Atiku Ya Fusata, Ya Fadi yadda Afuwar Tinubu Ta Zama Barazana ga Najeriya
- Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar ya bayyana fargaba a kan yadda Shugaba Bola Tinubu ya yafe wa wasu mutane
- A makon da ya gabata ne, Bola Tinubu ya dauki matakin yi wa wasu mutane 175 afuwa, daga cikin akwai manyan dilolin kwaya
- Sauran da Shugaban Kasan ya yi wa afuwa sun hada da wadanda kotu ta tabbatar masu da laifin kisan kai da cin hanci da rashawa
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT, Abuja – Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya soki matakin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na bada afuwa ga wasu mutane da aka yanke wa hukunci.
Atiku, wanda ya yi wa PDP takarar Shugaban Kasan ya bayyana cewa wannan mataki da Bola Tinubu ya dauka daidai ya ke da tauye adalci da nuna iko ta hanyar da ba ta dace ba.

Source: Facebook
A cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Facebook a ranar Lahadi, Atiku ya ce sanarwar afuwar ta tayar da kura da fushi a fadin ƙasar, kamar yadda ake tsammani.
Atiku ya soki afuwar Tinubu
A sakon, wanda Atiku ya kuma wallafa a shafinsa na X, ya bayyana cewa ikon bada afuwar shugaban ƙasa na da muhimmiyar manufa ta sassauta hukunci da jin kai.
Ya kara da cewa amma abin da gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta yi da wannan iko, ya yi hannun riga da adalci kuma ya saba ga manufar baiwa Shugaban wannan iko.
Atiku ya ce bai dace a yi afuwa ga mutanen da aka same su da manyan laifuffuka irin su safarar miyagun ƙwayoyi, garkuwa da mutane, kisan kai da cin hanci ba.

Source: Facebook
Tsohon Mataimakin Shugaban Kasan ya nanata cewa matakin ya rage darajar adalci kuma ya ba duniya sako mai muni game da abin da gwamnatin Najeriya ta tsaya a kai.
Ya ce musamman a lokacin da ƙasar ke fama da matsalar tsaro, lalacewar ɗabi’a da kuma ƙaruwa wajen safarar miyagun ƙwayoyi.
Atiku: Tinubu bai cancanci yin afuwa ba
Atiku ya bayyana damuwarsa kan yadda aka samu 29.2% na wadanda aka yafe wa da laifin safarar miyagun ƙwayoyi.
Ya ce wannan abin tashin hankali duba da cewa ana daidai gabar da matasan kasar ke kara lalacewa kuma kasar ke kokarin kawar da ta'ammali da miyagun kwayoyi.
Atiku Abubakar ya ce:
“Abin takaici shi ne, wannan afuwa ta fito daga shugaban da ake zargi da mika makudan kudi ga gwamnatin Amurka a kan binciken safarar miyagun ƙwayoyi da ake yi masa.”
Atiku ya bayyana cewa matakin cin mutuncin waɗanda aka zalunta ne, kuma ya raunana kwarin gwiwar jami’an tsaro, ya kuma cutar da ƙasa baki ɗaya.
Tinubu ya yafe wa Maryam Sanda
A baya, mun wallafa cewa Maryam Sanda, wadda aka yanke mata hukuncin kisa a shekara ta 2020 bisa laifin kashe mijinta, Bilyaminu Halliru ta shiga jerin wadanda Tinubu ya yafe wa.

Kara karanta wannan
Mansur Sokoto ya yi gugar zana da Tinubu ya yafe wa masu kisan kai da safarar kwaya
Kotun ta same ta da laifin kisa na gangan bayan ta soka wa mijinta wuka a gida da ke Abuja a watan Nuwamba 2017, lamarin da ya jawo aka yanke mata hukuncin kisa ta hanyar rataya.
Hadimin Shugaban Kasa, Bayo Onanuga, ya bayyana cewa Maryam ta shafe shekaru 6 da watanni takwas a gidan gyaran hali na Suleja, kuma yanzu haka, an yafe mata.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

