'Yan Uwan Bilyaminu Sun Shiga Kunci, Sun Yi Tir da Tinubu Ya Yafe wa Maryam Sanda
- Dangin marigayi Bilyaminu Bello sun soki yafiyar da Shugaban Kasa Bola Tinubu ya yi wa Maryam Sanda, wadda aka tabbatar ta kashe mijinta
- Sun ce wannan mataki na gwamnatin Tinubu ta dauka babban rashin adalci ne da ya sake bude masu zafin kisan 'dan uwansu da Maryam ta yi
- Iyalin sun bayyana cewa Maryam ba ta taɓa nuna nadama ba tun bayan kisan, wannan yafiya da Bola Tinubu ya yi ya kara jefa su a cikin wani hali
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Iyalin marigayi Bilyaminu Bello sun bayyana fushinsu kan yafiyar shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ga Maryam Sanda, matar da aka tabbatar da ta kashe mijinta a 2017.
A cikin wata sanarwa da Dr Bello Mohammed ya fitar a madadin iyalin a ranar Litinin, sun ce wannan yafiya abu ne mai matukar muni da iyalin su ka fuskanta.

Source: Facebook
Jaridar Punch ta wallafa cewa iyalan sun bayyana cewa wannan matakin ya sake buɗe masu radadin bayan kotu ta yi hukunci a kan kisan Bilyaminu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yafewa Maryam Sanda ya fusata iyalan Bilyaminu
Daily Post ta wallafa cewa iyalan Bilyaminu Bello sun ce sun fara samun sauki bayan da kotu ta yanke wa Maryam hukuncin kisa a ranar 27 ga Janairu, 2020.
Sanarwar da iyalan 'yan uwan marigalin su ka fitar ta ce:
“Yanzu Maryam Sanda za ta rika yawo a doron ƙasa kamar wadda ba ta taɓa aikata laifi ba, bayan ta kashe mijinta. Wannan babban zalunci ne da ya sake jefa mu a cikin takaici."
Iyalin sun bayyana cewa kotun daukaka ƙara ta tabbatar da hukuncin kisan da kotun farko ta yanke, sannan kotun koli ma ta tabbatar da shi a ranar 27 ga Oktoba, 2023.
Sun ce wannan ya ba su ɗan nutsuwa bayan sun tabbatar gaskiya ta yi aiki a kan kashe masu 'dan uwa da aka yi.
Iyalan Bilyaminu: "Maryam ba ta yi nadama ba"
'Yan uwan Bilyaminu sun bayyana cewa babu wata nadama da Maryam Sanda ta nuna, saboda haka sakinta ba karamin takaici ba ne.
Sun ce:
“Duk da cewa Maryam ba ta nuna nadama ba ko na ɗan lokaci, mun rungumi hukuncin da muke ganin adalci ne. Amma yanzu an sake caccaka mana wuƙa a ciki.”

Source: Facebook
Sun yi zargin cewa gwamnatin tarayya ta watsar da kimar hukuncin kotuna saboda kawai ta amince da roƙon iyalin Maryam.
A cewar su, hakan ya nuna an fifita tausayi ga mai laifi fiye da jin ƙuncin waɗanda suka rasa ɗan uwa a hannunta.
Sun kuma jaddada cewa Maryam ta raba ‘ya’yanta da kulawar uba da kauna tun kafin wannan yafiya, don haka ba a kamata a yi amfani da su wajen neman jinƙai ba.
Sun ce:
“A gare mu, wannan yafiya ba komai ba ce face ƙoƙarin faranta wa iyalin Maryam rai, alhali an ƙara cutar da mu."

Kara karanta wannan
Maryam Sanda da wasu sanannun mutane 5 da suka shiga cikin wadanda Tinubu ya yi wa afuwa
Sun ƙara da cewa:
“Mun bar wannan al’amari ga Mahalicci, wanda shi kaɗai ne zai yi cikakken hukunci a Ranar Sakamako.”
Yaron Tinubu ya fusata kan Maryam Sanda
A baya, kun ji cewa makusancin Shugaban Kasa Bola Tinubu, Dr. Josef Onoh, ya bayyana rashin amincewa da afuwar da Tinubu ya yi wa wasu mutane a makon da ya wuce.
Daga cikin wadanda Dr. Onoh ke takaicin yi masu afuwa akwai Maryam Sanda, matar nan da kotunan Najeriya su ka tabbatar da cewa ta kashe mijinta, Bilyaminu Belloi.
Ya ce wannan afuwar ta saba da adalci da ƙa’idoji, sannan tana iya rage martabar Najeriya a idon duniya, tare da sanya jami’an tsaro su ji kamar an watsa masu kasa a ido.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

