An Gano Tsofaffin Shugabannin Najeriya 3 da ba Su Halarci Taron Majalisar Koli ba

An Gano Tsofaffin Shugabannin Najeriya 3 da ba Su Halarci Taron Majalisar Koli ba

  • Shugaba Bola Tinubu ya jagoranci taron majalisar kolin Najeriya a ranar Alhamis, karo na biyu tun bayan hawansa mulki a 2023
  • A yayin taron, 'yan majalisar kolin sun amince da nadin Farfesa Joash Amupitan a matsayin sabon shugaban hukumar INEC
  • Babban abin da ya ja hankali shi ne yadda wasu tsoffin shugabannin Najeriya uku suka gaza halartar wannan muhimmin taro

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja – A ranar Alhamis, 9 ga Oktoba, 2025, Shugaba Bola Tinubu ya jagoranci taron majalisar koli karo na biyu tun bayan hawansa mulki.

Taron ya mayar da hankali ne kan manyan batutuwa na kasa, da suka haɗa da matsalar tsaro, shirye-shiryen zaben 2027 da kuma nadin sabon shugaban hukumar INEC.

Obasanjo, Jonathan ba su halarci taron majalisar koli da Tinubu ya jagoranta ba
Hoton Shugaba Bola Tinubu, da Olusegun Obasanjo, da Goodluck Jonthan. Hoto: @officialABAT, @Oolusegun_obj, @GEJonathan
Source: Twitter

Babu Gowon, Obasanjo, Jonathan a taron

Sai dai, abin da ya fi daukar hankalin jama’a shi ne rashin halartar wasu manyan tsofaffin shugabannin kasa da suka saba kasancewa a irin wannan zama, inji rahoton Business Day.

Kara karanta wannan

Wasu daga cikin mutane 175 da Tinubu ya yi wa afuwa da laifin da suka aikata

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tsofaffin shugabannin kasa – Janar Yakubu Gowon, Olusegun Obasanjo, da Goodluck Jonathan – ba su halarci taron ba.

Gowon, wanda shi ne tsohon shugaban kasa mafi tsufa da ke raye, yana daga cikin wadanda ke da kwarewa da tarihin shugabanci da ake yawan saurara a irin wannan taro. Rashinsa ya dauki hankali matuka.

Haka kuma, Obasanjo, wanda aka sani da tsayayyen ra’ayinsa kan mulki da tsarin zabe, bai samu damar halarta ba.

Rashinsa ya a taron ya jawo ce-ce-ku-ce kasancewar taron ya tattauna batutuwan zabe da shugabancin INEC.

Shi ma tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan, wanda ke taka muhimmiyar rawa a ci gaban dimokuradiyyar Najeriya, bai samu halartar taron ba.

Halartar wasu shugabanni ta yanar gizo

An ji tsofaffin shugabannin kasa Ibrahim Babangida da Abdulsalami Abubakar sun halarci taron ta yanar gizo ba tare da zuwa fadar Aso Rock ba.

Shi ma Gwamna Charles Soludo na Anambra ya halarci taron ne ta kafafen zamani.

Kara karanta wannan

Shugaba Bola Tinubu ya yi afuwa ga wasu 'yan Najeriya 175

Sai dai rashin ganin dattawa irinsu Janar Yakubu Gowon, Olusegun Obasanjo da Goodluck Jonathan ya bar gibi a tattaunawar ta kasa.

Masana siyasa sun bayyana cewa rashin su bai shafi sahihancin shawarwarin majalisar ba, amma yana iya yin tasiri wajen gina hadin kai da amincewa tsakanin manyan dattawan Najeriya, musamman a lokacin da ake tunkarar babban zabe.

Majalisar kolin Najeriya ta amince da Farfesa Joash Amupitan matsayin sabon shugaban INEC
Sabon shugaban hukumar INEC, Farfesa Joash Ojo Amupitan zaune a ofishinsa a jami'ar Jos. Hoto: Joash Amupitan
Source: Facebook

Farfesa Amupitan ya zama shugaban INEC

A yayin taron, majalisar koli ta amince da sunan Farfesa Joash Ojo Amupitan (SAN) a matsayin sabon shugaban INEC, inji rahoton Daily Trust.

Mun ruwaito cewa, Shugaba Tinubu ne ya gabatar da sunansa domin ya maye gurbin Farfesa Mahmood Yakubu, wanda ya kammala wa’adinsa na shekaru 10.

Amupitan, mai shekara 58, farfesa ne a fannin dokoki kuma mataimakin shugaban jami’a a harkokin gudanarwa a Jami’ar Jos.

Nadinsa ya samu amincewar majalisar kolin, yanzu kuma ana jiran tabbatar da shi a majalisar dattawa.

Tinubu ya yi afuwa ga 'yan Najeriya 175

A wani labarin, mun ruwaito cewa, shugaban kasar Najeriya ya yi afuwa ga wasu 'yan Najeriya da kotu ta yankewa hukunci kan laifuffuka daban daban.

Kara karanta wannan

IBB, Abdulsalami sun halarci taron majalisar koli, karon farko babu Buhari

Mai girma Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya amince da afuwar ne yayin taron majalisar koli da aka gudanar a fadar shugaban kasa a ranar Alhmis.

Daga cikin mutanen da aka yi wa afuwa har da sanannen dan kishin kasa, marigayi Herbert Macauley, da tsohon 'dan majalisar tarayya Farouq Lawan.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com