Abin da Tinubu Ya Fada wa Yaronsa, Seyi da Ya Cika Shekaru 40 a Duniya

Abin da Tinubu Ya Fada wa Yaronsa, Seyi da Ya Cika Shekaru 40 a Duniya

  • Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu ya rubuta sako mai ratsa zuciya ga ɗansa, Seyi Tinubu a bikin cikarsa shekaru 40 da haihuwa
  • Shugaba Tinubu ya yi godiya ga Allah SWT, yayin da ya kuma lissafa wasu daga cikin halayyar Seyi na son jagoranci da ci gaban mutane
  • Sannan ya kara da yi wa 'dansa addu'a, yana mai bayyana yadda ya ke alfahari da matakan da ya ke dauka wajen gina rayuwar jama'a

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT, AbujaShugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu ya bayyana farin ciki yayin da 'dansa, Seyi Tinubu ya cika shekaru 40 da haihuwa.

Shugaban Kasan ya bayyana cewa tun yana yaro, Seyi Tinubu ya nuna jajircewa da hazaka, musamman ta fuskar jagoranci da shugabantar jama'a.

Kara karanta wannan

Atiku ya fusata, ya fadi yadda afuwar Tinubu ta zama barazana ga Najeriya

'Dan Tinubu ya cika shekaru 40
Hoton Bola Tinubu da 'dansa, Seyi Hoto: @DukeofBourdilon, @officialABAT
Source: Facebook

A sakon da Bola Ahmed Tinubu ya wallafa a shafinsa na X, ya bayyana cewa yana matukar alfahari da yadda 'dansa ya girma, da matakin da ya kai a rayuwa.

Bola Tinubu ya yabi 'dansa, Seyi

Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu ya gode wa Allah SWT da ya bar rai, har 'dansa, Seyi Tinubu ya kai shekaru 40 da haihuwa.

A cikin sakon taya murna da ya wallafa, Tinubu ya ce:

"A lokacin da ka cika shekaru 40, na gode wa Allah Madaukakin Sarki bisa yadda ka yi rayuwarka da irin mutumin da ka zama."
"Ka maida hankali wajen gina jama'a, da kokarin cicciba na kasa domin su kai ga ci."
"Daga ƙuruciya ka nuna ƙwazo da shugabanci. Na sha ganin yadda ka juya tunani zuwa kamfanoni, ƙalubale zuwa damammaki."

Tinubu ya yabi halayen Seyi

Shugaba Tinubu ya yabi yadda 'dansa, Seyi ya nuna jajircewa wajen samun ci gaban kasuwanci da hidima.

Kara karanta wannan

Karon farko, yaron Tinubu ya saɓa masa, ya bukaci janye afuwa ga Maryam Sanda

Tinubu ya yi wa Seyi addu'a
Hoton 'dan Shugaban Kasa, Seyi Tinubu Hoto: Aso Villa
Source: Twitter

Ya bayyana cewa:

"A harkar kasuwanci da hidima, ka nuna cewa ba a kiyasta nasara da arziki kawai, sai dai da tasirin da mu ke yi da rayukan da mu ke kawo wa sauyi.
Dukkannin iyalinmu muna alfahari da kai. Barka da zagayowar ranar haihuwarka ta shekaru 40, ɗana. Ka sa mu alfahari, kuma na san za ka ci gaba da sa Najeriya alfahari.

Shugaban Kasan ya kuma yi wa Seyi addu'ar samun lafiya mai inganci da nasara a dukkanin abin da ya sanya a gaba a rayuwarsa.

Afuwar Shugaba Tinubu ta fusata Atiku

A wani labarin, mun wallafa cewa tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar ya caccaki matakin Tinubu na yin afuwa ga masu laifi, inda ya ce hakan barazana ce ga adalci.

Atiku ya yi gargadi cewa ikon bada afuwa na da muhimmanci, amma ya ce amfani da wannan ikon bai dace ba idan aka yi amfani da shi wajen sauƙaƙa hukuncin masu manyan laifuffuka.

Kara karanta wannan

Mansur Sokoto ya yi gugar zana da Tinubu ya yafe wa masu kisan kai da safarar kwaya

An sanar cewa a makon da ya gabata, Shugaba Tinubu ya yi afuwa ga mutane masu yawa — kimanin 175 — ciki har da waɗanda kotu ta tabbatar da laifuffukansu.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng