Bayan Yin Afuwa ga Su Maryam Sanda, Tinubu Ya Bar Najeriya, Ya Shilla Kasar Waje

Bayan Yin Afuwa ga Su Maryam Sanda, Tinubu Ya Bar Najeriya, Ya Shilla Kasar Waje

  • Shugaba Bola Tinubu zai bar Abuja ranar Lahadi, 12 ga Oktoba, domin halartar taron kolin shugabannin ƙasashe a birnin Rome, Italiya
  • Taron zai mayar da hankali kan matsalar tsaro a Afirka, musamman yaduwar ta’addanci da haɗin gwiwar ɓarayi da masu tayar da hankali
  • Tinubu zai gana da shugabanni da dama don tattauna dabarun haɗin kai wajen magance barazanar tsaro da ta shafi yankunan Sahel

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja – Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bar Abuja a ranar Lahadi, 12 ga Oktoba, domin halartar taron shugabannin ƙasashe na Aqaba Process da za a gudanar a birnin Rome, Italiya.

Taron zai fara ne a ranar Litinin, 14 ga Oktoba, kuma zai haɗa shugabanni da jami’an tsaro daga ƙasashen Afirka da wakilan ƙungiyoyin gwamnati da masu zaman kansu.

Kara karanta wannan

Sardaunan Zazzau: Tinubu ya taya Namadi Sambo murnar samun sarauta

Shugaba Bola Tinubu ya bar Abuja zuwa Italiya don halartar taron Aqaba
Shugaba Bola Tinubu ya na daga hannu yayin da zai shiga jirgin sama. Hoto: @aonanuga1956
Source: Twitter

Tinubu zai halarci taro a kasar Italiya

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasa, Bayo Onanuga ya fitar a shafinsa na X a ranar Lahadi.

A cikin sanarwar, fadar shugaban kasa ta an shirya taron ne domin tattauna matsalolin tsaro da ke ta ƙaruwa a yankin yammacin Afirka.

Taron Aqaba Process wani shiri ne da Sarkin Jordan, Abdullah II, ya ƙaddamar a 2015 tare da haɗin gwiwar gwamnatin Italiya.

Manufar taron Aqaba a Italiya

Manufarsa ita ce ƙarfafa haɗin kai tsakanin ƙasashe wajen magance barazanar ta’addanci, laifuffukan haɗin gwiwa da kuma satar jiragen ruwa a tekun Gulf of Guinea.

Za a tattauna hanyoyin da za su taimaka wajen yaƙi da tayar da hankali ta yanar gizo, da kuma dakile yada ra’ayoyin masu ta da kayar baya.

Sanarwar fadar shugaban kasar ta kara da cewa taron yana mayar da hankali sosai kan hanyoyin da za a tabbatar tsaro a cikin ƙasashe da iyakokinsu.

Kara karanta wannan

An gano tsofaffin shugabannin Najeriya 3 da ba su halarci taron majalisar koli ba

An ce Tinubu zai yi magana da shugabannin duniya a taron da zai je Italiya.
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya na jawabi a wani taro. Hoto: @aonanuga1956
Source: Twitter

Tinubu zai yi jawabi a taron Aqba Process

Baya ga halartar zaman babban taron, Shugaba Tinubu zai yi ganawa ta musamman da wasu shugabanni don tattauna matakan haɗin kai wajen magance matsalar tsaro a yankin Sahel.

Zai samu rakiya daga Ministan Harkokin Wajen ƙasa da ƙasa, Ambasada Bianca Odumegwu–Ojukwu, Ministan Tsaro, Mohammed Badaru Abubakar.

Sauran wadanda za su raka Tinubu sun hada da Mai Ba da Shawara kan Tsaro, Nuhu Ribadu, da Daraktan Hukumar Leken Asiri (NIA), Ambasada Mohammed Mohammed.

A 'yan watannin nan, shugaban kasa Tinubu ya yi tafiye-tafiye zuwa kasashe daban daban, inda aka fara ganin amfanin wasu daga cikin tafiye-tafiyen.

Tinubu ya halarci taron TICAD a Japan

A wani labarin, mun ruwaito cewa, Shugaba Bola Tinubu ya tashi daga Abuja ranar Alhamis 14 ga watan Agustan 2025 domin halartar wasu taruka a ƙasashe duniya.

Hadiminsa a ɓangaren yada labarai ya tabbatar da cewa shugaban zai tafi Japan da Brazil, inda zai halarci taro da ganawa da shugabanni.

Kara karanta wannan

Tsadar aure: Sarki ya gaji da korafin matasa, ya sanya doka kan lamarin bukukuwa

Sanarwar ta ce Shugaba Tinubu zai kuma tsaya a birnin Dubai, Hadaddiyar Daular Larabawa kafin ci gaba da tafiya zuwa kasar Japan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com