'Yan Ta'adda Sun Faki Ido, Sun Kai Hari Sansanin Sojojin Najeriya, An Rasa Rayuka da Dama

'Yan Ta'adda Sun Faki Ido, Sun Kai Hari Sansanin Sojojin Najeriya, An Rasa Rayuka da Dama

  • Yan ta'adda da ake kyautata zaton mayakan ISWAP ne sun kai hari sansanin Sojojin Najeriya da ke Ngamdu a kan titin Maiduguru zuwa Damaturu
  • Rahotanni sun bayyana cewa 'yan ta'addan sun mamayi sojojin da ke bakin aiki, suka bude masu wuta da misalin karfe 2:00 na safiyar yau Juma'a
  • Ana fargabar sojoji da dama sun rasa rayukansu a harin yayin da wata majiya ta ce an ga motar ujila na kwashe wadanda suka ji rauni

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Borno - Rahotanni sun nuna cewa mayakan kungiyar ta'addanci ta ISWAP sun kai mummunan hari da safiyar ranar Juma’a a wani sansanin sojoji da ke jihar Borno.

Yan ta'adda sun kai hari kan sojoji a wani sansanin rundunar soji da ke Ngamdu, a kan hanyar Maiduguri–Damaturu, cikin ƙaramar hukumar Kaga ta jihar Borno.

Kara karanta wannan

Ana batun zargin kisan Kiristoci, yan bindiga sun yi ta'asa a masallacin Katsina

Jihar Borno.
Hoton taswirar jihar Borno. Hoto: Legit.ng
Source: Original

Jaridar Leadership ta tattaro cewa ana fargabar sojoji da dama sun mutu a harin da kungiyar ISWAP, wacce ta balle daga Boko Haram ta kai yau Juma'a.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mayakan ISWAP sun mamayi sojoji a Borno

Majiyoyi sun ce mayakan ISWAP ɗin sun mamayi sansanin da misalin ƙarfe 2:00 na dare, inda suka fara harbe-harbe, suka bude wuta kan sojojin da ke bakin aiki.

A cewar wata majiyar tsaro, bayan harin, dakarun sojoji sun toshe hanyar Maiduguri zuwa Damaturu, wanda hakan ya sa fasinjoji da direbobi da dama suka makale a hanya ba tare da sanin abin da ke faruwa ba.

“Rahotanni sun nuna cewa ’yan ta’addan sun kai harin ne cikin dare, inda suka yi wa sansanin sojoji na Ngamdu kwantan ɓauna kuma suka jawo asarar rayuka da raunuka ga jami’an tsaro,” in ji majiyar.

Wane hali sojoji ke ciki bayan harin?

Majiyar ta kara da cewa tuni motar asibiti ta kwashi dakarun sojojin da suka jikkata zuwa asibiti domin kula da lafiyarsu.

Kara karanta wannan

Sojoji sun samu gagarumar nasara kan 'yan bindiga a Sokoto

A cewar majiyar:

“Da safiyar yau, an ga motar asibitin sojoji tana ɗaukar wasu daga cikin sojojin da suka jikkata zuwa asibitin koyarwa na Jami’ar Yobo da ke Damaturu domin kula da su."
Dakarun soji.
Hoton jami'an rundunar sojojin Najeriya a bakin aiki. Hoto: @NigeriaArmy
Source: Facebook

Sojoji sun toshe titin Damaturu-Maiduguri

Rahotanni sun nuna cewa matafiya da da suka fito daga Maiduguri da Damaturu sun makale a kan titin yayin domin jami’an tsaro suka toshe hanyar bayan harin.

Wani matafiyi ya shaida wa wakilin jaridar The Nation cewa harin ya faru ne da daddare a sansanin sojoji na Ngamdu, wanda ke da nisan kasa da kilomita 50 daga Damaturu.

“Dubban matafiya da motoci sun makale a nan titin Damaturu zuwa Maiduguri. Babu wanda ya san makomarmu ko lokacin da za a sake buɗe wannan hanya da ke cike da zirga-zirgar jama’a," in ji shi.

Dakarun Sojoji sun ragargaji yan bindiga a Neja

A wani labarin, kun ji cewa dakarun sojojin Najeriya da ke aiki tare da ’yan sa-kai sun yi artabu da ’yan bindigar da suka addabi jama'a a jihar Neja.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun samu nasara kan mutanen da ake zargi da kisan 'yar jarida a Abuja

An ruwaito cewa sojojin sun fafata da 'yan bindigan ne a kauyen Dare Biyu, kusa da Beri, a karamar Hukumar Mariga ta jihar Neja a ranar Litinin.

A wannan musayar wuta, an samu nasarar hallaka ’yan bindiga da dama, yayin da wani ɗan sa-kai ya rasa ransa, sannan wani ya jikkata sakamakon harbin bindiga.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262