Majalisa Ta Fara Binciken yadda NNPCL Ya Kashe $18bn a kan 'Matattun' Matatun Mai
- Majalisar wakilai ta fusata a kan yadda aka kashe biliyoyin Dala a wajen gyara matatu mallakin gwamnati, amma har yanzu ba canji
- 'Dan majalisa, Hon. Sesi Oluwaseun Whingan ne ya gabatar da kudiri a kan bukatar a yi bincike, a gano inda matsalar matatun su ke
- Ya tunatar da yadda gwamnatin Najeriya ta kashe abin da ya haura Dala Biliyan 18 domin farfado da matatun Kaduna, Warri da Fatakwal
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT, Abuja – Majalisar Wakilan Najeriya ta yanke shawarar bincikar kudin da suka haura Dala biliyan 18 da aka kashe wajen gyaran matatun man kasar nan.
Majalisar ta ce an kashe wannan kudi don farfado da matatun mai mallakar gwamnati da ke Fatakwal, Warri da Kaduna cikin shekaru 20, amma ba labari.

Kara karanta wannan
An jero sunayen tsofaffin gwamnoni 2 da ka iya maye gurbin minista a gwamnatin Tinubu

Source: Facebook
Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa an dauki matakin fara bincike biyo bayan wani kudiri da 'dan majalisa Hon. Sesi Oluwaseun Whingan ya gabatar gaban majalisa a ranar Alhamis.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Majalisa ta waiwayi matatun Najeriya
Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa Sesi Oluwaseun Whingan ya nuna damuwarsa kan yadda matatun su ka mutu, ba a cin gajiyarsu.
Ya ce wannan abun damu wa ne sosai idan aka yi la'akari da duk da kashe makudan kudi da aka kashe a wajen gyaran su da alkawarin gwamnati na farfado da su.
'Dan jalisan ya kara da cewa har yanzu matatun sun kasa fara aiki duk da cewa gwamnati ta kashe kudi masu yawa da nufin dawo da su hayyacinsu.

Source: Getty Images
'Dan kasuwa Alhaji Aliko Dangote da tsohon Shugaban Kasa Olusegun Obasanjo duk sun bayyana cewa kudin da aka kashe a kan matatun ba su da amfani.
Tsohon Shugaban Kasan da Mashahurin 'dan kasuwan sun tabbatar da cewa kudin da ake birne wa a gyaran matatun, asara ne kawai.
'Dan majalisa ya damu kan matatun mai
Hon. Whingan ya tuna cewa a shekarar 2007, lokacin mulkin Obasanjo, Dangote da wasu 'yan kasuwa sun sayi matatun, amma marigayi Shugaba Umaru Musa Yar’Adua ya soke cinikin.
Whingan ya bayyana cewa karin bayanin da shugaban NNPCL, Injiniya Bayo Ojulari, ya bayar cewa matatun sun jefa shakku a kan yadda ake kashe kudin gyara su.
Ya ce:
"Ci gaba da rashin aiki na wadannan matatu duk da kudin da aka ware cikin kasafin kudi da kuma yarjejeniyoyin gyara yana nuna babbar barna ce da cin amana ga 'yan kasa."
Ya jaddada cewa ganin yadda aka cire tallafin fetur, yana da matukar muhimmanci Najeriya ta mallaki matatu masu aiki domin kare tattalin arziki da tabbatar da tsaron makamashi.
Kwamitin zai duba halin da matatun ke ciki yanzu, yanda aka yi amfani da kudin gyara su, gano matsalolin rashawa da bada shawarwari don kare dukiyar jama'a nan gaba.
Bugu da kari, kwamitin da aka kafa zai gabatar da rahoton da ya tattaro a cikin makonni hudu masu zuwa.
Lauya: Akwai abin bincike a matatun mai
Wani lauya kuma mai sharhi a kan al'amuran man fetur da ke Abuja, Barista Ibrahim Kiyawa ya shaida Legit cewa akwai abin bincike a matatun Najeriya.
Ya ce:
"Akwai abubuwan bincike a kai da yawa, saboda an saka miliyoyin kudi kuma har yanzu babu wani aiki da matata daya ko biyu ta yi na tsawon wasu lokuta."
"Maganar gaskiya, akwai abin da mu ke kira zagon kasa, su kansu ma'aikatan wannan wuraren, kila ba za su so su yi aiki ba, saboda idan ya yi aiki, su ma za su yi aiki."
"Akwai ma'aikatan da aka dauka a wannan matata, kuma ana biyansu duk da matatar ba ta aiki."
Majalisa: An yi hayaniya kan Nnmadi Kanu
A wani labarin, kun ji cewa dan majalisar wakilai Obinna Aguocha na LP ya ja zare da Shugaban Majalisa, Tajudeen Abbas game da rashin lafiyar shugaban IPOB, Nnamdi Kanu.
Ya ce tun a watan Agusta, 2025, ya rubuta wasiku zuwa ga Shugaban Kasa Bola Tinubu, Ministan Shari’a Lateef Fagbemi, da Kakakin Majalisar Wakilai, Abbas Tajudeen kan batun.
Aguocha ya ce yana da rahoton likitoci da na kungiyoyin likitoci na kasar da suka tabbatar da cewa jikin Kanu na fuskantar matsaloli irin su gajiya, da kuma karancin sinadarin potassium.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


