Abubuwan da Ya Kamata Ku Sani kan Hukuncin Kotu game da Masarautar Kano

Abubuwan da Ya Kamata Ku Sani kan Hukuncin Kotu game da Masarautar Kano

Mai marataba Aminu Ado Bayero ya sanar da daukaka kara bayan kotun tarayya ta ba gwamnatin nasara kan tsige shi

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kano - A makon da ya wuce kotun daukaka kara ta yanke hukunci kan karar da bangaren mai martaba Aminu Ado Bayero ya shigar da gwamnatin Kano.

Bangaren mai martaba Aminu Ado Bayero ya shigar da gwamnatin Kano kara ne kan tube shi daga sarautar Kano da Abba Kabir Yusuf ya yi.

Sanusi II
Muhimman abubuwa kan hukuncin kotu game da masarautar Kano. Hoto: Masarautar Kano
Asali: Facebook

A wannan rahoton, mun tattaro muku wasu muhimman abubuwa da ya kamata ku sani a kan hukuncin da kotu ta yi a kan shari'ar masarautar Kano.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dawo da shari'a zuwa kotun jihar Kano

A ranar 10 ga Janairu, 2025, wata kotu da ke Abuja ta yanke hukunci mai muhimmanci kan rikicin masarautar Kano.

Kara karanta wannan

Tinubu ya bugi karji kan darajar Afrika a Qatar, ya fadi sirrin cigaban nahiyar

Kotun ta soke hukuncin Kotun Tarayya da ke Kano wanda ya rushe nadin Muhammadu Sanusi II a matsayin Sarkin Kano na 16.

Hukuncin ya dawo da lamarin shari'ar zuwa Kotun Jihar Kano, tare da jaddada cewa ana bukatar a sake sauraron shari’ar a matakin jiha.

A kan haka ne This Day ta wallafa cewa kotu ta umarci Aminu Baba-Dan’Agundi ya mayar da karar gaban kotun Kano domin sauraron kokensa.

Aminu Ado
Mai martaba Aminu Ado Bayero da Babba Dan Agundi. Hoto: Masarautar Kano
Asali: Facebook

An laftawa Dan Agundi biyan N500,000

Kotun daukaka kara, karkashin jagorancin Mai Shari’a Gabriel Kolawole, ta yi fatali da hukuncin da Kotun Tarayya ta yanke a watan Yunin 2024.

Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa kotun ta umarci mai shigar da kara, Aminu Baba-Dan’Agundi da ya biya gwamnatin Kano N500,000.

Batu kan zarge-zargen da aka gabatar

Kotun daukaka ta soke tuhume-tuhumen da aka shigar, wadanda suka hada da:

1. Zargin Rashin bin ka’ida wajen nada Sanusi II

Kara karanta wannan

Rikicin Masarautar Kano: Aminu Ado Bayero zai daukaka kara zuwa Kotun Koli

4. Kalubalantar hurumin majalisar jihar wajen yin gyare-gyare ga dokar masarauta

A dunkule, jaridar Tribune ta wallafa cewa Dan'Agundi ya ce babban abin da suke kalubalanta shi ne yadda aka soke dokar da ta kawo Aminu Ado Bayero ba tare da sauraron bangarensa ba.

Dan'Agundi ya ce sun amince majalisar Kano na da hurumin sauke sarki amma dole a bi hanyar da ta dace.

Me magoya bayan Aminu Bayero suka ce?

A yayin da rikicin masarautar Kano ke kara tsananta, wani fitaccen dan sarauta kuma mai nada sarki, Aminu Babba Dan'Agundi ya ce yanzu ma aka fara rikicin bayan hukuncin kotu.

Daily Trust ta wallafa cewa ya ce hukuncin ya bude wani sabon babi a cikin rikicin, tare da bai wa bangaren Bayero damar ci gaba da fafutukar neman adalci.

“Rikicin bai kare ba; a maimakon haka, mun shiga wani sabon mataki na fadan ganin an yi adalci.”

Kara karanta wannan

Lauya ya fadi hanyar da ta ragewa Aminu Ado bayan nasarar Sanusi II a kotu

- Babba Dan'Agundi

Dan'Agundi ya kara da cewa akwai bukatar duba yadda aka gudanar da nadin Sanusi II a matsayin Sarkin Kano, musamman dangane da dokokin da aka ce an karya wajen nada shi.

Sarkin Kano
Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II. Hoto: Masarautar Kano
Asali: Twitter

Bangaren Aminu Bayero ya daukaka kara

Jaridar Vanguard ta wallafa cewa bangaren Alhaji Aminu Ado Bayero ya bayyana aniyarsa ta daukaka kara zuwa Kotun Koli.

Wannan mataki ya biyo bayan hukuncin kotu da ya soke wasu shari’o’in da koka kan nadin Muhammadu Sanusi II a matsayin Sarkin Kano na 16.

Masarautar Kano: Me zai faru a karshe?

Bangaren Bayero ya nuna rashin gamsuwa da hukuncin kotu inda ya bayyana cewa, za su dauki matakin karshe domin tabbatar da cewa an yi adalci a shari'ar.

Babba Dan'Agundi ya ce sun yi imani cewa kotun daukaka kara za ta kalli lamarin cikin tsanaki tare da yanke hukunci mai kyau wanda zai kare al’adun gargajiya da mutuncin masarautar Kano.

Kara karanta wannan

'Muna kan tsari': Abba Kabir ya magantu bayan hukuncin kotu, ta ba yan Kano shawara

Barista Abba Hikima ya ce duk da kowane bangare na ikirarin samun nasara, za a iya cewa bangaren Sanusi II sun fi samun nasara idan aka kalli hukuncin kotun koli.

A yanzu haka dai kallo ya koma kan bangarorin Aminu Ado Bayero da Sanusi II domin ganin matakin da za su dauka idan shari'ar ta cigaba.

Aminu Ado ya ziyarci jihar Nasarawa

A wani rahoton, kun ji cewa mai martaba Aminu Ado Bayero ya ziyarci jihar Nasarawa domin ta'aziyyar rasuwar matar sarki.

Rahoton Legit ya nuna cewa ya ziyarci sarkin Keffi ne Alh. Dr Shehu Cindo Yamusa na Jihar Nassarawa bisa rasuwar matarsa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng