Katsina: Kananan Hukumomi 3 Sun Zauna da Ƴan Bindiga, an Kulla Yarjejeniyar Sulhu

Katsina: Kananan Hukumomi 3 Sun Zauna da Ƴan Bindiga, an Kulla Yarjejeniyar Sulhu

  • Kananan hukumomi uku a Katsina sun shiga yarjejeniyar zaman lafiya da ‘yan bindiga domin dakatar da hare-hare a yankin
  • Shugaban karamar hukumar Bakori ya ce tattaunawa da fahimtar juna ne ginshiƙin samun zaman lafiya mai dorewa a Katsina
  • Wasu mutane dai sun nuna shakku kan sabuwar yarjejeniyar bayan irinta da aka yi a wasu garuruwa ta gaza haifar da ɗa mai ido

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Katsina – A wani mataki na dawo da zaman lafiya, kananan hukumomi uku a jihar Katsina sun rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya da wasu gungun ‘yan bindiga.

Wannan mataki, wanda ke nufin kawo ƙarshen hare-hare da sace-sace a yankin, ya dawo da kwanciyar hankali ga al’ummomin da tsoron ‘yan ta’adda ya daɗe yana addaba.

Kananan hukumomi 3 sun kulla yarjejeniyar sulhu da 'yan bindiga a Katsina
Taswirar jihar Katsina da ke a Arewa maso Yammacin Najeriya. Hoto: Legit.ng
Source: Original

An sake yin sulhu da 'yan bindiga a Katsina

Kara karanta wannan

Kebbi: 'Yan bindiga sun yi ta'asa bayan kai mummunan hari, sun fille kan Sarki

Rahoton jaridar Daily Trust ya bayyana cewa Malumfashi, Funtua, da Bakori ne suka shiga cikin sabuwar yarjejeniyar zaman lafiya da ‘yan bindiga.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An gudanar da taron a garin Kakumi, karamar hukumar Bakori, inda wakilan ‘yan bindiga da na al’umma suka tattauna kai tsaye domin fahimtar juna da dakatar da rikici.

Majiyoyi sun tabbatar da cewa shugabannin wasu gungun ‘yan bindiga sun amince da dakatar da hare-hare da sace-sace daga Lahadi, 12 ga Oktoba, a yankunan da abin ya shafa.

Hakazalika, 'yan ta'addar sun yi alkawarin sako wasu daga cikin mutanen da suka yi garkuwa da su, don tabbatar da mutunta yarjejeniyar da aka kulla.

Katsina: Shirin dawo da noma da kasuwanci

Wannan sabon shiri na cikin tsarin gwamnatin jiha na dawo da zaman lafiya da farfaɗo da harkokin noma da kasuwanci da rashin tsaro ya daɗe yana lalatawa.

Taron ya samu halartar sarakuna, dattawa, da jami’an tsaro, inda suka bukaci kowa da kowa ya mutunta yarjejeniyar don dorewar zaman lafiya.

Shugaban karamar hukumar Bakori, Hon. Abubakar Barde, ya jaddada muhimmancin tattaunawa da fahimtar juna wajen samun dawwamammen zaman lafiya.

Kara karanta wannan

Ana batun zargin kisan Kiristoci, yan bindiga sun yi ta'asa a masallacin Katsina

Zagazola Makama, mai sharhi kan harkokin tsaro a Arewa maso Gabas da kuma yankin Tafkin Chadi ne ya rahoto a shafinsa na X cewa Barde ne ya jagoranci zaman sulhun a Bakori.

A taron, Barde ya ba wakilan Fulani tabbacin cewa gwamnati za ta ci gaba da tallafa wa duk wani yunkuri da ke kawo kwanciyar hankali da haɗin kai.

Ana shakku kan yarjejeniyar sulhu da 'yan bindiga a Katsina bayan sun ci gaba da kai hare-hare
Hoton wasu daga cikin 'yan bindiga da suka halarci taron sulhu da kananan hukumomin Katsina. Hoto: @ZagazOlaMakama
Source: Twitter

Shakku kan sahihancin sulhu da 'yan bindiga

Sai dai wasu mazauna yankin sun nuna shakku kan wannan yarjejeniya, inda suke cewa makamancinta da aka yi a baya bai haifar da d'a mai ido ba.

Sun tuna cewa bayan yarjejeniyar da aka kulla a wasu yankuna a watan da ya gabata, 'yan bindiga sun ci gaba da kai hare-hare, lamarin da ke nuna rashin gaskiya daga bangarensu.

A cewar majiyoyi, yawancin ‘yan bindigan sun ƙi ajiye makamai duk da alkawuran da suka yi a lokutan tattaunawa.

Rahoto ya kuma nuna cewa wasu kananan hukumomi kamar Batsari, Kankara, Kurfi, Musawa, Danmusa, Jibia, Faskari, Sabuwa, da Dandume ma sun shiga irin wannan yarjejeniya da ‘yan bindiga.

Manoman Katsina sun koma gona bayan sulhu

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun samu nasara kan mutanen da ake zargi da kisan 'yar jarida a Abuja

A wani labarin, mun ruwaito cewa, zaman lafiya ya fara dawowa a wasu yankuna Katsina bayan sulhun da al’umma suka yi da ’yan bindiga.

Manoma sun koma gonaki cikin kwanciyar hankali, inda wasu suka ce shekaru da dama ba su yi noma ba amma yanzu rayuwa ta sauya bayan wannan sulhu.

Duk da wannan ci gaba, akwai yankuna da 'yan bindiga suka ci gaba da kai hare-hare, inda aka yi garkuwa da mutane a Kankara, Sheme da Kakumi.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com