Yadda Zargin Bata Annabi SAW da Wasu Abubuwa Su ka Yamutsa Hazo a Kano
A tsakanin watan Satumba zuwa wannan wata na Oktoba, 2025, an samu manyan al'amura akalla uku da su ka bar mutanen Kano a cikin musayar yawu da mayar da zance.
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Daga watan Satumba zuwa Oktoba, an samu manyan al'amura da ke neman jawo hayaniya a tsakanin dariku daban-daban da kuma gwamnatin Kano da 'yan sanda.
A farkon watan Oktoba, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi wasu kalamai a cikin fushi a kan Kwamishinan ’Yan Sanda, Ibrahim Adamu Bakori.

Source: Facebook
Idan za a tuna, an samu sabanin Malamai a kan salon karatun daya daga cikinsu, Sheikh Lawan Triumph, lamarin da har yanzu ana tattauna wa a kai.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sannan an samu sabani a tsakanin sha'irai biyu; Malam Usman Mai Dubun Isa da Shehi Ahmad Tajul-izzi, wacce har ta kai ga suna kokarin kafirta junansu, kamar yadda za a karanta a wannan rahoto.
1. Gwamnan Kano da kwamishinan 'yan sanda
The Cable ta wallafa cewa a ranar 1 ga Oktoba, 2025, yayin bikin cikar Najeriya shekara 65 da samun ’yancin kai, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya nemi a cire kwamishinan 'yan sandan jihar,
Gwamna Abba ya bayyana a bainar jama’a cewa kwamishinan ’yan sanda ya nuna rashin kwarewa da rashin biyayya ga ƙasa, bayan ya janye jami'a, shi kansa ya ki halartar tarn ranar.

Source: Facebook
Gwamnan ya ce:
“Wannan ba aikin ƙwararre ba ne. Wannan rashin biyayya ce ga Jamhuriyar Tarayyar Najeriya.”
Ya ce yadda Kwamishinan, Ibrahim Adamu Bakori PhD ya ki halartar faretin tare da janye sauran jami'an 'yan sanda, rashin kunya ne gare shi a matsayin Gwamna da Kano baki daya.
Wadannan kalamai sun ja hankalin jama'a sosai, amma duk da haka, ba a ji rundunar ta yi martanin da aka sa rai za ta yi ba, wato cikakken bayani a kan janye dakaru daga faretin.
Amma awanni kadan bayan Gwamna Abba ya nemi a sake Kwamishinan 'yan sandan, kungiyar lauyoyi mata ta jagoranci zanga-zanga a jihar Kano.
Shugabar Kungiyar, Barista Nabila Abba Isma'il ta ce:
“A lokacin da al’amuran tsaro a jihar ke cikin barazana, irin wannan mataki na kara kawo alamar tambaya kan niyyar waɗanda ke riƙe da madafun iko.”
Jama'a da dama daga cikin Kanawa sun toda albarkacin bakinsu a kan wanan al'amari, inda da wasu daga cikinsu su ka bayyana rashin dadinsu.
Daya daga cikin mazauna jihar, Muhammad Lawan ya shaida wa Legit cewa:
"Wannan cin kashin da ake yi wa Gwamna ya isa haka, abin babu dadi."
Wani da ya bayyana sunasa da Musa, ya ce:
"Na fi tunanin wannan umarni ne daga sama, babu yadda za a yi Kwamishina ya yi gaban kansa."
Aminu Abdullahi Ibrahim, 'dan jarida kuma mai sharhi a kan siyasa ya ce:
"Kuma za a iya cewa raini ne ga shi Gwamnan Jihar Kano, raini ne ga kundin tsarin mulki kuma raini ne ga al'ummar Kano baki daya."
Watakila 'yan sanda ba su halarci taron ba ne ganin shugaban kasa ya soke fareti, sai dai an ga jami'an tsaro sun fito a sauran jihohi.

Kara karanta wannan
Atiku ya shiga sahun masu neman fito da shugaban kungiyar ta'addanci da aka kama tun 2021
2. Sheikh Lawal Triumph ya jawo sabani a Kano
Ana tsaka da wancan batu da 'yan sanda da gwamnatin Kano, sai Majlisar Shura na jihar ya sanar da dakatar da Malam Lawan Triumph daga yin karatunsa.
An bukaci ya daina yin karatuttukan da suka jawo rudani a Kano da wajen jihar.
Kwamitin ya dauki wannan mataki ne bayan an yi korafi a kan Malamin da zargin kalaman rashin daraja ga fiyayyen halitta, Annabi Muhammad (SAW).
Daruruwan mazauna Kano ne suka gudanar da zanga-zangar lumana zuwa fadar gwamnati, suna neman gwamnati ta ɗauki mataki, kuma gwamna ya ce su rubuto.

Source: Twitter
Bayan su, Kwamitin Malaman Sunnah a karkashin Sheikh Abdallah Gadon Kaya ya shigar da korafi gaban gwamnatin Kano, har aka nemi a kafa dokar batanci a jihar.
Daga bisani,martaninsu, Majalisar Shura ta Jihar Kano — wadda ke bayar da shawara kan lamurran addini — ta dakatar da malamin daga wa’azi da koyarwa har sai an kammala bincike.
Sakataren majalisar, Shehu Wada Sagagi, ya bayyana a taron manema labarai cewa:
“An dakatar da Malam Lawan daga yin wa’azi har sai an kammala bincike kuma ya bayyana a gaban majalisar don kare kansa.”
Ya ƙara da cewa:
“Kano na daga cikin jihohin da suka fi zaman lafiya a Arewacin Najeriya… dole mu kiyaye hakan don ci gaban tattalin arziki da zamantakewa.”
Har yanzu ana kan wannan batu, yayin da jama'a, musamman mabiya dariku daban-daban ke sukar junansu da zafafan kalamai a kafafen sada zumunta.
3. Mukabalar Mai Dubun Isa da Shehi a Kano
A kusan tsakiyar watan Satumba ne aka yi wata tattaunawa tsakanin Me Dubun Isa da Shehi Me Tajul Izzi a kan wani hadisi da ake dangantawa Sahabi Jabir RA.
An zauna ne game da ingancin hadisin da ya yi maganar asalin halittar Annabi Muhammad SAW, wanda ake ganin shi ne madogoran 'yan hakika.
Lamarin ya dauki zafi matuka, inda bayan an kammala mukabalar, Me Dubun Isa ya ki gaisa wa da Tajul Izzi, inda ya ke jingina shi da kokarin yin shirka.

Source: Facebook
Tuni Hukumar Tace Fina-Finai ta Jihar Kano ta sanar da dakatar da duk wani shiri na muƙabala tsakanin mawakan yabon Manzon Allah (SAW) a fadin jihar.
Shugaban hukumar, Alhaji Abba El-Mustapha, ya bayyana haka tare da gayyatar sha'iran biyu a kan su bayyana a gabanta domin a tattauna.
Kakakin Hukumar, Abdullahi Sani Sulaiman, ya bayyana cewa daga yanzu, babu wata muhawara ta addini da za a gudanar a jihar Kano sai an samu sahalewar hukumar.
Babban malami ya rasu a Kano
A wani labarin, mun wallafa cewa jihar Kano ta shiga yanayi na alhini bayan rasuwar Malam Kabiru Ibrahim Umar Madabo, fitaccen malamin addini, a ranar Alhamis bayan sallar La’asar.
Sheikh Anas Mahmud Madabo ya tabbatar da wannan rasuwa, kuma an sanar da cewa za a yi sallar jana’izarsa a ranar Juma’a, 10 ga Oktoba 2025, da misalin ƙarfe 10:00 na safe.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng



