Wasu daga cikin Mutane 175 da Tinubu Ya Yi wa Afuwa da Laifin da Suka Aikata
Gwamnatin Tarayya ta yi wa wasu mutane afuwa domin su sake samun damar komawa cikin al’umma kamar sauran marasa laifi.
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT, Abuja – Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu ya sanar da yafe wa manyan mutane 175 wasu manyan laifuffuka da su ka aikata, wasu daga cikinsu sun rasu.
Bayo Onanuga, hadimin Shugaban Kasa ya wallafa a shafinsa na X cewa daga cikin wadanda aka yafe wa akwai tsohon ɗan majalisa.

Source: Facebook
Legit ta tattaro wasu daga cikin mutum 17 da aka yi wa afuwa da laifuffukan da aka tabbatar sun aikata gabanin hukunta su.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
1. Mamman Vatsa
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi wa Manjo Janar Mamman Vatsa, tsohon Ministan Babban Birnin Tarayya da abokin ƙuruciyar tsohon shugaban mulkin soja Janar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB), afuwa bayan rasuwarsa.

Kara karanta wannan
Maryam Sanda da wasu sanannun mutane 5 da suka shiga cikin wadanda Tinubu ya yi wa afuwa
An zargi Vatsa da hannu a cikin yunƙurin juyin mulki a 1985, wanda ya yi sanadiyyar kamawa da kuma kashe su tare da wasu hafsoshin soja tara a watan Maris 1986, ƙarƙashin gwamnatin abokinsa, Babangida.
Babangida ya taɓa bayyana cewa ɗaukar wannan mataki na kashe abokinsa ya kasance ɗaya daga cikin lokutan da suka fi wahalar rayuwarsa.
Ya bayyana cewa binciken da jami’an leƙen asirin soja suka gudanar ya tabbatar da cewa Vatsa na da hannu kai tsaye a shirin juyin mulkin tare da bayar da kuɗi ga wasu daga cikin hafsoshin da aka zarga.
2. Herbert Macaulay
Shugaba Tinubu ya kuma yi wa Herbert Macaulay, wanda ake ɗauka a matsayin uban samuwar ‘yancin Nijeriya, afuwa bayan rasuwarsa.
An taɓa yankewa Macaulay hukunci sau biyu a ƙarƙashin gwamnatin Turawa ta Birtaniya a birnin Legas.
A shekarar 1913, lokacin da yake aiki a matsayin mai auna filaye mai zaman kansa, aka gurfanar da shi a gaban kotu bisa zargin yin almundahanar wasu kadarori.
Daga baya Macaulay ya zama ɗaya daga cikin fitattun masu fafutukar neman ‘yancin kai a Nijeriya, inda ya kafa jam’iyyar NNDP sannan ya taimaka wajen kafa NCNC.
3. Hon. Farouk Lawan
Hukumar ICPC ta wallafa cewa Farouk Lawan, an same shi da laifin karɓar $500,000 a matsayin cin hanci daga mai kamfanin man fetur, Femi Otedola.
Ya karbu kudin a lokacin da yake shugaban kwamitin majalisar wakilai da ke binciken batun tallafin man fetur a 2012.

Source: Facebook
An fara yanke masa hukuncin shekara bakwai a gidan yari, daga baya aka rage zuwa shekara biyar, wanda kotun koli ta tabbatar a watan Janairu 2024.
'Dan majalisar ya yi zaman gidan yari kuma a karshen shekarar 2024 ya bar kurkukun Kuje.
4. Mrs. Anastasia Daniel Nwaobia
Daily Post ta ruwaito cewa Tsohuwar sakatariya a ma’aikatar cikin gida, Anastasia Daniel Nwaobia, ta gamu da fushin hukuma.
Kotu ta yanke mata hukunci kan badakalar daukar ma’aikatan hukumar shige da fice (NIS) a 2014, inda matasa da dama su ka rasu a wajen neman aikin.
An same ta da laifin satar kuɗi da karya tsarin kwangila, inda aka karɓi kuɗin rajista daga dubunan matasa da suka nemi aiki.
5. Dr. Saadu Ayinla Alanamu
ICIR ta wallafa cewa hukumar ICPC ta tuhumi Dr. Saadu Ayinla Alanamu, tsohon shugaban majalisar gudanarwa ta Kwara Polytechnic da karbar rashawa.
Kotu ta kuma same shi da laifin karɓar cin hancin N5m daga wani ɗan kwangila domin bayar da kwangilar gina dakin taro mai kimanin N182m.
Kamfanin da aka ba kwangilar bai cancanci aikin ba, amma aka amince da shi saboda cin hanci, wanda ya jawo Kotun koli ta yanke masa shekaru 12 a gidan yari.
6. Nweke Francis Chibueze
Law global hub ta ruwaito cewa an samu Nweke Francis Chibueze da laifin fitar da hodar iblis mai nauyin kilo 1.416 ba tare da izini ba.
Kotun tarayya ta yanke masa hukuncin daurin rai da rai a gidan yari bayan tabbatar da laifin safarar miyagun ƙwayoyi.
A ranar Alhamis shugaban kasa ya yafe masa laifinsa kamar yadda sanarwa ta gabata.
7. Dr. Nwogu Peters
Kotu ta samu Dr. Nwogu Peters, wanda aka fi sani da Dr. N.D.C. Peters da laifin damfara ta kadarori da almundahana ta hanyar tallata gidaje da filaye na bogi.

Kara karanta wannan
Farouk Lawan: Abin da tsohon dan majalisa a Kano ya fadawa Tinubu bayan masa afuwa
An kuma kama shi da laifin karɓar kuɗi daga mutane da suka nemi haya, da kuma bayar da takardun karbar kudi na bogi, kamar yadda EFCC ta wallafa.
An yanke masa hukuncin shekaru 17 a gidan yari ba tare da zabin tara ba, tare da umartar shi ya biya waɗanda ya yaudara, an yade masa kafin ya gama zaman kaso.
8. Mutum 9 a Ogoni
AP News ta wallafa cewa an tabbatar da cewa an kashe wasu mutane tara a Ogoni da ke fafutuka kare muhalli da hakkin ɗan adam a mulkin Janar Sani Abacha a shekara ta 1995.
Sun hada da:
1. Ken Saro-Wiwa
2. Saturday Dobee
3. Nordu Eawo
4. Daniel Gbooko
5. Paul Levera
6. Felix Nuate
7. Baribor Bera
8. Barinem Kiobel
9. John Kpuine
An gurfanar da su a gaban kotun soja ta musamman inda aka same su da laifin kisan wasu shugabannin ƙabilar Ogoni huɗu.
Wadanda su ka kashe sun hada da Cif Albert Badey, Cif Edward Kobani, Cif Samuel Orage, da Theophilus Orage, waɗanda aka kashe a Mayu 1994 sakamakon rikicin MOSOP.
Kotun ta yanke musu hukuncin kisa ta hanyar rataya, kuma aka aiwatar da hukuncin a ranar 10 ga Nuwamba, 1995.
Lauya: Doka ta ba Tinubu damar yafiya
Fitaccen lauya kuma mai sharhi a kan al'amura, Barista Isma'il Kiyawa ya tabbatar wa Legit cewa abin da Bola Tinubu ya yi, yana kan tsarin doka.
Ya ce:
"Dokar kasa ta ba Shugaba Bola Tinubu dama ya yafe wa duk wanda ya so, a sanda ya ga dama."
"Kuma zai iya yafe wanda ya ga dama, sai dai a na shi shawara a kan wanda ya fi kamata ya yafe wa."
Tinubu ya yi wa mutum 17 afuwa
A baya, mun wallafa cewa Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu ya amince da yin afuwa ga mutane 175 daga sassa daban-daban na Najeriya da su ka aikata laifi.
An gabatar da jerin sunayen da manyan lauyoyi suka yi a madadin Tinubu, wadanda aka yafe wa sun hada da Herbert Macaulay da Manjo Janar Mamman Vatsa (mai ritaya).
Gwamna Uba Sani ya yabawa wannan mataki na Shugaba Tinubu, inda ya ce ya nuna ƙoƙarinsa wajen tabbatar da adalci da gyara ga waɗanda shari'a ta azabtar.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


