Maryam Sanda Ta Shiga Jerin Wadanda Aka Yafewa, Tinubu Ya Fadi dalilin Yafe Mata
- Shugaba Bola Tinubu ya yi wa mutane 175 afuwa, ciki har da tsofaffi, matattu da wasu da suka aikata manyan laifuffuka
- Daga cikin wadanda suka amfana da afuwar har da Maryam Sanda, wacce aka yankewa hukuncin kisa bisa tuhumar kisan mijinta
- Sanarwar ta kuma nuna wasu daga cikin wadanda aka yafewa suna fuskantar hukuncin safarar kwayoyi da hakar ma’adinai ba ka’ida
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Shugaba Bola Tinubu ya sanar da yiwa mutane 175 afuwa a makon da ya gabata a wani taro da aka yi a birnin Abuja.
Shugaban ya bayyana dalilin yin afuwar ga zaɓaɓɓun mutane da suka hada da wasu dattawa da kuma wasu da suka ba kasa gudunmawa.

Source: Facebook
Hakan na cikin wata sanarwa da hadiminsa a bangaren sadarwa, Dada Olusegun ya tabbatar a shafin X a yau Asabar 11 Oktoba, 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanarwar ta jero mutanen da aka yi wa afuwa da kuma laifuffukan da suka aikata da aka yanke musu hukunci.
Tinubu ya yi afuwa ga Maryam Sanda
Daga cikinsu akwai Maryam Sanda wacce aka tura ta gidan gyaran hali bayan tuhumarta da kisan mijinta, Bilyaminu Bello.
Akalla shekaru uku aka shafe ana shari'ar bayan ta hallaka shi kan zargin yana cin amanarta da wata budurwa.
A shekarar 2020 ne aka yanke wa Maryam wannan hukunci wanda mutane da dama a Najeriya suka yi farin ciki da haka.
Al'umma sun yi ta tsinewa Maryam Sanda a wancan lokaci duba da irin cin amanar mijinta da ta yi da kuma yadda ta yi ajalinsa.

Source: Facebook
Dalilin Tinubu na yafewa Maryam Sanda
Sai dai kwatsam sai sanarwa da fito daga fadar shugaban kasa, inda aka gano sunan Maryam Sanda a ciki.
A cewar sanarwar, an yanke wannan shawara ne bayan roƙon da iyalanta suka yi, inda suka ce sakin ta zai fi alheri ga ’ya’yanta biyu.
Ta ƙara da cewa, an yi afuwar ne saboda kyawawan halayenta a gidan gyaran hali da kuma “nadama da rungumar sabuwar rayuwa” da ta nuna.
Sanarwar ta ce:
An yankewa Maryam Sanda, mai shekaru 37 hukuncin kisa a shekarar 2020 saboda laifin kisan mijinta, kuma ta shafe shekaru shida da watanni takwas a gidan gyaran hali na Suleja."
Daga cikin sauran wadanda aka yi wa afuwa akwai wanda aka tuhuma da safarar kwayoyi.
Sai kuma mafi yawa daga cikinsu ana tuhumar su tare da daure su a gidan kaso kan hakar ma'adinai ba bisa ka'ida ba.
Afuwa: Farouk Lawan ya godewa Tinubu
Mun ba ku labarin cewa tsohon dan majalisar tarayya a jihar Kano. Hon. Farouk Lawan ya yi martani bayan shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya yi masa afuwa.
Tsohon dan majalisar da ya wakilci Shanono/Bagwai a Kano ya gode wa shugaban ƙasa Bola Tinubu bisa yafiyar da ya samu bayan tuhume-tuhume
Ya bayyana Tinubu a matsayin uba mai tausayi da jajircewa, wanda ya nuna rahama da adalci a cikin shugabancinsa, ya ce ya samu kwarin guiwa.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

