"Auren Wuri na Kara Haifar da Talauci a Najeriya," Ministar Tinubu Ta Yi Maganganu

"Auren Wuri na Kara Haifar da Talauci a Najeriya," Ministar Tinubu Ta Yi Maganganu

  • Ministan harkokin mata, Imaan Sulaiman-Ibrahim, ta bayyana cewa auren wuri na ci gaba da hana ci gaban Najeriya ta fuskoki da dama
  • A ranar 'yan mata ta Duniya, ministar ta ce auren wuri yana haifar da talauci, mutuwar mata masu juna biyu, da rasa damar ilimi
  • Kungiyoyi kamar Save the Children sun bukaci ƙarin goyon baya ga ‘yan mata don zama shugabanni masu kawo sauyi a cikin al’umma

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Abuja – Ministan harkokin mata, Imaan Sulaiman-Ibrahim, ta bayyana cewa auren wuri na ci gaba da zama babban cikas ga ci gaban Najeriya.

Imaan Sulaiman-Ibrahim ta bayyana cewa 44% na ‘yan mata na yin aure kafin shekara 18, yayin da 18% ke yin aure kafin shekara 15.

Ministar mata, Imaan Sulaiman Ibrahim ta ce auren wuri ya na hana Najeriya samun ci gaba.
Ministar harkokin mata, Imaan Sulaiman Ibrahim tana jawabi a ofishinta da ke Abuja. Hoto: @hm_womenaffairs
Source: Twitter

'Auren wuri na jawo talauci' - Minista

Kara karanta wannan

Tashin hankali: Sojoji sun harbe ɗan sanda har lahira daga musayar yawu a Bauchi

Ta bayyana hakan ne a yayin bikin ranar 'ya'ya mata ta Duniya ta 2025 a Abuja, wanda aka shirya tare da haɗin gwiwar kungiyar SCI da PUGI, inji rahoton Daily Trust.

Ministar ta bayyana cewa auren wuri babban take hakkin yara ne, wanda ke haifar da rashin daidaito, karuwar talauci, da hana ‘yan mata samun damar ilimi da cigaban rayuwa.

"Duk da irin ci gaban da aka samu, alkaluma na nuna abubuwa masu ban takaici. A cewar UNICEF, 44% na 'yan mata na aure kafin shekra 18, 18% na aure kafin shekaru 15."

- Imaan Sulaiman-Ibrahim.

Ta ce auren wuri yana ƙara yawan mace-mace a lokacin haihuwa, yana haifar da talauci, da kuma rage ci gaban ɗan adam, wanda ke dakile cigaban ƙasa gaba ɗaya.

'Ilimi shi ne makamin yaki da talauci' - Minista

Ministar ta kara da cewa:

“Ya zama dole iyaye su kare ‘ya’yansu, al’umma su ƙi al’adun da ke cutarwa, kuma shugabannin addini su zama jagorori na gaskiya."

Imaan Sulaiman-Ibrahim ta bayyana cewa ilimi shi ne makami mafi ƙarfi da zai karya da’irar talauci, inda ta ce “yarinya mai ilimi tana sauya rayuwarta, ta iyalinta, da al’ummarta.”

Kara karanta wannan

ADC ta yi baki 1 da Bankin Duniya a kan karuwar talauci a mulkin Tinubu

Ta kuma shawarci ‘yan mata da su tashi tsaye su kare kansu daga cin zarafi da wariya, domin su ne gajiyayyu masu ƙarfin canza Najeriya ta gobe, inji rahoton The Guardian.

Ministar mata, Imaan Sulaiman Ibrahim ta ce auren wuri ya na hana Najeriya samun ci gaba.
Ministar harkokin mata, Imaan Sulaiman Ibrahim tana jawabi a ofishinta da ke Abuja. Hoto: @hm_womenaffairs
Source: Facebook

An yi kira da a karfafa muradun ‘yan mata

A nasa jawabin, Duncan Harvey, Daraktan Save the Children, ya ce lokaci ya yi da za a rika kallon 'yan mata a matsayin shugabanni, kuma masu fasaha maimakon masu rauni kawai.

Ya bayyana cewa duk da kalubalen talauci da rashin tsaro, ‘yan mata da dama suna tashi suna shirya ayyukan cigaba don kawo karshen auren wuri da karfafa ilimi.

Shi ma Bukky Maiye, Shugaban Pink Up for Girls, ta bukaci da a ci gaba da kokari wajen kare ‘yan mata da basu damar cimma cikakkiyar manufarsu a rayuwa.

Maiye, ta bakin wakilarta Ginika Ukoha, ta ce ƙungiyarsu na samar da wuri mai aminci ga mata da ‘yan mata domin su bunƙasa, su kuma zama jagorori a nan gaba.

Auren wuri na halaka 'ya'ya mata 60 kullum

A wani labarin, mun ruwaito cewa, kungiyar Save The Children International ta ce auren wuri yana halaka fiye da yara mata 60 a ko wacce rana.

Kara karanta wannan

Kano: 'Dan jarida ya debo ruwan dafa kansa, ICPC ta kama shi kan zambar N14m

Bisa kiyasi, ana aurar da 44% na yara mata a Najeriya kafin su cika shekaru 18, wanda Najeriya tana daya daga cikin kasashen da su ka fi yin auren wuri.

Kungiyar Save the Children ta bayyana bukatar rage yawan auren wuri a Najeriya sakamakon tsaka mai wuya da mata suke rayuwa a ciki a halin yanzu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com