ADC Ta Yi Kaca Kaca da Tinubu kan Yafe wa Masu Safarar Miyagun Kwayoyi

ADC Ta Yi Kaca Kaca da Tinubu kan Yafe wa Masu Safarar Miyagun Kwayoyi

  • Jam'iyyar 'yan hamayya ta ADC ta dura a kan Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu bayan ya sanar da yafiya ga wasu 'yan Najerita
  • Kakakin jam'iyyar ya bayyana mamaki a kan yadda Shugaban ya rufe idanunsa, ya kuma ayyana afuwa ga masu migayun laifuffuka
  • ADC ta bakin mai magana da yawunta, Bolaji Abdullahi ta bayyana cewa matakin Tinubu babban kuskure ne, kuma abin kunya

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT, Abuja - Jam’iyyar ADC ta yi watsi da matakin da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya dauka na yafewa wasu ’yan Najeriya.

Daga cikin wadanda Bola Tinubu ya yi wa afuwa akwai wadanda aka kama da laifin safarar miyagun kwayoyi da kuma masu fasa kwauri.

ADC ta caccaki Tinubu kan yafe wa wasu 'yan Najeriya
Hoton Shugaba Bola Tinubu, Bolaji Abdullahi Hoto: Hoto: Sanusi Bature D-Tofa, Mallam Bolaji Abdullah
Source: Facebook

Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa ADC ta sanar da fushinta ne a cikin wata sanarwa da Malam Bolaji Abdullahi, kakakin jam’iyyar na kasa ya fitar.

Kara karanta wannan

Atiku ya fusata, ya fadi yadda afuwar Tinubu ta zama barazana ga Najeriya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

ADC ta yi kaca-kaca da Tinubu

An ji jaridar Punch ta ruwaito cewa ADC ta bayyana matakin Shugaba Tinubu a matsayin abin takaici, kuma abin kunya ga kasa baki daya.

Jam'iyyar ta yi gargadi cewa hakan na iya mayar da kokarin da ake yi wajen yaki da shan miyagun kwayoyi baya, sannan zai kara bata wa Najeriya suna a idon duniya.

Kakakin ADC, Bolaji Abdullahi ya ce matakin Tinubu na yafewa wadanda aka kama da laifuffukan da su ka shafi safarar miyagun kwayoyi babbar nakasu ce ga kasa.

Ya ce:

“ADC na kallon wannan yafe wa da aka yi a matsayin abin takaici da kuma wani babban abin kunya ga kasa, wanda ya sabawa manufar amfani da ikon yafiya don gyara kura-kurai da kuma tallafa wa wadanda suka bi ka’idar zaman gidan yari yadda ya dace.”
ADC ta ce akwai matsala a yafe wa wasu 'yan Najeriya
Hoton Shugaban ADC na kasa, David Mark Hoto: 2027 ADC Coalition
Source: Twitter
“Ba mu fahimci abin da Najeriya za ta amfana da shi ba ta hanyar yafe wa wadanda ke da hukuncin daurin rai da rai, alhali ba su gama shekara biyu ba a gidan yari.”

Kara karanta wannan

ADC ta yi baki 1 da Bankin Duniya a kan karuwar talauci a mulkin Tinubu

Najeriya na fama da annobar shaye-shaye – ADC

ADC ta bayyana damuwarta kan yadda Najeriya ke kara shiga cikin matsalar yawan masu amfani da miyagun kwayoyi.

Ta ce rahotanni sun nuna cewa 14.4% na ’yan Najeriya na ta'ammali da miyagun kwayoyi, wanda ya ninka matsakaicin kason duniya har sau uku.

Jam’iyyar ta yaba wa kokarin hukumar NDLEA da sauran hukumomin tsaro da ke fuskantar hadurra don dakile safarar miyagun kwayoyi da kama masu laifi.

Ta ce:

“Wadanda ke aikin yaki da miyagun kwayoyi na cikin tsananin hadari don kare lafiyar al’umma, kuma doka ta tanadi hukunci mai tsauri saboda illa da safarar kwayoyi ke yi ga matasa da tsaron kasa baki daya.”

Jam’iyyar ADC ta ce wannan yafe wa da Tinubu ya yi zai kara lalata matsayin Najeriya a idon duniya, domin za a rika kallonta a matsayin mai sassauci ga miyagun laifuffuka.

Atiku ya dura kan shugaban kasa Tinubu

A baya, kun ji cewa tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya bayyana damuwa game da yadda shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yafe wa wasu mutane a Najeriya.

Kara karanta wannan

Atiku ya shiga sahun masu neman fito da shugaban kungiyar ta'addanci da aka kama tun 2021

Rahotanni sun nuna cewa daga cikin mutum 175 da aka yafe wa, akwai wadanda aka kama da laifuffukan safarar miyagun ƙwayoyi, kisan kai da cin hanci da rashawa.

Atiku ya bayyana cewa bai dace ace a yi afuwa ga waɗanda aka same su da manyan laifuka kamar safarar miyagun ƙwayoyi, garkuwa da mutane, ko kisan kai ba.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng