Trump Ya Bar Mata Tsirara, Tsarinsa Ya Jefa Masu Ciki a Barazanar Kanjamau

Trump Ya Bar Mata Tsirara, Tsarinsa Ya Jefa Masu Ciki a Barazanar Kanjamau

  • Rage tallafin da Amurka ke baiwa Najeriya ya bar mata masu dauke da juna biyu da ke dauke da cuta mai karya garkuwar jiki a matsala
  • Bayanai sun nuna cewa janye tallafin ya sa an samu raguwar magungunan da ke taimaka wa masu juna biyu masu dauke da cutar
  • Rahotanni sun bayyana cewa wasu daga cikin masu karban maganin ba sa iya biyan kudin mota zuwa asibiti saboda rage yawan maganin da ake ba su

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Kasar USA – A yayin da gwamnatin Amurka ke rage tallafin kudIn agaji na kasashen waje, musamman ga Najeriya, mata masu juna biyu masu dauke da HIV sun shuga matsala.

Ba su kadai ba, har da sauran masu fama da cutar HIV/AIDS na fuskantar babbar matsala wajen samun magunguna masu muhimmanci a karkashin shirin.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: Za a rika biya wa talabijin da radiyo haraji, jama'a sun fara korafi

Shugaban Amurka ya janye tallafi ga Najeriya
Hoton Shugaban Kasar Amurka, Donald Trump Hoto: Donald J Trump
Source: Getty Images

Jaridar Premium Times ta wallafa cewa wannan lamari ya shafi Kyuntu John, wata uwa mai yara uku, wadda ta kusan karasa magungunanta na antiretroviral (ART).

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Trump ya jefa masu kanjamau a matsala

Ita jaridar The Guardian ta ruwaito cewa Amurka ta dakatar da mafi yawa daga cikin tallafin agaji da take bai wa Najeriya.

Ta dauki matakin duk da kalubalantarta ta hanyar shari’a da aka yi, kuma har yanzu wasu shirye-shiryen lafiya sun ci gaba da fuskantar tangarɗa.

Wannan ya jefa mata kamar Kyuntu cikin mawuyacin hali wajen samun kudin tafiye-tafiye zuwa asibitoci domin karɓar magunguna da ake buƙata.

Mata sun shiga matsala saboda Donald Trump
Shugaban Kasar Amurka, Donald Trump Hoto: Donald Trump J Trump
Source: Twitter

Ta ce a baya tana samun magunguna har tsawon watanni shida, amma yanzu ana iyakancewa zuwa watanni uku kacal saboda matsin ƙarancin kayan aiki.

Umarnin Donald Trump ya jawo matsala

Yayin da wasu daga cikin masu dauke da cutar kanjamau ke fama, a’aikatan lafiya kuma suna ƙara aiki da wahala domin cike gibin da ragin tallafin ya haddasa.

Kara karanta wannan

Najeriya na cikin hadari da WHO ta tabbatar da bullar cutar Chikungunya a kasashe 40

A baya, ana cika magungunan ART na marasa lafiya duk wata guda; daga baya, an sauya zuwa watanni uku, sannan watanni shida domin sauƙaƙa aiki da bai wa mutane sauƙi.

Likitoci da masu ba da kulawa sun nuna damuwa cewa tsallake amfani da magunguna na iya jawo illa mai girma, ga lafiyar uwa da ɗanta.

Marasa lafiya da dama sun bayyana cewa ba su da ikon biyan kudin mota a kai a kai, musamman ma waɗanda suke rayuwa a nesa da asibitoci saboda tsoron za a gane suna da HIV.

Ya zuwa yanzu, an kiyasta cewa fiye da miliyoyin mutane biyu ke rayuwa da cutar HIV a Najeriya, kuma dokar Trump ta jawo jefa su a cikin matsala.

Hukumar UNICEF ta ce cigaban da ake samu wajen kariya da jiyya na yara da matasa ya tsaya cak, musamman a yadda ake samun wannan matsala.

Shugaba Trump ya garzaya asibiti

A baya, kun ji cewa Donald Trump, tsohon shugaban Amurka, ya garzaya asibiti domin a gudanar da gwajin lafiya domin tabbatar ingancin lafiyarsa.

Wannan ziyarar ta janyo cece-kuce da tambayoyi daga jama’a kan halin da yake ciki da kuma yadda wannan zai shafi tsayuwarsa a fagen siyasa yayin da ya ke kan mulki.

Kara karanta wannan

"Tinubu ya yi abin da muke ta kira," Sarki Sanusi II ya hango goben tattalin arziki

Likitoci sun shiga cikin gwaji da nazari domin tantance ko akwai wata matsala da za ta bukaci kulawa ta musamman, masu sharhi sun nuna cewa irin wannan gwaji na da muhimmanci.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng