Farouk Lawan: Abin da Tsohon Dan Majalisa a Kano Ya Fadawa Tinubu bayan Masa Afuwa
- Tsohon dan majalisar tarayya a jihar Kano. Hon. Farouk Lawan ya yi martani bayan shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya yi masa a fuwa.
- Tsohon dan majalisar da ya wakilci Shanono/Bagwai a Kano ya gode wa shugaban ƙasa Bola Tinubu bisa yafiyar da ya samu bayan tuhume-tuhume
- Ya bayyana Tinubu a matsayin uba mai tausayi da jajircewa, wanda ya nuna rahama da adalci a cikin shugabancinsa, ya ce ya samu kwarin guiwa
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kano - Tsohon ɗan majalisar wakilai, Farouk Lawan, ya nuna farin cikinsa bayan samun afuwa daga Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu.
Tsohon dan majalisar daga jihar Kano ya yi godiya ga shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu bisa yafiyar da ya yi masa ta musamman.

Source: Facebook
Hakan na cikin wani rubutu da ya yi a shafinsa na Facebook a jiya Alhamis 9 ga watan Oktobar 2025 da muke ciki.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Farouq Lawan da wadanda Tinubu ya yiwa afuwa
Tsohon dan majalisar da ya taba wakiltar mazabar Shanono/Bagwai ya bayyana cewa wannan afuwa da ya samu ta kara masa kwarin guiwa.
Lawan na daga cikin mutane 175 da suka samu yafiyar shugaban ƙasa bayan amincewar Majalisar Koli ta Ƙasa bisa shawarar Tinubu a ranar Alhamis.
Wasu fitattun da suka amfana da wannan afuwa sun haɗa da Herbert Macaulay da tsohon ministan Abuja, Janar Mamman Vatsa (mai ritaya).
Zargin da aka yi wa Farouk Lawan
Tun farko an zargi tsohon dan majalisar da karbar cin hanci wajen binciken badakalar tallafin man fetur wanda ya yi sanadin daure shi a gidan kaso.
Daga bisani, an saki tsohon dan majalisar bayan zargin cin hanci na makudan kudi har $3m a hannun babban 'dan kasuwa, Femi Otedola.
Wannan na zuwa ne bayan daure tsohon dan Majalisar har na tsawon shekaru biyar a gidan gyaran hali na Kuje a Abuja.

Source: Facebook
Abin da Farouk Lawan ya fadawa Tinubu
Har ila yau, Farouk Lawan ya bayyana Tinubu a matsayin shugaba mai tausayi da kishin al’umma, inda ya ce shugaban ya masa abin da ba zai manta ba.
Ya ce:
"Ina godiya ga Allah Maɗaukaki (SWT), Mai jin ƙai kuma Mai rahama, bisa ni’imar rayuwa da ya ba ni.
"Zuwa ga uba mai tausayi, mai jin ƙai kuma jajirtaccen jagoran siyasa, Mai girma Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, GCFR, tarihi zai tuna da kai.
"Shugaban ƙasa ya shimfiɗa mini bargo na tausayawa, ya fitar da ni daga sanyi da ƙunci da nake ciki a baya, na durƙusa da cikakken tawali’u cikin zuciyata, ina gode wa rahamar da Allah (SWT), ta hannun Shugaban Ƙasa da ƙasata suka nuna mini."
'Gidan yari ya sauya ni' - Farouk Lawan
Kun ji cewa bayan fitowa daga gidan yari, tsohon dan Majalisar Tarayya daga jihar Kano ya fadi darusan da ya koya yayin zamansa a gidan kaso.

Kara karanta wannan
Atiku ya shiga sahun masu neman fito da shugaban kungiyar ta'addanci da aka kama tun 2021
Hon. Farouk Lawan ya ce zamansa a gidan gyaran hali na tsawon shekaru ya mayar da shi mutumin kirki fiye da yadda yake a baya.
Tsohon dan Majalisar ya kuma bayyana matsayar siyasarsa inda ya yabawa tsarin Sanata Rabi'u Kwankwaso duba da irin gudunmawar da yake bayarwa.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

