An Saki Sunayen 'Yan Najeriya 2 da Aka Kama Dauke da $6.1m a Filin Jirgin Sama
- Hukumar tsaro ta FAAN ta cafke mutane biyu da ke dauke da dala miliyan $6.1 a filin jirgin sama na Murtala Muhammed, Legas
- An bayyana sunayen mutanen da aka kama, waɗanda suka fito daga Dubai suna kokarin tafiya Abuja, sannan su wuce Addis Ababa
- Bayan kama su, jami’an FAAN sun mika su ga DSS, daga nan kuma aka mika su ga hukumar EFCC domin ci gaba da bincike
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Legas – Hukumar kula da filayen jiragen sama ta Najeriya (FAAN) ta tabbatar da kama mutane biyu dauke da dala miliyan $6.1 a filin jirgin sama
FAAN ta sanar da cewa ta kama mutanen biyu dauke da makudan kudi a filin jirgin Murtala Muhammed Terminal 2 (MMA2), da ke Legas.

Source: Twitter
An cafke mutane 2 dauke da $6.1m
Jami’an tsaron AVSEC da ke karkashin FAAN ne suka kama mutanen yayin da suke shirin hawa jirgin Aero Contractors da ke hanyar zuwa Abuja, inji rahoton Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cewar majiya daga filin jirgin, an bayyana sunayen mutanen da aka kama da Mahmud Nasidi da kuma Yahaya Nasidi.
An same su ne dauke da akwatuna masu cike da dalolin Amurka da ba su gabatar da su ga hukumar Kwastam ba, kamar yadda doka ta tanada.
Rahotanni sun nuna cewa mutanen sun riga sun wuce wuraren tsaro na filin jirgin kafin jami’an tsaro su kama su a wurin tarmac.
An mika mutanen da aka kama ga EFCC
Bayan kama su, FAAN AVSEC ta mika su ga hannun hukumar DSS, wacce ta mika su ga hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC domin gudanar da cikakken bincike.
Mai magana da yawun EFCC, Dele Oyewale, ya tabbatar da cewa mutanen biyu suna hannun hukumar.
Dele Oyewale ya ce:
“Zan iya tabbatar muku cewa mutanen biyu da aka kama da kudin an mika su gare mu domin gudanar da bincike.”

Kara karanta wannan
Babbar magana: An kama fasinjojin jirgin sama da tsabar kudi kusan Naira biliyan 10

Source: Facebook
Yadda aka kama mutanen 2 a filin jirgi
Shugaban kamfanin Aero Contractors, Ado Sanusi, ya ce ma’aikatan tsaron su ne suka lura da mutanen da ke dauke da jakunkuna masu nauyi da ba su son a duba su, inji rahoton The Nation.
Sanusi ya ce:
“Sun ce jakunkunan na dauke da kudi, amma ba su bayyana su ba ga hukumar kwastam kamar yadda doka ta tanada.”
Ya ce mutanen sun yi ikirarin cewa su jami’an tsaro ne da ke rakiyar wani wanda ake zargi amma ba su sanar da kamfanin jirgin ba, wanda hakan ya saba da ka’idar tafiyar da irin wannan lamari.
Saboda haka, kamfanin ya hana su shiga jirgi, sannan daga bisani aka kama su tare da mika su ga hukumomin tsaro.
Mai shara ya tsinci $10,000 a jirgin sama
A wani labarin, mun ruwaito cewa, har yanzu akwai sauran masu tsoron Allah, inda wani mai shara ya mayar da $10,000 da ya tsinta lokacin da ya ke aikinsa.
Mai aikin sharar, Auwal Ahmed Dankode ya tsinci dalolin Amurka da kudinsu ya kai Naira Miliyan 16 a kudin Nairar Najeriya a cikin jirgi.
An rahoto cewa Auwalu, wanda dan asalin karamar hukumar Bunkure ne a jihar Kano ya mayar da kudin da ya tsinta a jirgin Egypt Air ga hukumomi.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng

