Nnamdi Kanu: Tsohon Shugaban Kasa Zai Gana da Tinubu kan Jagoran 'Yan Ta'adda a Najeriya

Nnamdi Kanu: Tsohon Shugaban Kasa Zai Gana da Tinubu kan Jagoran 'Yan Ta'adda a Najeriya

  • Fitaccen dan gwagwarmayar nan, Omoyele Sowore ya gana da tsohon shugaban kasa, Dr. Goodluck Jonathan a Abuja
  • Sowore ya bayyana cewa ya ziyarci Jonathan ne kan batun sakin shugaban kungiyar ta'addanci ta IPOB, Nnamdi Kanu
  • Ya ce tsohon shugaban kasar ya yi alkawarin zuwa ya gana da Bola Tinubu domin jin inda aka kwana kan jagoran na IPOB

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan ya amince zai gana da shugaba Bola Ahmed Tinubu kan batun shugaban ƙungiyar ta'addanci, IPOB, Nnamdi Kanu.

Wannan bayani ya fito ne daga bakin fitaccen ɗan gwagwarmaya, Omoyele Sowore, bayan ganawar da ya yi da Jonathan a Abuja ranar Jumma’a.

Sowore tare da Jonathan.
Hoton dan gwagwarmaya, Omoyele Sowore tare da Goodluck Jonathan lokacin da ya kai masa ziyara a Abuja. Hoto: @omoyelesowore
Source: Twitter

Kanu: Jonathan ya shiga layin su Sowore

A cikin sakon da ya wallafa a shafinsa na X, Sowore ya ce Jonathan ya amince cewa akwai bukatar kawo karshen lamarin Nnamdi Kanu cikin gaggawa, adalci da tsari.

Kara karanta wannan

Wasu daga cikin mutane 175 da Tinubu ya yi wa afuwa da laifin da suka aikata

Sowore ya bayyana cewa tsohon shugaban ƙasar ya shiga cikin jerin manyan ‘yan Najeriya da ke kira da a tabbatar da adalci ga Nnamdi Kanu.

Daga cikin wadanda suka shiga wannan fafutuka ta neman sakin Kanu akwai tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, Femi Falana (SAN), Sanata Shehu Sani, da wasu fitattun mutane a Najeriya.

Jonathan zai gana da Tinubu kan Nnamdi Kanu

Sowore ya rubuta cewa:

“Da safiyar yau a Abuja, na gana da tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan domin tattauna batun ci gaba da tsare Mazi Nnamdi Kanu.
"Jonathan ya amince cewa ya kamata a hanzarta wajen magance wannan batu cikin gaskiya da adalci.
"Ya kuma yi alkawarin zuwa ya gana da shugaba Bola Ahmed Tinubu domin tattauna wa kan lamarin.”

Sowore ya soki ci gaba da tsare Kanu

Sowore ya yi ikirarin cewa ana tsare da Kanu ne saboda ya tsaya kan gaskiya wajen fallasa yadda ake nuna wariya da take hakki a siyasar Najeriya.

Kara karanta wannan

Sanatan APC ya kafa misali da Trump, ya ce da yiwuwar ya zama shugaban Najeriya a 2039

“Su na tsare da Mazi Nnamdi Kanu har yanzu saboda ya tsaya tsayin daka wajen bayyana matsalar take haƙƙin yankuna da wariyar siyasa a Najeriya.
"Kamar yadda aka saki wasu masu fafutuka daga yankuna daban-daban bayan an janye tuhume-tuhumen da ke kansu, ya dace a sake shi ba tare da ɓata lokaci ba.”

- In ji Omoyele Sowore.

Dan gwagwarmaya, Omoyele Sowore.
Hoton fitaccen dan gwagwarmayar nan, Omoyele Sowore. Hoto: @yelesowore
Source: Facebook

Ya kuma yi kira ga shugabanni na siyasa, addini, al’adu da ƙabilu su haɗa kai wajen neman adalci ga Nnamdi Kanu.

“Ina roƙon ‘yan uwa daga Kudu maso Gabas kamar Peter Obi, Charles Soludo, Alex Otti, Francis Nwifuru, Peter Mbah, Hope Uzodinma, Obiageli Ezekwesili, da John Mbata na Ohanaeze Ndigbo, su haɗa kai da sauran ‘yan Najeriya wajen neman a sake Nnamdi Kanu."

Atiku ya goyi bayan kiran a saki Nnamdi Kanu

A wani labarin, kun ji cewa tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar ya shiga layin masu kira da a saki shugaban IPOB, Nnamdi Kanu.

Atiku, ɗan takarar shugaban ƙasar PDP a zaɓen 2023 ya buƙaci gwamnatin tarayya ta saki jagoran IPOB, Mazi Nnamdi Kanu, ko ta gurfanar da shi a kotu.

Kara karanta wannan

Atiku ya shiga sahun masu neman fito da shugaban kungiyar ta'addanci da aka kama tun 2021

Ya kuma nuna goyon bayansa ga kamfen ɗin da Omoyele Sowore ke jagoranta domin ganin an saki Kanu ko kuma a gurfanar da shi a kotu.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262