‘Mu Ma Masoyanka ne’: Malamin Ahlus Sunnah Ya Shawarci Abba game da Mukarrabansa

‘Mu Ma Masoyanka ne’: Malamin Ahlus Sunnah Ya Shawarci Abba game da Mukarrabansa

  • Wani malami ya roki Gwamna Abba Kabir da ya ja kunnen mukarrabansa da ke yin kalaman da ka iya haifar da rarrabuwar kawuna
  • Malamin ya ce Ahlus Sunnah ma suna goyon bayan gwamnan, don haka bai dace wasu su rika zaginsu ko iyayensu a bainar jama’a ba
  • Sheikh Ibrahim Aliyu Kaduna ya ce Abba Kabir Yusuf gwamna ne na kowa, daga Izalah, darika, har ma da Kiristoci ba Musulmai kadai ba

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Kaduna - Malamin Musulunci a jihar Kaduna ya tsoma baki kan lamarin da ke faruwa a Kano bayan zargin Malam Lawan Abubakar Shu'aib Triumph.

Bayan zargin malamin, maganganu suna ta fitowa game da lamarin wanda ke neman farraka jihar musamman a bangaren siyasa.

Malami ya shawarci Abba Kabir kan zagin Ahlus Sunnah
Gwamna Abba Kabir Yusuf da Malam Ibrahim Aliyu Kaduna. Hoto: Abba Kabir Yusuf, Malam Ibrahim Aliyu Kaduna.
Source: Facebook

Malamin ya shawarci Gwamna Abba Kabir

Sheikh Ibrahim Aliyu Kaduna ya shawarci Gwamna Abba Kabir Yusuf a bidiyo da shafin Karatun Sunnah ya wallafa a Facebook.

Kara karanta wannan

An fara guna guni da Majalisar Benue ta amince gwamna ya karbo bashin Naira biliyan 100

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Malamin ya yi kira na musamman ga gwamna Abba Kabir da ya ja kunnen makarrabansa da suke wasu irin maganganu kan zabe.

Shehi ya ce abin takaici ne yadda suke maganganu cewa ko babu yan Izalah, za su ci zabe, ya ce su ma Ahlus Sunnah masoyan gwamna ne.

Malamin ya ce:

"Ina son zan yi kira na musamman ga mai girma gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, mutane suna ganin mutuncin gwamnan Kano.
"Suna ganin darajar shi da kuma ganin alfanunsa, amma gwamna ya yi kokari ya duba mukarrabansa ko wadanda suke biye da shi.
"Akwai wadanda suke fitowa suna aibata Ahlus Sunnah a cikin tafiyar yan Kwankwasiyya, mu kuma mu Ahlus Sunnah muna son gwamna kuma muna mara masa baya."
An ba Abba Kabir shawari domin jan kunnen mukarrabansa
Gwamna Abba Kabir yayin wani taro a gidan gwamnatin Kano. Hoto: Abba Kabir Yusuf.
Source: Facebook

Sheikh Ibrahim ya bukaci Abba ya kwabi masoyansa

Sheikh Ibrahim Aliyu ya ce ba su jin dadi ana zaginsu da iyayensu yayin da ya ce akwai manyan malamansu a cikin tafiyar yan Kwankwasiyya.

Kara karanta wannan

Shehi ya nemi zama da Kiristoci kan zuwan Isra'ila Najeriya da barazanar yaki

Ya ce gwamna na kowa ne kuma mutane da dama ne suka zabe shi daga cikin yan darika da Izalah har ma da sauran kungiyoyi.

"Idan muka ji ana zaginu, ana zagin iyayenmu ai baya muka yi, a cikin tafiyar Kwankwasiyya akwai manyan malamanmu, malamai ne na Ahlus Sunnah amma da su ake tafiyar.
"Ba kadai yan Izalah suka zabi Abba Kabir Yusuf ba, haka ba kadai yan darika suka zabe shi ba, ba kuma yan wata kungiya suka zabe shi ba, gwamna ya sani shi na kowa ne."

- Sheikh Ibrahim Aliyu Kaduna

Malamin ya ce wannan kira ne ga Gwamna saboda sun yi kokarin samunsa ta wasu hanyoyi abin ya ci tura, shi ne suka zo ta nan saboda sakon yana saurin zuwa.

Sheikh Ibrahim ya ce su Ahlus Sunnah suna kaunarsa, suna sonsa kuma suna mara masa baya kan alherin da yake yi saboda shi mai adalci ne.

Legit Hausa ta tattauna da Ahlus Sunnah

Ustaz Muhammad Umar ya yi tsokaci inda ya ce ba iya Kano ba akwai yan wasu jihohi ma da ke goyon bayan salon mulkin Kwanwkasiyya.

Kara karanta wannan

'Da Allah na dogara': Abba kan barazanar da ake yi masa game da zaben 2027

Ya ce:

"Ko a nan Gombe, na san akwai yan Kwankwasiyya da kuma sauran jihohi saboda yanain salon mulkinsu."

Dalibin ilimin ya ba da shawara da a kai zuciya nesa wurin bambance akida a sha'anin siyasa tare da bukatar masoyan Abba su bar sukar yan Izalah.

2027: Shehi ya fadi shirin Ahlus Sunnah a Kano

Kun ji cewa maganar zargin da ake yi wa Sheikh Abubakar Lawan Triumph a Kano ta dauki sabon salo na siyasa a Kano.

Sheikh Ishaq Adam Ishaq ya bayyana cewa suna da shiri na musamman kan zaben 2027 domin su tabbatar da wanda zai kare addini.

Ya shawarci Ahlus Sunnah da su yanki katin zabe domin tabbatar da muradinsu, yana mai cewa su ne suka fi yawa a Kano da masallatai.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.