Hotuna: Jerin mata Musulmai guda 10 da suka fi kudi a duniya

Hotuna: Jerin mata Musulmai guda 10 da suka fi kudi a duniya

A kokarin da jaridar mu ta Legit.ng take yi na ilimantar da masu karatu da bibiyar su, jaridar ta yi kokarin zakulo muku jerin mataye guda goma na duniya da suke da arzikin da babu kamar su kaf duniya

1. Princess Ameerah ('Yar Sarkin Saudiyya)

Hotuna: Jerin mata Musulmai guda 10 da suka fi kudi a duniya
Princess Ameerah
Asali: Facebook

An haifi gimbiya Ameerah a ranar 6 ga watan Nuwambar shekarar 1983, mata ce a wajen Waleed bin Talal, yana da nasaba da gidan sarautar Saudiyya. Waleed yana da shekaru 58 kuma an bayyana shi a matsayin daya daga cikin masu kudin duniya inda ya zo a matsayin na 26 a jerin masu kudin. Yana da zunzurutun kudi har dalar Amurka biliyan ashirin da biyar ($25b), sannan kuma shine ya mallaki babban kamfanin nan mai suna 'Kingdom Holdin Company'.

2. Queen Rania (Sarauniyar kasar Jordan)

Hotuna: Jerin mata Musulmai guda 10 da suka fi kudi a duniya
Queen Rania
Asali: Facebook

An bayyana Sarauniya Rania a matsayin Sarauniyar da ta fi kowacce Sarauniya kyau a duniya, kamar yadda jaridar Harpers da kuma mujallar Queen Magazine ta ruwaito a shekarar 2011.

Ita ce matar Sarkin Jordan, Sarki Abdullah II, an haifeta a ranar 31 ga watan Agustan shekarar 1970. Mijinta shine Sarki na 51 a kasar Jordan. Bai fiya son nuna arzikin da Allah yayi masa ba sosai. Amma ya gina wata katuwar alkarya wacce ya kashe makudan kudade wanda ya sanya aka yadda cewa kwarai yana da arziki.

3. Princess Bolkiah ('Yar Sarkin Brunei)

Hotuna: Jerin mata Musulmai guda 10 da suka fi kudi a duniya
Princess Bolkiah
Asali: Facebook

Gimbiya Bolkiah ita ce 'yar Sarkin Brunei Sultan Hassanal Bolkaih, kuma mata a wajen Yam Pengiran Anak Haji Mohammad Ruzaini, an haifeta a ranar 12 ga watan Maris na shekarar 1980, sannan kuma mujallar Forbes ta bayyana mahaifinta a matsayin mutumin da yafi kowa kudi a shekarar 1997.

Sarkin yana da wata mota kirar Rolls-Royce wacce aka yita da zallar zinare, wacce tana daya daga cikin motocin da yake da su, haka kuma yana da gida mai dakuna 1,700.

Hotunan bikinta sun bar tarihi matuka a duniya.

4. Princess Lalla Salma (Matar Sarkin Morocco)

Princess Lalla Salma
Princess Lalla Salma
Asali: Facebook

Gimbiya Lalla, tana da 'ya'ya guda biyu, 'ya ce a wajen wani Malamin Makaranta, ta auri Sarkin Morocco, Mohammad IV. Mijinta yana da zunzurutun kudi har dalar Amurka biliyan biyu da rabi ($2.5b), duk da ita ce matar Sarkin kasar amma ba ta damu da sai duniya ta san da ita ba, hakan ya sanya take rayuwarta cikin sauki.

5. Sheikha Maitha (Dubai)

Hotuna: Jerin mata Musulmai guda 10 da suka fi kudi a duniya
Sheikha Maitha
Asali: Facebook

Sheikha 'yar wasan dambe ce na (Taekwondo), ta samu nasarar lashe gasar da aka yi ta dambe a yankin Asia a shekarar 2006 inda ta wakilci kasar Dubai a gasar. Mahaifin ta Sheikh Mohammed Bin Rashid Al Maktoum shine firaiministan kasar Dubai. Mahaifin ta yana da kudi sama da dalar Amurka biliyan 40 ($40b).

6. Sheikha Hanadi (Qatar)

Hotuna: Jerin mata Musulmai guda 10 da suka fi kudi a duniya
Sheikha Hanadi
Asali: Facebook

Sheikha Hanadi 'yar kasuwa ce, sannan kuma ita ce mai ba da shawara a bankin Standard Chartered. Tana da zunzurutun kudi sama da dalar Amurka biliyan goma sha biyar ($15b).

7. Princess Fathima ('Yar Sarkin Saudiyya)

Hotuna: Jerin mata Musulmai guda 10 da suka fi kudi a duniya
Princess Fathima
Asali: Facebook

Ita ce Sarauniyar kasar da tafi kowacce kasa arzikin man fetur, inda kashi 39 na man kasar mallakin gidan sarautar su ne. Ita ce matar Sheikh Avdi Al Muhammad.

8. Sultana Nur Zahirah (Sarauniyar Malaysia)

Hotuna: Jerin mata Musulmai guda 10 da suka fi kudi a duniya
Sultana Nur Zahirah
Asali: Facebook

Ita ce matar Sarki Al Wathiqu an haife ta a ranar 7 ga watan Disambar shekarar 1973. Ita ce Sarauniya ta 13 a kasar Malaysia, ita ma tana da kudi sama da dalar Amurka biliyan goma sha biyar ($15b).

9. Princess Hajah Majeedah ('Yar Sarkin Brunei ta hudu)

Hotuna: Jerin mata Musulmai guda 10 da suka fi kudi a duniya
Princess Hajah Majeedah
Asali: Facebook

Ita ce 'yar Sarkin Brunei ta hudu, wanda yake shine mutumin da yafi kowa kudi a duniya a shekarar 1997, ta auri Khairul Khalil, wanda yake shine mataimaki na musamman a ofishin firaministan kasar.

10. Sheikha Mozah (Qatar)

Hotuna: Jerin mata Musulmai guda 10 da suka fi kudi a duniya
Sheikha Mozah
Asali: Facebook

Ita ce mata ta biyu a wajen Sheikh Hamad Bin Khalifa, yana da kudi sama da dalar Amurka biliyan bakwai ($7b).

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel