Ta Faru Ta Kare: Kwamishinoni da Manyan Hadiman Gwamna Sun Bar PDP Sun Koma APC
- 'Yan majalisar zartarwar Gwamna Peter Mbah sun bar PDP, inda ake sa ran APC za ta karbe su a gobe, 14 ga Oktoba, 2025
- Hadiman Mbah, ciki har da kwamishinoni, sun bayyana goyon bayansu ga APC, inda suka rera yabo ga Shugaba Bola Tinubu
- Wannan sauyin siyasa zai sanya Enugu ta zama jiha ta farko daga Kudu maso Gabas da ke karkashin APC tun bayan 2023
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Enugu – Kafin sanarwar ficewar Gwamna Peter Mbah daga jam’iyyar PDP zuwa APC a ranar Talata a hukumance, dukkan mambobin majalisar zartarwa ta jihar Enugu sun sauya sheka.
Wannan matakin na zuwa ne bayan tsohon shugaban matasan PDP a kasa, Sunday Udeh-Okoye, ya sanar da ficewarsa daga PDP, yana mai cewa ta rasa akida da darajar siyasa.

Source: Twitter
Enugu: Mukarraban gwamna sun yi watsi da PDP
Mai taimaka wa gwamna kan harkokin yada labarai, Dan Nwomeh, ne ya tabbatar da sauyin sheka a wani bidiyo da ya wallafa a shafinsa na X a ranar Litinin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cikin bidiyon, an ga kwamishinoni da manyan hadiman gwamnati suna bayyana goyon bayansu ga jam’iyyar APC.
An kuma ga yadda suke rera wakokin yabo ga Shugaba Bola Tinubu tare da bayyana cewa sun tsunduma cikin APC da karfinsu.
“Mambobin majalisar zartarwa ta Enugu sun shiga APC tare da Gwamna Peter Mbah kansu tsaye,” in ji Nwomeh.
Daga cikin wadanda suka sauya sheka akwai Lawrence Ezeh, kwamishinan kirkire-kirkire da kimiyya; Amaka Ngene, shugabar hukumar makarantun fasaha da sana’o’i; da kuma Felix Nnamani, kwamishinan kwadago da aiki.
Enugu: APC ta shirya taron maraba da Mbah
Rahotanni sun tabbatar cewa jam’iyyar APC ta kammala shirin karɓar Gwamna Mbah a wani babban taro da za a gudanar a Enugu a ranar Talata.
Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa tuni aka daga tutar APC a fadar gwamnatin Enugu a daren Lahadi, abin da ya tabbatar da jita-jitar da ke yawo tun makonnin baya.
Jami’an jam’iyyar sun fara shiri don maraba da manyan baƙi daga sassan ƙasa a bikin da ake sa ran zai jawo hankalin shugabannin siyasa na kasa da yankin Kudu maso Gabas.

Source: Twitter
Sabon sauyin siyasa a yankin Kudu maso Gabas
Ficewar Gwamna Mbah daga PDP zuwa APC na nuna sabon juyin siyasa a yankin Kudu maso Gabas, musamman ma a jihar Enugu da ta kasance gidan PDP tun 1999.
Idan aka kammala sauyin, Enugu za ta zama jiha ta farko daga yankin Kudu maso Gabas da ke karkashin APC tun bayan zaben 2023.
Sai dai har yanzu Gwamna Mbah bai fadi komai a hukumance ba, amma yawancin hadimansa da abokansa sun riga sun canza sheka.
Rahotanni sun bayyana cewa wannan cigaba ya zama wani babban koma-baya ga PDP, wadda ke fama da ficewar manyan ’ya’yanta a sassan kasar nan.
APC ta bude kofa ga Gwamna Mbah
Tun da fari, mun ruwaito cewa, APC ta bayyana cewa kofarta a bude take ga Gwamna Peter Mbah a duk lokacin da ya shirya sauya sheka daga PDP.
Tsohon Darakta Janar na Voice Of Nigeria (VON), Osita Okechukwu, ne ya bayyana hakan, yana mai cewa APC na maraba da gwamna Mbah a ko wane lokaci.
Okechukwu dai ya mayar da martani ne kan wani jawabi da aka danganta ga Ministan Kimiyya da Fasaha, Cif Uche Nnaji, wanda ya yi magana kan ’yancin shiga APC.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


