ADC Ta Yi Baki 1 da Bankin Duniya a kan Karuwar Talauci a Mulkin Tinubu
- ADC ta sako gwamnatin APC a karkashin Bola Ahmed Tinubu a gaba bayan rahoton da Bankin Duniya ya fitar na cewa talauci ya karu
- A cewa rahoton, mutanen kasar nan akalla miliyan 139 ne su ka kara dulmiya a cikin bakin talauci a duk da manufofin Bola Tinubu
- Mai magana da yawun ADC, Bolaji Abdullahi ya ce yanzu ba lokacin burga ba ne, har ma ya ba gwamnatin APC shawara a kan inganta rayuwar talaka
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Jam’iyyar ADC ta bukaci Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya amince da rahoton da Bankin Duniya ya fitar a kan karuwar talauci a Najeriya, domin gaskiya ne.
Rahoton bankin ya nuna cewa mutane miliyan 139 a Najeriya yanzu na rayuwa a cikin bakin talauci, karin mutane miliyan 58 daga miliyan 81 a shekarar 2019.

Kara karanta wannan
Durkusa wa wada: Gwamnatin Tinubu ta roki ASUU, ta dauki sabon alkawarin hana yajin aiki

Source: Facebook
Jaridar Punch ta wallafa cewa Bolaji Abdullahi, mai magana da yawun jam’iyyar na kasa, ya ce rahoton na Oktoba 2025 ya bankado banbancin kalaman gwamnati da ci gaban jama'a.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jam'iyyar ADC ta soki gwamnatin Tinubu
Ita kuwa Daily Post ta wallafa cewa bai kamata gwamnatin tarayya ta rika musu a kan rahoton da Bankin Duniya ya fitar a kan talauci ba.

Source: Facebook
A cewar Bolaji Abdullahi:
"Wannan rahoto shaida ce ta zahiri da ke nuna cewa tsarin tattalin arzikin gwamnati mai ci bai taimaka wa 'yan kasa ba. Idan a 2019 mutane hudu daga cikin goma ke cikin talauci, yanzu mutane shida ne cikin goma."
ADC: Talauci ya karu a Najeriya
ADC ta soki yadda gwamnati ke yawan magana kan samun kudin shiga, amma ba ta magance matsalolin da ke jefa jama’a cikin mawuyacin hali ba.
Jam’iyyar ta ce:
“Farashin buhun shinkafa ya karu sau biyar cikin shekara hudu, kuma mafi yawan iyalai suna kashe 70% na kudin shiga wajen sayen abinci kawai. Babu abin da ya rage domin haya, kudin makaranta, ko magani.”
Haka zalika, jam’iyyar ta soki gazawar tsare-tsaren tallafi, inda tace:
“A 2019, mutane 20 a cikin 100 na karbar tallafi daga gwamnati. Amma a 2025, wannan adadi ya ragu zuwa 6%. Gwamnati na kashe 0.14% ne kacal na GDP wajen taimaka wa talakawa, alhali kasashen duniya na kashe akalla 1.5%.”
ADC ta ce a maimakon gwamnati ta cigaba da kare kanta da karya, kamata ya yi ta karbi wannan gaskiyar daga abokiyar hulda kamar Bankin Duniya.
Jam’iyyar ta bukaci gwamnati ta daina yin alfahari da kudin shiga, ta mayar da hankali wajen samar da tsaro na abinci, ayyukan yi da kariya ga jama’a.
Gwamnati: "Babu karuwar talauci a Najeriya"
A wani labarin, mun ruwaito cewa Fadar shugaban kasa ta Najeriya ta musanta rahoton Bankin Duniya da ya bayyana cewa kusan mutane miliyan 139 a Najeriya suna cikin talauci.
Sunday Dare, mai bai wa shugaban kasa shawara kan yada labarai, ya bayyana wannan matsaya ne ta fadar shugaban kasa a wani sakon da ya fitar bayan rahoton Bankin Duniya.

Kara karanta wannan
Atiku ya shiga sahun masu neman fito da shugaban kungiyar ta'addanci da aka kama tun 2021
Ya ce alkaluman da Bankin Duniya ta yi amfani da su sun dogara ne da tsofaffin kididdiga, wanda, idan aka fassara zuwa Naira, ya kai kusan N100,000, wanda ya fi mafi karancin albashi.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
