A Karon Farko, Kwamishinan Yan Sandan Kano Ya Yi Magana da Gwamna Abba Ya ce a Kore Shi
- Kwamishinan ‘yan sandan Kano, Ibrahim Adamu Bakori, ya yi magana a kan zargin samun sabani da gwamnan jihar, Abba Kabir Yusuf
- A ranar 1 ga watan Oktoba, 2025 ne Mai girma Gwamna Abba ya zargi CP Bakori da ci wa mutanen Kano fuska da kin girmama shi
- Gwamnan ya bayyana haka ne bayan Kwamishinan 'yan sandan ya janye jami'ansa daga faretin ranar 'yancin kai ba tare da sanarwa ba
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Kwamishinan ‘yan sandan Kano, Ibrahim Adamu Bakori, ya yi karin bayani a kan sabanin da ake ganin ya samu da Gwamna Abba Kabir Yusuf.
Bayaninsa na zuwa ne akalla kwanaki 13 bayan Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bukaci a canja Kwamishinan 'yan sandan a jihar saboda CP Bakori ya ki aikinsa yadda ya dace.

Source: Facebook
Daily Trust ta wallafa cewa a martanin Kwamishinan, ya bayyana cewa duk da kiran da Abba Kabir Yusuf ya yi, har yanzu yana da alaka mai kyau da Gwamnan.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
CP Bakori ya fadi alakarsa da Gwamnan Kano
Daily Post ta ruwaito cewa da yake magana da manema labarai a ofishin rundunar a Kano, CP Bakori ya ce ba wata matsala a tsakaninsa da Gwamnan Kano.
Ya kara da cewa kowannensu yana aiwatar da ayyukansa ne bisa kundin tsarin mulkiin kasa wajen aikata duk abin da ya dace.
A kalamamsa:
“Dukkanninmu muna yin aikinnanmu ne, kuma har yanzu mu abokan juna ne, muna haɗa kai wajen tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyi a jihar."
A ranar 1 ga watan Oktoba ne dai Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana takaicin yadda Kwamishinan 'yan sandan ya ki halartar faretin zagayowar ranar 'yancin Najeriya ba tare da dalili ba.

Kara karanta wannan
An fara guna guni da Majalisar Benue ta amince gwamna ya karbo bashin Naira biliyan 100
'Yan sandan jihar Kano sun yi kame
Kwamishinan ya kuma sanar da cafke mutum tara da ake zargi da fashi da makami a sassan Kano, ciki har da wani harin da aka yi a Unguwar Wambai, Dorayi Babba.
Ya ce an kuma yi nasarar kwato motar Toyota Yaris, kuɗin Najeriya da na waje da suka kai Naira miliyan 3.7, da wayoyi guda uku da wasu kayayyaki masu muhimmanci daga hannunsu.

Source: Facebook
Kwamishinan ya ce:
“An kama su ne bayan rahoton da muka samu a ranar 8 ga Oktoba, 2025, da 2:00 na dare."
Ya kara da cewa jami'ansu sun kuma gudanar da samame wanda ya kai ga kama sauran takwas a Kano da Kaduna. Ya ce sun amsa aikata wasu manyan laifuka a Kano, Kaduna da Abuja.
CP Bakori ya yaba wa jami’an 'yan sandan da suka gudanar da aikin bisa ƙwarewa da jajircewa, yana mai kira su ci gaba da aiki tukuru don kare jama’ar Kano.
Kwamishinan 'yan sandan Kano ya fusata Gwamna
A baya, mun wallafa cewa gwamnatin jihar ta ce matakin da Kwamishinan ‘yan Sanda, Ibrahim Adamu Bakori ya ɗauka a ranar 1 ga watan Oktoba babbar barazana ce ga tsaro.
Lauyan Gwamnatin Kano, AbdulKarim Maude, ya bayyana cewa janyewar ‘yan sanda daga filin biki ya saba wa umarnin gwamnati kuma hakan ya nuna watsi da ikon gwamna a fannin tsaro.
Maude ya ce ya wajaba Kwamishinan ya bi umarnin Gwamnan jihar da ya ke aiki a harkokin tsaro da zaman lafiya, sai dai idan Shugaban Kasa ya bayar da umarni daban.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

