Majalisar Kolin Musulunci Ta Karyata batun Kisan Kiristoci, Ta Caccaki CAN, Tinubu
- Majalisar kolin addinin Musulmi a Najeriya (NSCIA) ta bayyana damuwarta kan zargin kisan kiyashi da ake yadawa a duniya
- Rahoto ya nuna cewa majalisar ta ce wannan zargi karya ne mai hatsari da ka iya tayar da rikicin addini tsakanin al’umma
- Majalisar ta yaba wa hukumomi da ‘yan kasa masu kishin da suka fito suka karyata wannan labari tun bayan fitowar shi
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kaduna - Majalisar kolin addinin Musulmi a Najeriya (NSCIA) ta yi kakkausar suka ga zarge-zargen yi wa Kiristoci kisan kiyashi.
Hakan na zuwa ne bayan wani mutum a Amurka ya yi zargin cewa ana yi wa Kiristoci kisan kiyashi a Najeriya.

Source: Facebook
Daily Trust ta ce an samu bayanin ne a wata sanarwa da mataimakin mai ba da shawara a fannin shari’a na ƙasa na NSCIA, Imam Haroun Muhammad Eze, ya sanya wa hannu.
Sanarwar ta nuna cewa NSCIA ta bayyana wannan zargi a matsayin “karya da yaudara, mai cike da hatsari.”
Majalisar ta gargadi cewa irin wannan furuci na iya jefa ƙasar cikin tashin hankali da rikicin addini idan ba a dauki mataki ba.
NSCIA ta karyata zargin kisan kiyashin kiristoci
Majalisar ta yaba wa hukumomin gwamnati, majalisar dokoki, da sauran ‘yan Najeriya masu kishin ƙasa da suka gaggauta karyata wannan zargi.
Amma duk da haka, ta yi tambaya da cewa me yasa gwamnati ba ta fito fili ta bayyana waɗanda ke yada irin labari ba.
A cewar sanarwar, akwai wasu masu alaƙa da kungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN) da ke yada irin waɗannan bayanai saboda wasu dalilai na kashin kansu.
NSCIA ta yi nuni da cewa irin wannan yaudara tana kawo mummunan suna ga ƙasar a kasashen waje, inda wasu ke amfani da ita wajen neman kuɗi da tallafi.
Majalisar NSCIA ta ce ana son raba kawuna
Majalisar ta bayyana cewa wasu ‘yan siyasa da shugabannin addini na amfani da maganar wariyar addini don lalata nagartar gwamnati mai ci.
Ta tuna da wata tattaunawa da aka samu lokacin zaben shugaban ƙasa na 2023, inda wani ɗan takara ya bayyana zaben a matsayin “yaƙin addini.”
NSCIA ta ce wannan tunani na nufin ƙirƙirar rabuwar kai tsakanin ‘yan ƙasa da kuma rage amincewa da gwamnati a idon duniya.
Binciken gaskiya kan hare-hare a Najeriya
Premium Times wallafa cewa majalisar NSCIA ta jaddada cewa babu wata ƙungiya ko wani addini da aka ware ana kaiwa hari a Najeriya.
Ta ce rahoton ma’aikatar harkokin wajen Amurka na 2023 ya nuna cewa ‘yan ta’adda da ‘yan fashi suna kai wa masallatai da coci-coci hari ba tare da bambanci ba.
A cewar wasu bayanai, an kashe mutum 2,266 a Arewacin ƙasar a 2025, inda Musulmai suka fi yawa, kuma sama da mutane miliyan 2 sun rasa matsugunansu.
Kira ga gwamnati kan zaman lafiya
NSCIA ta nuna damuwa da yadda gwamnati ba ta fito fili ta karyata kalaman wasu shugabannin Kiristoci ba, ciki har da Wilfred Anagbe da Rev. Joseph Hayab.
Ta ce su ne wadanda suka nemi Amurka ta sanya Najeriya cikin jerin kasashen da ake nuna wariyar addini.
Sai dai ta yaba da furucin wani jagora a CAN wanda ya ce idan aka bude wuta a kasuwa, harsasai ba sa bambance Musulmi da Kirista.
Majalisar ta kuma koka kan fifikon da take ganin gwamnati ke bai wa Kiristoci wajen nadin mukamai, inda ta ce kashi 62% na wadanda aka nada Kiristoci ne.
NSCIA ta caccaki shugaba Tinubu
Majalisar ta caccaki shugaban kasa Bola Tinubu kan gana wa da shugabannin Kiristoci a jihar Filato ba tare da zama da musulmai ba.

Source: Facebook
Shugaban ya ziyarci jihar Filato ne a makon da ya wuce, inda ya gana da Kiristoci bayan jana'izar mahaifiyar shugaban APC na kasa.
Malami ya nemi a zauna da Kiristoci
A wani rahoton, kun ji cewa wani malamin addinin Musulunci Dr Abdulmudallib Gidado Triumph ya yi magana kan zargin kisan Kiristoci.
Malamin ya ce kowa ya san karya ne ba wani addini da aka ware ana kashewa a Najeriya a hare haren da ake kaiwa.
Dr Abdulmudallib ya bukaci manyan Arewa su zauna da shugabannin Kiristoci domin sanin abin da suke kullawa da Isra'ila.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng



