Shehi Ya Nemi Zama da Kiristoci kan Zuwan Isra'ila Najeriya da Barazanar Yaki
- Sheikh Abdulmudallib Gidado Triumph ya ce ya kamata a zauna da shugabannin Kiristoci na Arewa domin fahimtar dangantakarsu da Isra’ila
- Malamin musuluncin ya bukaci a tattara bayanai na adadin musulmai da aka kashe a rikice-rikice don a san hakikanin abun da ke faruwa
- Shehin ya yi gargaɗi cewa daukar makami zai kawo barna mai girma kuma ya nemi manyan malamai da shugabanni su zauna a tattauna
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kano — Malamin Musulunci, Dr Abdulmudallib Gidado Triumph, ya yi kira ga ‘yan Arewa da su zauna da shugabannin Kiristoci.
Ya nemi a zauna ne domin tattauna batutuwan da suka shafi dangantaka da Isra’ila da kuma matsalolin da ake dangantawa da kisan kare dangi a wasu wurare.

Source: Facebook
Ya bayyana hakan a wani bidiyo ya wallafa a Facebook, inda ya jaddada bukatar fahimtar juna da tuntubar manyan malaman addini.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sheikh Abdulmatallab ya ce ana kashe Musulmai
Malamin ya bayyana cewa rashin cikakken bayani yana kara dagula al’amura game da mutannen da aka fi kashewa a Najeriya,
A kan haka ya ce mataki na farko shi ne a gudanar da bincike mai inganci don gano yawan musulmai da suka rasa rayukansu a rikice-rikicen da aka yi a Najeriya.
Ya ce akwai bukatar tsofaffin sojoji, ‘yan sanda da jami’an DSS su fito su bayyana adadin wadanda suka mutu a rikicin Boko Haram da sauransu domin a san a wane ɓangare ne aka fi kashewa.
A watan Agustan 2025 ne Isra'ila ta zauna da Kiristocin Najeriya kamar yadda wani Fasto da aka yi zaman da shi ya wallafa a X.
Bukatar zama da Kiristocin Arewa
Mataki na biyu, in ji shi, shi ne zama tsakanin manyan malaman Musulunci da shugabannin Kiristoci a Arewa.
Malamin ya ce ya kamata manyan Arewa, tun daga kan mai Alfarma Sarkin Musulmi su zauna da shugabannin Kirstoci domi fahimtar alakarsu da Isra'ila.
Ya ce yin shiru yayin da aka fito da zarge zargen da za su iya tayar da yaki ba abin yarda ba ne, musamman lura da halin da Arewa ke ciki.

Source: Twitter
Gargaɗi kan daukar makami a Arewa
Malamin ya yi gargaɗin cewa daukar makami zai kawo babbar matsala ga ƙasa baki ɗaya, yana ambaton misalai irin su Sudan inda yaki ya lalata makarantu da tattalin arziki.
Ya ce idan an fara fada tsakanin Musulmi da Kiristoci, babu wanda zai samu nasara — za a rasa rayuwa mai ma’ana.
Masanin fikihun ya yi gargadin cewa abinci zai kare, kasuwanni za su tsaya, kuma jama’a za su yi rayuwa cikin tsanani.
Bala Lau ya goyi bayan Triumph
A wani rahoton, kun ji cewa Sheikh Abdullahi Bala Lau ya yi magana kan korafin da aka shigar game da Sheikh Lawan Shuaibu Triumph.
Shugaban Izala ya bayyana cewa maganganun Sheikh Triumph suna kan layi kuma duk mai kalubalantarsa ya fito da hujja.
Bala Lau ya yi martani ga mataimakin gwamnan Kano kan cewa akwai siyasa a cikin tsare Abduljabbar Nasiru Kabara da aka yi.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng

