Shiri Ya Baci: 'Yan Bindiga Sun Hallaka Jami'an Tsaro a Zamfara
- An samu asarar rayukan jami'an tsaro na kungiyar 'yan sa-kai ta CJTF a jihar Zamfara da ke yankin Arewa maso Yammacin Najeriya
- Jami'an tsaron sun rasa rayukansu yayin wata arangama da suka yi da tsagerun 'yan bindiga a karamar hukumar Tsafe
- Lamarin ya auku ne makonni bayan wasu 'yan bindiga sun hallaka masallata a yankin lokacin Sallar Asuba
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Zamfara - 'Yan bindiga sun hallaka 'yan sa-kai na CJTF akalla guda takwas a jihar Zamfara.
'Yan sa-kan na CJTF sun rasa rayukansu ne a harin da ‘yan bindiga suka kai a kauyen Dan Loto, da ke karamar hukumar Tsafe, jihar Zamfara.

Source: Facebook
Jaridar Daily Trust ta kawo rahoto cewa mambobin CJTF sun faɗa tarkon ‘yan bindiga ne a lokacin da suke amsa kiran gaggawa kan yunƙurin maharan na kawo hari ga al’umma.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Harin ya faru ne kusan makonni biyu bayan da wasu ‘yan bindiga suka kai hari a masallaci, inda suka kashe mutane biyar ciki har da limami a yankin.
Ƙauyen Dan Loto na cikin Yandoton Daji, inda aka kashe waɗannan masallata a ranar 26 ga watan Satumba, 2025.
Yadda 'yan bindiga suka kashe jami'an CJTF
Wani mazaunin yankin mai suna Usman Yusuf Tsafe ya tabbatar da cewa an kashe mambobin na CJTF yayin musayar wuta da ‘yan bindigan.
"Mai yiwuwa ‘yan bindigan sun samu labarin zuwan ‘yan sa-kan ne, shi ya sa suka yi musu kwanton-bauna."
“Sun kashe su sannan suka gudu zuwa cikin daji. Ba su kai hari ga mazauna kauyen ba, sun yi niyyar farmakar jami'an CJTF din ne kawai."
- Usman Yusuf Tsafe
Mutanen Zamfara sun firgita saboda harin
Wani mazaunin Yandoton Daji, mai suna Aliyu Danlami, ya bayyana cewa al’ummar yankin sun shiga fargaba da rudani bayan harin.
“An tattaro gawarwakin waɗanda aka kashe daga wurin harin kuma an binne su bisa tanadin da addinin Musulunci ya yi."
“Mutanen kauyen sun firgita ƙwarai, amma sun yi sa’a ba a kai hari ga al’umma ko sace kowa ba."
- Aliyu Danlami
Karanta karin wasu labaran kan 'yan bindiga
- 'Yan bindiga sun tare babbar hanya a Zamfara, sun sace shugaban majalisar Malamai
- 'Yan bindiga sun tafka barna bayan tare matafiya a Zamfara
- Zamfara: Yan bindiga sun dauke kansiloli, sun sace limami bayan idar da Sallah
- 'Yan bindiga sun bude wuta a masallaci ranar Juma'a, mutane da dama sun mutu
'Yan bindiga sun sace mutane a Zamfara
A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu 'yan bindiga dauke da makamai, sun yi awon gaba da mutanen da ba su ji ba, ba su gani ba a jihar Zamfara.
'Yan bindigan sun sace mutane 30 yayin wani hari da suka kai a kauyen Zamfarawa, da ke gundumar Zugu cikin karamar hukumar Bukkuyum ta jihar Zamfara.
Miyagun 'yan bindigan sun yi dirar mikiya a kauyen kafin daga bisani su bude wuta kan mai uwa da wabi.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

