Sojan Najeriya da Ya Bindige Matarsa Ya Bude wa Kansa Wuta, Sun Mutu Dukkansu
- An samu tashin hankali a sansanin soja na Wawa da ke Jihar Neja bayan wani soja ya kashe matarsa kafin ya kashe kansa
- Rundunar sojojin Najeriya ta tabbatar da cewa Kofur Akenleye Femi ne ya aikata laifin ranar 11, Oktoba, 2025 a cikin gidansu
- Rundunar ta ce an fara cikakken bincike don gano musabbabin lamarin tare da daukar matakai don hana sake faruwar haka
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Neja – Wani mummunan lamari ya girgiza sansanin soja na Wawa a Jihar Neja bayan da wani soja ya kashe matarsa sannan ya hallaka kansa.
Lamarin ya faru ne a ranar 11, Oktoba, 2025, inda mazauna sansanin suka fada cikin tashin hankali da mamaki.

Source: Facebook
Rundunar sojojin Najeriya ta tabbatar da faruwar lamarin a cikin wata sanarwa da Mataimakin Daraktan Hulda da Jama’a na sojojin ƙasa, Stephen Nwachukwu, ya wallafa a X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Soja ya kashe kan shi, matarsa a Neja
Darektan ya bayyana cewa wanda ake zargi da kashe matar shi da kuma kansa shi ne Kofur Akenleye Femi na bataliya ta 221 da ke sansanin Wawa.
Sanarwar ta ce an gano gawar sojan da ta matarsa ne a gidansu da ke ɗaki na 24 a wurin zaman ƙananan jami’ai a cikin sansanin, abin da ya jefa jama’a cikin tsananin firgici da mamaki.
Yadda sojan ya nemi izini kafin kisan
Rahotanni sun bayyana cewa kafin aukuwar lamarin, Femi yana bakin aiki amma ya nemi izini daga shugabansa domin zuwa ya biya wata bukata.
Jaridar Punch ta wallafa cewa bayan ya tafi ne daga baya aka gano gawar shi da matarsa a mace a cikin gidan nasu.
Rundunar sojoji ta bayyana cewa wannan lamari abin takaici ne kuma ta yi ta’aziyya ga iyalan mamatan, abokai da duk wanda lamarin ya shafa.
Nwachukwu ya ce sojojin ƙasan Najeriya suna addu’ar samun rahamar Allah ga rayukan ma’auratan da suka mutu cikin wannan hali.
Rundunar sojoji ta fara binciken kisan
Rundunar ta tabbatar da cewa an adana gawar mamatan yayin da bincike mai zurfi ya fara domin gano hakikanin abin da ya jawo lamarin.
An kafa kwamiti na musamman da zai duba al’amuran da suka faru kafin mutuwar su, da duba ko akwai yiwuwar matsala ko rikici a cikin gidan.

Source: Facebook
Rundunar ta yi alkawarin daukar mataki
Birgediya Janar Ezra Barkins, ya bayyana cewa za a gudanar da bincike cikin gaskiya da adalci kan lamarin.
Ya ce sakamakon binciken zai kasance a bude domin a dauki matakan gyara da kariya daga irin wannan lamari a gaba.
Ya kara da cewa rundunar sojoji ta dauki wannan lamari da muhimmanci, musamman wajen kare rayukan jami’anta da iyalansu.
Rundunar ta kuma bukaci jama’a da su guji yada jita-jita a kan lamarin, tana mai jaddada cewa za a sanar da sakamakon binciken da zarar an kammala shi.
Matar soja ta kashe mijinta
A wani jikon, kun ji cewa ana zargin matar wani sojan Najeriya, Laftanar Samson Haruna ta kashe shi.
Rahotanni sun bayyana cewa sojan ya mutu ne bayan an zargi matar da cinna masa wuta da man fetur a Akwa Ibom.
Kamar yadda bayanai suka gabata, rundunar sojojin Najeriya ta tsare matar domin gudanar da cikakken bincike.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


