Tashin Hankali: Sojoji Sun Harbe Ɗan Sanda har Lahira daga Musayar Yawu a Bauchi

Tashin Hankali: Sojoji Sun Harbe Ɗan Sanda har Lahira daga Musayar Yawu a Bauchi

  • Rashin jituwa tsakanin jami’an soja da ‘yan sanda a Bauchi ya jawo an harbe wani dan sanda, Ukasha Muhammed har lahira
  • Rundunar ‘yan sanda ta tabbatar da kama sojoji uku da ake zargi, yayin da kwamishina ya umarci gudanar da cikakken bincike
  • Rashida Muhammed ta bayyana cewa rikicin ya faru ne bayan dan sandan ya tsaya binciken ababen hawa a Bayan Gari, Bauchi

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Bauchi – Rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi ta tabbatar da mutuwar wani dan sanda, Ukasha Muhammed, mai lambar aiki F/No 533164.

An ruwaito cewa, dan sandan ya rasa ransa ne bayan sojoji sun harbe shi har lahira lokacin da wani sabani ya barke a tsakaninsu a Bauchi.

Wasu sojoji sun harbe dan sanda har lahira a Bauchi.
Hoton 'yan sandan Najeriya a bakin aiki. Hoto: Abdullahi Haruna Kiyawa
Source: Facebook

Bauchi: Yadda sojoji suka kashe dan sanda

Wata ‘yar uwar mamacin, Rashida Muhammed, ta shaida wa Daily Trust cewa lamarin ya faru ne da misalin karfe 9:00 na daren ranar Juma'a a yankin Tudun Wadan Dan Iya (Bayan Gari) da ke cikin garin Bauchi.

Kara karanta wannan

Babban 'dan sanda ya yi wani irin mutuwa mai rikitarwa a cikin bandaki

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewarta, tawagar ‘yan sanda masu sintiri ta tsaya a wajen domin bincikar motocin da ke wucewa da kuma masu babura, lokacin da wani mutum ya ki bayar da hadin kai, lamarin da ya haifar da tashin hankali.

Malama Rashida ta bayyana cewa:

“Bayan awa guda, mutumin ya dawo tare da wasu abokansa sojoji biyu. Kafin mutane su ankara, daya daga cikinsu ya bude wa Ukasha wuta a kirji.”

Bayan haka, jama’ar yankin suka yi kokarin cafke sojojin da suka yi harbin kafin jami’an ‘yan sanda su isa wajen domin kame su.

Rundunar ‘yan sanda ta yi martani

Mai magana da yawun ‘yan sandan Bauchi, CSP Mohammed Ahmed Wakil, ya tabbatar da faruwar lamarin cikin wata sanarwa da aka wallafa a shafin rundunar na Facebook ranar Asabar.

Sanarwar ta ce:

“Da misalin karfe 10:35 na dare, rundunar ta samu rahoton wani mummunan lamari da ya shafi tawagar sintiri karkashin jagorancin Sufeta Hussaini Samaila a yankin Bayan Gari."

Kara karanta wannan

Sabon rikici ya barke a jihar Benue, an yi asarar rayuka kafin zuwan sojoji

Wakil ya bayyana cewa bayan musayar yawu, sojoji uku daga rundunar Operation Safe Haven suka isa wurin a cikin kakin soja, suna dauke da bindigogi.

“Sojojin sun bude wuta kan Ukasha Muhammed, inda harsashi ya same shi a gefen kirji, wanda hakan ya jawo mutuwarsa.”

- CSP Mohammed Ahmed Wakil.

An cafke sojoji 3 da ake zargi da kashe wani dan sandan Najeriya a Bauchi
Taswirar jihar Bauchi da ke a Arewa maso Gabashin Najeriya. Hoto: Legit.ng
Source: Original

Sojojin da ake zargi da kashe dan sandan

Ya kara da cewa mamacin an garzaya da shi asibitin koyarwa na jami’ar Abubakar Tafawa Balewa (ATBUTH), inda likitoci suka tabbatar da mutuwarsa.

Wakil ya bayyana sunayen wadanda ake zargi da hannu a kisan su ne:

  1. Private Usman Mubarak (23NA/84/5346);
  2. Private Yakubu Yahuza (23NA/85/10185);
  3. Private Godspower Gabriel (23NA/84/5654).

Sanarwar rundunar 'yan sandan ta ce dukkanin sojojin uku suna aiki ne karkashin rundunar Operation Safe Haven dake Jos, jihar Filato.

Dan sanda ya harbe soja har lahira a Najeriya

A wani labarin, mun ruwaito cewa, wani dan sandan MOPOL ya saita bindiga, ya harbe wani sojan Najeriya har lahira a jihar Bauchi.

An ce takaddama ta barke a lokacin da sojoji suka nemi duba wata motar kamfanin 'yan China da ke hakar ma'adanai a garin Futuk.

Kara karanta wannan

Ana batun zargin kisan Kiristoci, yan bindiga sun yi ta'asa a masallacin Katsina

Rundunar sojojin Najeriya da rundunar 'yan sanda ta yi bayani game da matakin da aka dauka kan jami'in da ya yi harbin yayin da ake bincike.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com