Sanusi II Ya Sake Kare Tinubu kan Cire Tallafin Mai, Ya Tuna Lokacin Jonathan
- Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II ya yaba wa Bola Tinubu bisa jajircewarsa wajen cire tallafin mai da ya dade yana gurgunta tattalin arziki
- Sanusi II ya ce lokacin da yake gwamnan CBN, sun taba ba da shawarar cire tallafi amma wasu kalilan suka hana saboda moriyar da suke samu
- Ya kara da cewa cire tallafin man fetur dole ne, kodayake yana da tasiri ga farashin kaya ga marasa karfi, amma lamarin ya kai intaha
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kano - Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ya sake tabo batun cire tallafin man fetur da shugaban kasa, Bola Tinubu ya yi.
Basaraken ya yabawa shugaban ne bisa jajaircewa da ya yi wurin tabbatar da kawo karshen tallafin da ake cewa ana biya.

Source: UGC
Sarki Sanusi II ya bayyana haka ne a wani faifan bidiyo yayin hira da yan jarida da shafin Masarautar Kano ya wallafa a X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanusi II ya magantu kan cire tallafin mai
Yayin hirar, Sanusi II ya ce abin murna ne yadda aka kawo karshen biyan kudin tallafin da wasu ƙalilan ke cin moriya.
A cewarsa:
"Lokacin da nake gwamnan babban bankin Najeriya, CBN mun ba da shawara ga shugaban kasa ya cire tallafin mai, an cire kuma mutane sun yi zanga-zanga.
"Amma yanzu gwamnati ta cire shi, wannan shi ne abin da ya kamata, abin da shugaban kasa ya yi yanzu ya zama dole.
"Na yarda cewa idan ka ce za ka cire tallafin mai a hankali, wadanda ke cin moriyar kudin ba za su barka ka cire ba, za su yi duk mai yiwuwa domin ganin hakan bai faru ba."

Source: Twitter
Sanusi II ya kare matakin cire tallafin mai
Sanusi II ya bayyana yadda aka tattauna da kungiyar kwadago kan cire tallafin tun a lokacin mulkin Goodluck Jonathan.
Ya bayyana cewa cire tallafin dole zai jawo matsaloli da suka hada da tashin farashin kaya da suka fi shafar marasa ƙarfi.

Kara karanta wannan
Sanusi II ya yabi CBN da Tinubu, ya kawo hujjojin fitowa daga kangin tattalin arzik
"Ko a lokacin Jonathan, an tattauna da kungiyar kwadago cewa za a cire kashi 50 na tallafin mai sannan daga baya a cire sauran.
"Cire tallafin mai tabbas abu ne mawuyaci kuma na bazata, dole zai shafi wasu lamura amma idan har ba a yi hakan yadda ya kamata ba.
"Tabbas mun sani idan aka cire tallafin mai dole za a samu hauhawar farashin kaya da kuma shafar marasa karfi amma mun kai wani lokaci da muke karar da kudin, muna karbar bashi domin biyan kudin tallafin."
- Sarki Sanusi II
Sanusi II ya kare kansa kan batun dukan mata
Mun ba ku labarin cewa mai martaba Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ya ce an yi masa mummunan fahimta kan kalamansa game da dukan mata a Musulunci.
Sanusi II ya bayyana cewa bai ce mace ta rama mari ba, inda ya yi bayanin cewa maganarsa ta danganci yarsa ne, ba umarni ga sauran mata ba.
Ya kara da cewa Manzon Allah SAW ya kushe masu dukan matansu, yana mai cewa dukan mace ba alamar mutunci ko kyawawan dabi’u ba ne.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
