Hijabi: Zulum Ya Dauki Mataki kan Zargin cin Zarafin Mata Musulmai a Asibitocin Borno
- Farfesa Babagana Zulum ya umarci gudanar da bincike kan zargin cin zarafin mata musulmai masu sanya hijabi a wasu asibitoci
- Kungiyar MURIC ce ta gabatar da korafi cewa ana takura wa mata saboda sanya hijabi, lamarin da ya tada hankalin gwamnati
- Gwamna Zulum ya tabbatar da cewa gwamnatin jihar Borno ba za ta lamunci wariya ko cin zarafi ga masu bin koyarwar addini ba
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Borno - Gwamna Babagana Umara Zulum, ya umarci a gudanar da bincike mai zurfi kan zargin cewa ana cin zararafin mata masu sanya Hijabi a wasu asibitocin Maiduguri.
Wannan na zuwa ne bayan kungiyar kare hakkin Musulmai (MURIC) ta bayyana damuwarta kan rahoton da ta samu daga wasu mata da abin ya shafa.

Source: Twitter
Mai magana da yawun gwamna Babagana Zulum, Dauda Iliya ne ya fitar da sanarwa kan lamarin a shafinsa na Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hijabi: Martanin Zulum kan lamarin
Zulum, wanda ya nuna damuwarsa matuka a ranar Alhamis, ya ce duk da bai samu rahoton hukuma kai tsaye ba kan lamarin, gwamnatin sa ba za ta yi sakaci da irin wannan zargi ba.
Ya ce addinin musulunci da al’adun jihar Borno suna daraja hijabi, don haka duk wani nau’in cin zarafi ga masu sa shi abin ƙyama ne.
Daily Trust ta wallafa cewa gwamnan ya bayyana cewa gwamnati za ta yi cikakken bincike da gaskiya, tare da daukar matakin da ya dace idan aka tabbatar da gaskiyar zargin.
Wanda zai jagoranci bincike kan hijabi
A cikin umarnin da ya bayar, Gwamna Zulum ya ba wa Kwamishinan Lafiya da Walwalar Jama’a, Farfesa Baba Malam Gana, damar jagorantar binciken.
Ya bukaci kwamishinan da ya gano ainihin gaskiya game da rahoton cin zarafin, tare da gabatar da cikakken rahoto cikin gaggawa.
Gwamnan ya kara da cewa gwamnatinsa ta kuduri aniyar kare ‘yancin addini da mutuncin dukkan ‘yan jihar Borno.

Source: Twitter
Ya ce gwamnatin Borno tana girmama Hijabi da kuma mata musulmai da ke amfani da shi, don haka ba za a lamunci keta musu haddi ba.
Kira kan zaman lafiya a jihar Borno
Zulum ya roki al’umma da su kasance masu gaskiya wajen bayar da bayanai idan suna da hujjoji kan zargin da ake.
Ya ce za a gudanar da binciken cikin gaskiya da bayyana komai a fili:
“Idan aka tabbatar da cewa wani ya aikata laifi, gwamnati za ta dauki matakin ladabtarwa nan take,”
Gwamnan ya ce walwalar mata, iyaye, da ‘ya’ya mata a jihar Borno abu ne da gwamnati ke dauka da muhimmanci.
Ya kuma yi kira ga al’umma su ci gaba da zama cikin zaman lafiya da hadin kai, domin jihar Borno ta samu ci gaba cikin lumana da mutunta juna.
Zulum ya yi kyautar gida a Borno
A wani rahoton, kun ji cewa, gwamna Bababaga Umara Zulum ya ba wata ma'aikaciyar lafiya kyautar gida a jihar Borno.

Kara karanta wannan
Wata sabuwa: Za a rika biya wa talabijin da radiyo haraji, jama'a sun fara korafi
Farfesa Zulum ya ba ma'akaciyar gida ne saboda yadda ta shafe shekaru tana hidima a jihar duk da cewa 'yar kabilar Ibo ce.
Wasu rahotanni sun kara da cewa bayan mata kyautar gida, gwamna Zulum ya ba danta aikin gwamnati a jihar.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

