Sardaunan Zazzau: Jonathan, Atiku, Obi Sun Taya Namadi Sambo Samun Sarauta
- Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Namadi Sambo, ya karɓi sarautar Sardaunan Zazzau daga Sarkin Zazzau, Ambasada Ahmed Nuhu Bamalli
- Tsohon Shugaban Kasa Goodluck Jonathan da tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa Peter Obi sun taya shi murnar sabon sarautar da ya samu
- Rahotanni sun bayyana cewa an gudanar da bikin nadin sarautar ne a fadar Sarkin Zazzau da ke Zariya ranar Asabar, 11 ga Oktoba, 2025
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kaduna – Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Mohammed Namadi Sambo, ya karɓi sarautar Sardaunan Zazzau daga Mai Martaba Sarkin Zazzau, Ambasada Ahmed Nuhu Bamalli.
Rahotanni sun bayyana cewa an yi bikin nadin sarautar ne a wani babban bikin da aka gudanar a fadar Sarkin Zazzau.

Source: Facebook
Bikin ya samu halartar fitattun mutane daga sassan Najeriya daban-daban, ciki har da tsohon Shugaban Ƙasa Goodluck Jonathan kamar yadda ya wallafa a X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jonathan ya taya Namadi murna
Tsohon Shugaban Ƙasa Goodluck Jonathan ya nuna farin cikin samun damar halartar nadin sarautar, inda ya bayyana Namadi Sambo a matsayin mutum mai gaskiya da kishin ƙasa.
A cikin sakon da ya wallafa, Jonathan ya ce:
“Na yi matuƙar farin ciki da kasancewa tare da ɗan’uwana mai girma, tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Namadi Sambo, yayin bikin nadin sa a matsayin Sardaunan Zazzau.”
Ya ƙara da cewa sabon matsayin zai ƙara dankon zumuncinsa da al’umma tare da ƙarfafa sadaukarwarsa wajen tabbatar da zaman lafiya da ci gaban ƙasa.
Peter Obi ya yaba wa Namadi Sambo
Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa, Peter Obi, ya bayyana nadin sarautar a matsayin wata gagarumar shaida ta yadda masarautar Zazzau ke girmama mutanen da suka ba da gudunmawa.
A cikin sakon da ya wallafa a X, Obi ya ce:
“Ina taya ɗan’uwana mai girma, tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa Namadi Sambo, murnar samun wannan sarauta mai daraja.
"Nadin ya nuna amincewar masarautar da hikimarka, amincinka, da jajircewarka wajen ci gaban al’umma.”
Baya ga haka, Obi ya mika godiya ga Sarkin Zazzau bisa cigaba da girmama mutanen kirki a cikin al’umma.

Source: Facebook
Maganar Atiku da Abbas Tajudeen
Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya taya Namadi Sambo murnar nada shi sarautar da aka yi a sakon da ya wallafa a X.
A sanarwar da ya fitar a X, Shugaban majalisar wakilai kuma Iyan Zazzau, Abbas Tajudeen ya taya Namadi Sambo murna bayan halartar taron.
Sanata Lawal Adamu ya taya Namadi murna
Sanata Lawal Adamu ma ya taya tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa murnar Sarautar da aka ba shi.
A cikin sakon da ya wallafa a X, ya ce:
“Ina taya tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa Namadi Sambo murnar nadin sa a matsayin Sardaunan Zazzau. Allah Ya sanya alheri, Amin.”
Sanatan ya bayyana Namadi Sambo a matsayin mutum mai sadaukarwa da natsuwa wanda ya ba da gudunmawa sosai ga harkokin mulki da ci gaban al’umma.
Tinubu ya taya Sardaunan Zazzau murna
A wani rahoton, kun ji cewa shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya taya tsohon mataimakin shugaban kasa murna zama Sardaunan Zazzau.
Shugaba Tinubu ya bayyana cewa nadin sarautar ya nuna yadda Namadi Sambo ya kawo cigaba a lokacin da ya ke rike da madafun iko.
Shugaban kasar ya yaba wa masarautar Zazzau kan cigaba da girmama mutanen da suka yi wa kasa hidima wajen kawo cigaba.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


