Tinubu Zai Sauya 1 daga cikin Ministoci saboda Rashin Lafiya? An Ji Ta Bakin Gwamnati
- Fadar shugaban kasa ta bayyana cewa Wale Edun bai kamu da hawan jini ba, kuma yana samun kulawar likitocin Najeriya a yanzu
- Gwamnati ta kuma karyata jita-jitar da ake yadawa cewa Shugaba Bola Tinubu zai sauya ministan tattalin arzikin saboda rashin lafiyarsa
- Rahoto ya nuna cewa saboda rashin lafiyarsa, Wale Edun ba zai samu damar halartar wani muhimmin taro a birnin Washington D.C ba
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Fadar Shugaban kasa ta yi martani game da jita-jitar da ake yadawa cewa Shugaba Bola Tinubu zai sauya ministan kudi, Wale Edun.
Rahotanni dai sun bayyana cewa, ministan kudi da tsare-tsaren tattalin arzikin kasa, Cif Wale Edun, yana kwance ba shi da lafiya.

Source: Facebook
Ministan kudi na kwance ba shi da lafiya
Amma wani rahoto na jaridar Leadership ya nuna cewa Wale Edun yana samun sauƙi a gidansa dake Abuja bayan da ya yi fama da jinya a 'yan kwanakin nan.

Kara karanta wannan
Da gaske sabon shugaban INEC na cikin lauyoyin Tinubu a zaben 2023? an samu bayanai
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wani babban jami’in gwamnati da ya nemi a sakaya sunansa ya tabbatar da cewa, rashin lafiyar ministan ta ɗan tsananta.
Amma ya jaddada cewa ba gaskiya ba ne jita-jitar da ake yadawa cewa ya kamu da hawan jini ba ko kuma an kai shi ƙasashen waje jinya.
Majiyar ta bayyana cewa:
“Eh, gaskiya ne cewa bai da lafiya, amma ba bugun jini ba ne. A yanzu haka yana cikin gidansa a Abuja. Likitoci na ƙasar nan ke lura da lafiyarsa, kuma ba a kai shi ko’ina ba.
'Babu shirin sauya ministan kudi' - Majiya
Wani ma’aikacin gwamnati ya tabbatar da wannan bayanin, yana mai cewa Edun yana samun kulawa daga likitocin Najeriya, kuma ana ci gaba da sa ido kan lafiyarsa.
"Yanzu haka yana samun kulawa ne daga likitocin Najeriya.
"Suna ci gaba da ba shi kulawa yadda ya kamata. Idan bukatar kai shi asibitin waje ta taso, za a yi hakan. Amma dai a yanzu yana gida.
"Kuma gaskiya babu wani shiri na sauya shi daga mukamin ministan kudi."

Source: Twitter
Fadar shugaban kasa ta sake yin bayani
Haka kuma, mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin yada labarai, Bayo Onanuga, ya tabbatar da cewa Minista Wale Edun yana cikin gida yana murmurewa.
A zantawarsa da jaridar Punch a daren ranar Lahadi, Onanuga ya ce:
“Eh, gaskiya ne yana fama da rashin lafiya, amma yana cikin gida har yanzu, ba a kai shi waje ba.
"Wale Edun ya manyanta, ya kai shekaru 69, kuma yanzu haka yana cikin gida yana samun sauƙi."
Rahotanni sun bayyana cewa, saboda rashin lafiyarsa, Edun ba zai halarci taron shekara-shekara na Bankin Duniya IMF da za a gudanar a Washington D.C. daga ranar Litinin, 14 ga Oktoba, 2025 ba.
Wale Edun ya fadi asarar da Najeriya ke yi
A wani labarin, mun ruwaito cewa, ministan kuɗi, Wale Edun ya ce Najeriya na asarar dala biliyan 15 duk shekara sakamakon karkatar da kudin haraji.

Kara karanta wannan
Sanatan APC ya kafa misali da Trump, ya ce da yiwuwar ya zama shugaban Najeriya a 2039
Wale Edun ya ce hakan na hana gina asibitoci, makarantu, hanyoyi, da rage talauci, inda ya bukaci a dakile fitar da haramtattun kuɗie.
Gwamnatin Bola Tinubu na gyaran haraji don gina tattalin arziki na cikin gida, ba da dogaro da bashi ba, inji Edun a taron IFFs da aka gudanar a Abuja.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
