayin da Hamas ta saki mutanen Isra'ila

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ambaci yarjejeniyar sulhu tsakanin Isra’ila da Hamas a matsayin hujja cewa koda a rikici mai tsanani, tattaunawa na iya kawo mafita.

Ahmad Gumi ya nemi tattaunawa da ’yan bindiga

Sheikh Gumi ya ce yarjejeniyar zaman lafiya tsakanin Isra’ila da Hamas da ta samu jagorancin Donald Trump, ta nuna cewa ba abin kunya ba ne gwamnati ta tattauna da masu daukar makami.

A cewarsa, Isra’ila ta amince da janye dakarunta a matakai daban-daban tare da sakin 'yan Falasdinu, yayin da Hamas ta saki wasu 'yan Isra’ila da ta kama.
Punch ta wallafa cewa ya ce:

“Sulhu tsakanin Isra’ila da Hamas, wadanda ake kiran ’yan ta’adda, Amurka ce ta shiga tsakani wajen kulla yarjejeniyar.
"To waye zai ce ba a iya yin sulhu da ’yan ta’adda? Ku yi sulhu da ’yan bindiga mu huta.”

Dalilin Gumi na goyon bayan tattaunawa

Sheikh Gumi ya yi nuni da cewa Najeriya ta shafe shekaru tana fama da rikicin ’yan bindiga da garkuwa da mutane, amma duk da tsauraran matakan da ake dauka, matsalar na kara kamari.

Kara karanta wannan

Katsina: Kananan hukumomi 3 sun zauna da ƴan bindiga, an kulla yarjejeniyar sulhu

Bayanansa sun nuna cewa tattaunawa da kungiyoyin da ke da hannu a rikicin ita ce hanya mafi sauki da za ta iya kawo karshen zubar da jini da asarar rayuka.

Malamin ya dade yana kira a kawo karshen tashin hankali ta hanyar tattaunawa da bangarorin da ake kallon su a matsayin masu tayar da hankali.

Yadda aka kawo karshen yaki a Gaza

Yarjejeniyar sulhu tsakanin Hamas da Isra’ila da aka cimma a ranar Litinin ta kawo karshen yakin da ya dauki tsawon shekaru biyu a Gaza, wanda ya hallaka dubban mutane.

A karkashin yarjejeniyar, Hamas ta saki wasu fursunonin Isra’ila yayin da Isra’ila ta fara sakin Falasdinawa fiye da 1,900 daga gidajen yari, tare da janye dakarunta daga wasu yankuna.

Sheikh Gumi ya ce wannan lamari ya zama darasi ga Najeriya, domin ya nuna cewa tattaunawa ba rauni ba ne, illa dai mataki ne na hikima da neman zaman lafiya.

An yi sulhu da 'yan bindiga a Katsina

Kara karanta wannan

Shehi ya nemi zama da Kiristoci kan zuwan Isra'ila Najeriya da barazanar yaki

A wani rahoton, kun ji cewa an samu karin kananan hukumomi uku da suka yi sulhu da 'yan bindiga domin kawo zaman lafiya.

Shugaban karamar hukumar Bakori ta jihar Katsina ya bayyana cewa sulhu da 'yan bindiga ne hanyar kawo karshe kashe-kashe.

Duk da maganar da ya yi, wasu mutane na ganin cewa sulhu da 'yan bindiga ba lallai ya dore ba kasancewar an samu matsala a baya.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng