Hafsan Tsaro a Mulkin Buhari Ya Fadi Adadin Sojoji da Aka Kashe a Yakin Boko Haram
- Tsohon hafsan tsaro a Najeriya, Janar Lucky Irabor ya bayyana yawan sojoji da aka hallaka a yaki da Boko Haram a Arewacin Najeriya
- Irabor ya ce aƙalla sojoji 2,700 ne suka mutu cikin shekaru 12 na yaƙin da Najeriya ke yi da yan ta'addan Boko Haram wanda ya jawo asararar rayukan fararen hula
- Tsohon hafsan tsaron ya ƙaryata zargin cewa sojoji daga wani addini ne kawai ake tura wa yanki mai haɗari inda ake rasa rayukansu
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Abuja - Tsohon Hafsan Tsaron Ƙasa, Janar Lucky Irabor (mai ritaya), ya bayyana adadin sojoji da suka mutu a yaki da Boko Haram.
Irabor ya bayyana cewa an rasa rayukan sojoji kusan 2,700 cikin shekaru 12 na yaƙin Boko Haram musamman a yankunan Borno, Yobe da jihar Adamawa.

Source: Facebook
Boko Haram: Irabor ya fadi adadin asarar rayuka
Ya bayyana haka ne cikin sabon littafinsa mai suna “SCARS: Nigeria’s Journey and the Boko Haram Conundrum” wanda Leadership ta bibiya.
Janar Irabor ya ƙaryata zargin cewa sojoji daga wani addini ko ƙabila ne suka fi mutuwa a yaƙin, yana mai cewa asarar ta shafi kowa.
Ya kuma ambaci rahoton UNDP da ya nuna cewa rikicin Boko Haram ya yi sanadin mutuwar mutum kusan 350,000 zuwa shekarar 2020.
A cewarsa:
“Ziyartar makabartar sojoji na nuna cewa Musulmai da Kiristoci sun yi asara iri ɗaya, ba kamar yadda ake yaɗa jita-jita ba.”
Janar ɗin ya bayyana cewa yaƙin Boko Haram ya bar tabo ga Najeriya, yana kira ga ƙasar ta koya darasi da ƙarfafa haɗin kai.

Source: Original
Zargin da Irabor ya yi kan wasu kungiyoyi
Irabor ya zargi rahotannin wasu ƙungiyoyi da suka rage ƙarfin gwiwar sojoji tare da ɓata suna a idon Amurka har aka yi wa wasu takunkumi.
Ya tuna cewa Amnesty International ta taɓa zargin sojojin Najeriya da kisan fararen hula, duk da rahoton gwamnati ya tabbatar babu gaskiya a ciki, cewar Punch.
Irabor ya bayyana cewa Janar Ngubane da Janar Bamigboye sun fuskanci wahala bayan ƙin basu 'visa' daga Amurka saboda waɗannan rahotanni.
Ya ce matsalolin tsaro a Arewacin ƙasa sun samo asali ne daga jahilci, talauci, da rikice-rikicen neman albarkatun ƙasa tsakanin manoma da makiyaya.
Haka kuma ya danganta matsalolin IPOB, Oduduwa, da rashin adalcin tattalin arziki a yankin Neja Delta da sakamakon gazawar tsaro a Najeriya.
Janar Irabor ya tuna wahalar da ya sha
Mun ba ku labarin cewa tsohon Hafsan tsaron Najeriya, Lucky Irabor ya yi magana kan kalubale da ya fuskanta a lokacin jagorancinsa a mulkin Muhammadu Buhari.
Irabor ya bayyana cewa harin jirgin kasa da aka kai na Abuja zuwa Kaduna a 2022 shi ne abu mafi wahala wanda ya rikita shi a lokacin jagorancinsa.
Tsohon hafsan tsaron ya ce ya rubuta littafi mai suna 'Scars. 'bayan ritaya, inda ya tattauna batun wahalhalun da ke cikin yaki da Boko Haram da tsaro.
Asali: Legit.ng

